Watakila Rasha ta fara buga gasar matasa ƴan 15 da FIfa za ta gudanar, Gasar kofin duniya
Za a iya ƙyale wata tawagar Rasha ta shiga gasar kwallon kafa ta FIFA a karon farko tun bayan mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine a 2022, bayan da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta ce gasa ta farko ta U-15 World Cup, wadda aka shirya gudanarwa a Azerbaijan a watan Oktoba, a buɗe take ga dukkan ƙasashe membobin FIFA.
FIFA ta haramta wa Rasha shiga ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa a watan Fabrairu 2022 bayan da ta fara kai farmakin yaki ga Ukraine, amma ta dage dakatarwar ga tawagarta ta ƴan ƙasa da shekara 17 ta maza da ta mata daga shekara mai zuwa.
Sai dai, Rasha tana daga baya- baya a wasannin U-17 da FIFA da UEFA ke shiryawa, yayin da ƙasashen Turai da dama ciki har da Ukraine da Ingila ke ci gaba da kaurace wa Rasha saboda mamayar da take yi wa makwabciyarta.
Za a fara gasar tamaula ta matasa U-15 a ranar 22 ga Oktoba kuma zai ƙare bayan kwanaki tara.