Beckham ya ce Messi ya cancanci lashe Ballon d’Or na 2026, Ballon d'Or
David Beckham, wanda ɗaya ne daga cikin waɗanda suka mallaki Inter Miami kuma tsohon kyaftin ɗin Ingila, ya ce Lionel Messi ya cancanci lashe kyautar Ballon d’Or ta bana.
Shahararren ɗan wasan Argentina mai shekara 39, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na duniya sau takwas, kuma aka saka sunansa cikin jerin ƴan wasa 30 da aka zaɓa domin takarar Ballon d’Or na 2026, ya ci ƙwallonsa na 100 a Miami ranar Laraba.
Ya kuma bayar da kwallo ta biyu da Casemiro ya zura a raga a wasan da suka doke Cruz Azul da ci 2-0, nasarar da ta tabbatar wa Miami daukar Campeones Cup – gasar da ake fafatawa tsakanin waɗanda suka lashe kofunan ƙasashen Amurka da Mexico a kowace shekara.
Messi ya ci ƙwallo takwas da bayar da hudu aka zura a raga da taimakawa Argentina kaiwa wasan karshe a gasar Kofin Duniya a 2026, inda Spain ta doke su ta daga kofin.
Shi ne ɗan wasa na biyu mafi yawan cin ƙwallaye a tarihin Kofin Duniya mai 21, bayan Kylian Mbappe na Faransa, wanda ya ci ƙwallaye 22.
Ƴan wasan da aka zaɓa takarar Ballon d’Or
Ɗan wasan gaba na Bayern Munich, Harry Kane, na ɗaya daga cikin ƴan wasan Ingila uku da aka zaɓa cikin jerin 30 na Ballon d’Or na 2026, sauran sun hada da Jude Bellingham na Real Madrid da Declan Rice na Arsenal daga Ingila.
Lamine Yamal na ɗaya daga cikin ƴan wasan Spain shida da suka lashe Kofin Duniya kuma aka saka sunayensu cikin ƴan takara, ciki harda dan wasan Paris St-Germain, Ferran Torres, wanda ya koma ƙungiyar Faransa daga Barcelona a bazara, ya shiga jerin bayan ya ci ƙwallon da ta ba Spain nasara a wasan ƙarshe.
PSG, wadda ta lashe gasar Zakarun Turai sau biyu a jere, tana da ƴan wasa tara da aka zaɓa – ciki har da wanda ya lashe kyautar bara, Ousmane Dembele.
Ƴan wasan gaba na Real Madrid, Kylian Mbappe da Vinicius Jr, su ma suna cikin takara, kamar yadda aka hada da masu tsaron bayan Arsenal, Gabriel da William Saliba suke.
Kyautar Ballon d'Or ta bana tana daga bikin cika shekara 70 da kafata, bayan da mujallar France Football ta ƙirƙire kyautar a shekarar 1956. Za a sanar da wanda ya lashe kyautar bana a wani bikin da za a gudanar a Landan ranar 26 ga Oktoba.

Asalin hoton, Getty Images















