KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Asabar 10 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku
  • Sanata BARAU da Hon Abba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Tinubu zai fara yaƙin neman zaɓen shi daga Kaduna

    Tinubu

    Jam’iyyar APC ta sanar da cewa za ta fara gangamin yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoban 2026.

    A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya fitar, jam’iyyar ta ce ƙaddamar da gangamin a Kaduna zai zama farkon zagayen neman goyon baya a faɗin jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin tarayya, Abuja.

    Sanarwar ta ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki wasu matakai masu wahala na gyaran tattalin arziki da gwamnatocin baya suka kauce wa ɗauka, kuma saboda haka APC na neman ƴan Najeriya su ba shugaban ƙasar ƙarin shekaru huɗu domin kammala sauye-sauyen da ya fara.

    Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ƴaƴanta, shugabanni da magoya baya su fito domin halartar taron da za a yi a Kaduna, tana mai cewa nasarar zaɓen 2027 za ta fara ne daga aiki a matakin gunduma da rumfunan zaɓe.

    Sanarwar ta kammala da kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar su fara shirye-shiryen wayar da kan masu zaɓe tare da tabbatar da cewa gangamin ya gudana cikin lumana.

  2. Ba za mu sauya sharuɗɗanmu bakwai domin maslaha da Amurka ba - Iran

    Iran

    Mai magana da yawun Kwamitin Tsaron Ƙasa na Majalisar Dokokin Iran, ya ce sharuɗɗa bakwai da Iran ta gindaya domin tattaunawa da Amurka "manyan jagororin ƙasar ne suka ayyana su" kuma "ba wani batu ba ne da za a iya karya ko sauya shi a matakan yanke hukunci daban-daban a Iran."

    Ya kuma ce: "Idan aka yi la'akari da tarihin Amurka, dole ne a cika waɗannan sharuɗɗa bakwai. Amurka tana da ɗabi'ar ɓoyewa a ƙarƙashin teburin tattaunawa, tana juya baya ga diflomasiyya, kuma ba abin dogaro ba ce.

    "Saboda haka, babu wani mai hankali da zai amince a ɗauki wani mataki kafin a cika waɗannan sharuɗɗa bakwai da shugabannin Iran da Amurka suka sanya hannu a kansu."

    Dangane da martanin Amurka kan shirin kwanaki bakwai, ya ce: "Saɓanin abin da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai, mai shiga tsakani daga ƙasar Qatar ya gabatar mana da ra'ayin Amurka a daidai lokacin da Abbas Araqchi yake New York, har ma kafin ya koma Iran."

    Hassan Qashqavi ya ƙara da cewa martanin ɗayan ɓangaren kan wannan shirin shi ne: "Iran ta fara buɗe mashigin ruwa na Hormuz, sannan daga baya a hankali a riƙa cika sharuɗɗan bakwai."

    Jami'an Iran sun ce waɗannan sharuɗɗan bakwai tuni suna cikin takardar fahimtar juna ta Islamabad.

  3. Shugaban gwamnatin Falasɗinawa ya ɗage zaɓen yankin zuwa 2027

    Abbas

    Shugaban gwamnatin Falasɗinawa, Mahmoud Abbas, ya ɗage zaɓen majalisar dokokin Falasɗinu daga ranar 28 ga Nuwamba zuwa 11 ga Satumba, 2027.

    Haka kuma za a gudanar da zaɓen shugaban gwamnatin Falasɗinawa a ranar ɗaya da zaɓen majalisar.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasɗinu, Wafa, ya ruwaito cewa Abbas ya ɗauki wannan mataki ne saboda abin da ya bayyana a matsayin hare-haren soji na Isra'ila da kuma ci gaba da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinawa.

    A cikin sanarwar da ya fitar, Abbas ya ce akwai ƙalubale da dama da suka haɗa da:

    • Takunkumin zirga-zirga da motsi,
    • Matsalolin tsaro,
    • Matsalolin tattalin arziki,
    • Da kuma cikas na gudanarwa wajen shirya da gudanar da zaɓe.

    Zaɓen majalisar dokokin Falasɗinu na ƙarshe an gudanar da shi ne a shekarar 2006, inda ƙungiyar Hamas ta samu nasara.

    Wannan zaɓe ya haifar da babban rikici da rarrabuwar kawuna tsakanin ƙungiyoyin Fatah da Hamas, lamarin da ya ci gaba da tasiri a siyasar Falasɗinu har zuwa yau.

