West Ham ta tuntubi Parker, bayan korar Nuno, West Han United

Asalin hoton, Shutterstock
West Ham United na sa ran nada Scott Parker a matsayin babban kocinta, bayan sallamar Nuno Espirito Santo.
Babban kocin ɗan ƙasar Portugal mai shekaru 52 ya kara gaba, saboda kasa taka rawar gani a wasannin da ya ja ragamar West Ham a gasar Championship, bayan kuma ya jagoranci ƙungiyar zuwa faɗuwa daga Premier League a kakar da ta gabata.
BBC Sport ta fahimci cewa kungiyar na tattaunawa da tsohon kocin Burnley da Bournemouth da Fulham, Scott Parker kuma ana iya tabbatar da naɗinsa kafin zuwa gidan Cardiff City da kungiyar za ta yi ranar Laraba a gasar Championship.
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Ingila ya shafe shekara huɗu a matsayin ɗan wasa a West Ham, sannan ya jagoranci Bournemouth da Burnley wajen samun tikitin hawa daga Championship a matsayin koci.
Duk da cewa ana kallon ƙungiyar ta Landan a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda aka fi sa ran za su koma gasar Premier League kai tsaye a halin yanzu tana matsayi na takwas a teburin gasar, maki shida a bayan Middlesbrough wadda ke jan ragama.
West Ham ta yi nasara biyu kacal a wasanninta shida na baya-bayan nan, sannan ta sha kashi a wasanni biyu a jere a gida, inda ta yi rashin nasara da ci 3-2 a hannun Southampton sannan kuma ta sha kashi 3-1 a hannun West Bromwich Albion ranar Asabar. Wadannan sakamakon sun sa ta sauka daga matsayi na biyu.











