Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Lahadi 29/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. WHO ta yi kira ga Amurka ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Cuba

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Ghebreyesus, ya yi kira ga Amurka da ta janye takunkuman tattalin arzikin da ta ƙaƙaba wa Cuba.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta bayan ziyarar da ya kai ƙasar, Tedros ya ce ya ga yadda ma'aikatan lafiya ke kula da yara a asibitoci duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

    Amurka dai ta ƙara tsaurara takunkumanta kan Cuba, ciki har da ƙarin takunkumai da hana shiga da mai.

    Lamarin ya yi matuƙar tasiri ga tattalin arzikin ƙasar tare da janyo yawaitar katsewar wutar lantarki.

  2. Gwamnan Plateau ya gargaɗi masu hannu a kai hare-hare jihar

    Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya gargaɗi mutanen da ke da hannu a kashe-kashe da sauran ayyukan ta'addanci a jihar cewa, gwamnatinsa a shirye take ta yi amfani da dukkan karfin da take da shi domin murkushe su.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a Jos yayin bikin yaye jami'an tsaron dazuka 1,000 da aka horas, karkashin shirin horas da jami'an tsaron dazuka na shugaban Najeriya, wanda tsari ne na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

    Mutfwang ya ce shirin na daga cikin tsare-tsare na ɓangaren tsaro na shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ɗaukar aiki da horar da jami'an zai taimaka wajen karfafa ayyukan tsaro, musamman a yankunan da ake yawan kai hare-hare da kuma cikin dazuka.

    Gwamnan ya yaba jami'an da aka ɗora wa alhakin tsaron al'umma, yana mai cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta tafi a banza ba.

    Gwamnan ya kuma bayyana cewa shekaru da yawa na sakaci, rashin kula da kuma rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, ya bai wa ɓata-gari damar cin karensu babu babbaka.

    Sai dai ya yi watsi da batun cewa rikicin da ake fama da shi a Filato rikicin makiyaya da manoma ne kaɗai, inda ya ce wasu daga cikin hare-haren na da nufin yi wa jihar zagon ƙasa.

    Mutfwang ya zargi wasu ƙungiyoyin 'yanbindiga da ke kai hare-hare a arewaci da kuma tsakiyar Filato, da fitowa daga wajen jihar domin addabar al'ummomi, kashe mazauna yankuna da kuma kwace filayensu.

  3. Ambaliya ta shafi mutum sama da miliyan ɗaya a Peru

    Mamakon ruwan sama na ci gaba da addabar arewacin ƙasar Peru, inda hukumomi suka ce yanzu sama da mutum miliyan ɗaya ne abin ya shafa.

    Sun yi gargaɗin cewa akwai barazanar zaftarewar ƙasa baya ga ambaliyar ruwa da ta mamaye birane da dama.

    Jami'ai sun fara raba ruwan sha a kwalabe da tankokin ruwa bayan lalacewar wasu cibiyoyin tace ruwan kasar.

    Mazauna biranen da lamarin yafi ƙamari sun ce ba a kula da magudanan ruwa yadda ya kamata ba.

    Sun kuma buƙaci Shugabar ƙasar, ta cika alkawarin da ta yi na ziyartar yankunan da ambaliyar ta shafa.

  4. Jami’ar Northwest ta haramta wa ɗalibai bai wa malamai kyautuka

    Jami’ar Northwest da ke jihar Kano ta haramta wa ɗalibai da malamai daga bayarwa ko kuma karɓar kyautuka a tsakaninsu, inda ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin karya wannan umarni zai fuskanci hukunci.

    Jami’ar ta bayyana wannan ɗabi’a ta bayar da kayutuka a matsayin cin hanci da kuma babban laifi na rashin ɗa’a, tana mai jaddada cewa haramcin ya shafi ma’aikata da ɗalibai baki ɗaya, ba tare da la’akari da manufar bayar da kyautar ba.

    Rajistra na jami’ar, Isyaku Adamu, ne ya sanar da haramcin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu ɗalibai sun bai wa malamai kyaututtuka da sunan karrama su a matsayin waɗanda suka hazaƙa.

    A cewarsa, irin wannan ɗabi’a na iya lalata martabar jami’ar tare da saɓa wa tanade-tanaden dokokin aikin jami'ar na 2025 da aka yi wa garambawul.

    Jami’ar ta bayyana karara cewa bayarwa da karɓar kyautukan yana a matsyain cin hanci da zai iya ɓata ƙimar ta.

    “Saboda haka, duk wani ma’aikaci ko ɗalibin da aka samu yana bayarwa ko karɓar kyauta za a tuhume shi da aikata babban laifi. Kuma za a ɗauki mataki nan take kan malami ko ɗalibin da aka samu da laifi," in ji Adamu.

  5. Netanyahu na shirin ganawa da babban abokin hamayyarsa Eisenkot

    Firaministan rikon ƙwarya na Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai gana da babban abokin hamayyarsa, Gadi Eisenkot, a safiyar Lahadi.

    Ana sa ran za su tattauna yiwuwar kafa gwamnati bayan zaɓen watan da ya gabata wanda bai samar da cikakken rinjaye ba.

    Ganawar za ta gudana ne a wani otal da ke bakin teku kusa da Tel Aviv, bayan da Netanyahu ya ba da shawarar miƙa ragamar mulki na ɗan lokaci ga Gadi a wata gwamnati ta haɗin kai.

    Wakilin BBC ya ce an kasa samun wanda ya yi rinjaye tsakanin Netanyahu da Gadi a zaɓen da aka gudanar watan da ya gabata.

  6. Sifaniya na gudanar da babban zaɓe a yau Lahadi

    Al'ummar Sifaniya na kaɗa ƙuri'a yau Lahadi a wani zaɓen gaggawa da Firaministan kasar Pedro San-ches ya nemi a yi bayan majalisa ta yi watsi da wasu matakan gaggawa da gwamnatinsa ta gabatar domin magance matsalolin muhalli.

    Sai dai kuri'un jin ra'ayin jama'a na nuna cewa jam'iyyarsa ta Socialist na iya fuskantar rashin nasara, yayin da ake alakanta gwamnatin da zarge-zargen cin hanci da kuma wasu munanan haɗurran jirgin ƙasa da suka faru kasar.

    A ranar Juma'a, Sanchez ya shaida wa magoya bayansa cewa har yanzu suna da damar yin nasara.

    Masu nazarin siyasa dai na hasashen cewa jam'iyyar People's Party za ta karɓi mulki tare da goyon bayan jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Vox.

  7. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke kawo muku a shafukan mu na sada zumunta.