    A shekarar 2005 kuma, Mahmoud Abbas ya lashe zaɓen shugaban gwamnatin Falasɗinawa. Tun daga wannan lokaci yake ci gaba da riƙe da mukamin, bayan da aka tsawaita wa’adinsa sau da dama, duk da cewa ba a sake gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa ba.

  4. Kenya ta hana taron jama'a saboda cutar Ebola

    Ebola

    Ƙasar Kenya ta dakatar da gudanar da tarukan gwamnati da tarurruka a cikin otal-otal bayan ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola.

    Jami'an lafiya sun ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na dakile yaɗuwar cutar.

    A cewar hukumomi, mutumin da ya kamu da cutar, wanda ɗan ƙasar Kenya ne, ya rasu a ranar Litinin bayan ya yi tafiya daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ta cikin ƙasar Uganda kafin ya isa Kenya.

    Hukumomin lafiya sun ce suna ci gaba da ɗaukar matakan kariya da sa ido domin hana yaduwar cutar zuwa wasu yankuna na ƙasar.

  5. An soki Amurka bisa ƙaƙaba wa kotun ICC takunkumin kuɗi

    ICC

    An yi Allah-wadai a wurare da dama da matakin Amurka na kakaba karin takunkumin kudi akan Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC.

    Kotun ta ICC da kuma Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana haramta mu'amalar kudi da kotun a matsayin wani hari kan tsarin tabbatar da adalci na kasa da kasa.

    Kasashen Canada da Japan da kuma wasu kasashen Turai, sun sake jaddada goyon bayansu ga kotun ta ICC, wadda ke kokarin gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifukan yaki da kuma laifukan cin zarafin bil'adama.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Shugaba Donald Trump ba zai taba amincewa da abin da ya kira "kotu marar bin ka'ida" ta gurfanar da 'yan Amurka gaban shari'a ba.

    Matakin na Washington ya zo ne 'yan sa'o'i bayan da aka bai wa tsohuwar alkali Niavi File lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya.

  6. Putin ya goyi bayan ci gaba da tattaunawar Iran da Amurka ta hannun Qatar

    Putin

    Mai magana da yawun fadar mulkin Kremlin, Dmitry Peskov, ya shaida wa manema labarai a yau cewa mafi yawan tattaunawar wayar da aka yi a daren jiya tsakanin Vladimir Putin da Donald Trump ta fi mayar da hankali ne kan batun Ukraine, amma shugaban na Rasha ya kuma isar da ra'ayin Iran a yayin tattaunawar.

    Tun da farko, wani babban mataimaki ga shugaban Rasha, Yuri Ushakov, ya bayyana cewa a cikin wannan kiran waya, Putin ya maraba da ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta hannun ƙasar Qatar.

    A cewarsa, Putin ya jaddada cewa tayin da Rasha ta yi na karɓar sinadarin uranium mai matuƙar wadatarwa na Iran domin a adana shi a Rasha na nan daram kuma har yanzu yana kan teburin tattaunawa.

    Ushakov ya kuma ce akwai yiwuwar shugabannin biyu su gana ido-da-ido yayin taron kungiyar APEC da za a gudanar a ƙasar China a ranakun 18 zuwa 19 ga Nuwamba, duk da cewa ba a tattauna batun wannan ganawar ba a cikin kiran wayar da suka yi a jiya.

  7. An girke ƴansanda domin shirin sabuwar zanga-zangar jam'iyyar Coacroach

    India

    An girke karin dubban jami'an ƴansanda da na sauran rundunonin tsaro a Delhi, yayin da babban birnin na Indiya ke shirin fuskantar wata zanga-zanga da wata ƙungiyar matasa mai suna Cockroach Janta Movement ta kira.

    Ƙungiyar na neman shugaban hukumar zaɓe ya yi murabus saboda sauye-sauyen da aka yi wa jerin sunayen masu kaɗa ƙuri'a, waɗanda ƙungiyar ke cewa suna bai wa jam'iyyar BJP mai mulki tagomashi.

    Sai dai hukumar zaɓen ta musanta zargin. Hukumomi sun rufe tashoshin jirgin ƙasa da dama tare da soke wasu jiragen ƙasa da ke shiga birnin, domin hana masu zanga-zangar taruwa.

    An kuma dakatar da ayyukan intanet ta wayar salula, sannan an toshe hanyoyin shiga babban wurin da ake shirin gudanar da zanga-zangar da manyan shingayen karafa.

