Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 17 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida, Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. Ana atisayen soji tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu

    Ana ci gaba da gudanar da atisayen soji na shekara-shekara tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka, duk da umarnin Shugaba Donald Trump na rage girman atisayen sosai.

    A wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Mista Trump ya ce atisayen, wanda aka tsara domin tunkarar barazana irin su hare-haren intanet da kuma jiragen sama marasa matuƙa, yana da tsada kuma yana ɗauke da saƙon ƙiyayya ga Koriya ta Arewa.

    Atisayen yana da muhimmanci sosai ga alakar sojin Amurka da Koriya ta Kudu.

    Mista Trump ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, na daga cikin dalilan da suka sa ya yanke wannan shawara.

    Matakin da Mista Trump ya ɗauka na iya zama wani babban sauyi a daɗaɗɗiyar dangantakar tsaro ta tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu.

    A halin yanzu, Koriya ta Arewa ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan lamarin ba.

  2. Barka da warhaka!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiyar ranar Litinin.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.