    Wakiliyar BBC ta ce A Indiya, ba a yarda a gudanar da zanga-zanga ba tare da izinin hukumomi ba.Duk da cewa kungiyar ta nemi izinin gudanar da zanga-zangar kwanaki uku kafin lokacin, ƴansanda sun ce ya kamata a gabatar da buƙatar aƙalla kwana goma kafin ranar zanga-zangar.

  8. Faransa ta kori jami’an leƙen asirin Nijar biyu yayin da dangantaka ke ƙara tsami

    Nijar

    Faransa ta kori jami’an leƙen asiri biyu na Jamhuriyar Nijar da ke aiki a ofishin jakadancin Nijar da ke birnin Paris, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito a ranar 9 ga Oktoba.

    Rahoton ya ce jami’an biyu, waɗanda ke aiki a ƙarƙashin babban daraktan takardu da tsaron harkokin waje, hukumar leƙen asirin Nijar, an ayyana su a matsayin waɗanda ba a maraba da zamansu ba a ranar 16 ga Satumba. Daga bisani suka fice daga Faransa bayan kwanaki uku.

    Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar wa RFI cewa an kori jami’an biyu.

    Rahoton ya ƙara da cewa an danganta korar tasu da abin da aka bayyana a matsayin “rashin jituwar ɓangarorin biyu.” Sai dai wata majiya ta ce ana zargin ɗaya daga cikin jami’an da sa ido kan ’yan adawar gwamnatin Nijar da ke zaune a Faransa.

    Duk da wannan takun-saƙa, ofishin jakadancin Nijar da ke Faransa na ci gaba da aiki a birnin Paris, a cewar RFI.

    Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sha zargin cewa Faransa na aiki tare da ƙasashen Benin da Côte d’Ivoire (Ivory Coast) domin tayar da zaune tsaye da haddasa rashin zaman lafiya a ƙasarsa.

  9. Ukraine ta yi Allah-wadai bayan Amurka ta sassauta wa Rasha takunkumi

    Ukraine

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi Allah-wadai da sanarwar Shugaba Donald Trump ta sassauta wasu takunkuman da aka ƙaƙaba wa Rasha, domin ba ta damar samar wa Amurka da kasuwannin duniya man dizel.

    Trump ya ce ya cimma yarjejeniyar ce bayan tattaunawa ta wayar tarho da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

    Zelensky ya ce sassauta takunkuman ba tare da wata kwakkwarar yarjejeniya ta rage zaman dar-dar ba, alama ce ta rauni, kuma hakan zai bai wa Rasha damar ci gaba da yakin da ta ke da kasarsa na tsawon lokaci.

    Ƴan jam'iyyar Democrat a kwamitin harkokin wajen Majalisar Dattawan Amurka, sun bayyana matakin a matsayin cin amanar Ukraine da kawayen Amurka na Turai da kuma tsaron kasar Amurka.

    Farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi tun bayan da Amurka ta fara yaki da Iran a watan Fabrairu, lamarin da ke kara matsin lamba kan 'yan jam'iyyar Republican ta Trump gabanin zaben rabin wa'adi.

  10. 'Trump ya yi maraba da yunƙurin Rasha na warware rikicin Iran'

    Trump

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga fadar shugaban ƙasar Rasha Kremlin, cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yaba da shigar Rasha cikin ƙoƙarin warware matsalar da ta shafi Iran yayin wata tattaunawar waya da ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin.

    A lokaci guda kuma, kafafen yaɗa labarai na Iran sun ruwaito, suna naƙalto Yuri Ushakov, mai bai wa shugaban Rasha shawara, cewa Putin ya shaida wa Trump a tattaunawar cewa har yanzu hanyoyin diflomasiyya a kan batun Iran suna nan a buɗe.

    Ya kuma ce yana ganin cimma yarjejeniya abu ne mai yiwuwa kuma mai matuƙar muhimmanci.

    Tun da farko, Kremlin ya bayyana a cikin sanarwarsa cewa shugabannin biyu sun tattauna kan "halin da ake ciki dangane da Iran" a kiran wayar da suka yi ranar Juma'a, amma bai yi ƙarin bayani kan abin da suka tattauna game da wannan batu ba.

    Wannan tattaunawar ta waya ta zo ne kwana guda bayan Putin da shugaban Iran Masoud Pezeshkian sun gana a ƙasar Turkmenistan.

    A yayin ganawar, Putin ya ce Rasha a shirye take ta yi "duk abin da za ta iya" domin taimakawa wajen kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

  11. Farawa

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da warhaka.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya – musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da Tuwita da kuma Instagram inda a nan ma muka wallafa ƙarin labarai da bidiyo.

    Sai ku kasance tare da mu.