Arsenal na sa ido kan Mora, AC Milan na harin Endrick

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta taya ɗan wasan Mexico Gilberto Mora, da kwantaaginsa ya ƙunshi sharaɗin siyar da shi kan fam miliyan 21.2 da Club Tijuana, da ke ɗaukar hankula daga Real Madrid, da Barcelona, da Liverpool, da Borussia Dortmund sai Benfica. (El Porvenir - in Spanish)
AC Milan na ganin ita ce kan gaba wajen iya ɗaukar ɗan wasan Brazil Endrick a matsayin ɗan wasan aro daga Real Madrid a watan Janairu, inda ɗan wasan ya ci gaba da fafutuka neman samun babba rƙungiya a cikin ƙungiyoyin Spaniya. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Nottingham Forest ta dage wajen ganin ta ɗauki Murillo a wannan bazara, inda Manchester United, da Liverpool, da Chelsea ke son ɗaukar ɗan wasan. (Teamtalk)
Daraktan wasannin Bayern Munich Christoph Freund ya ce ana samun ci gaba a tattunawar da suke yi da wajen sabunta kwantaring ɗan wasan Ingila Harry Kane, don ganin ya tsawaita zaman sa a ƙungiyar. (ESPN)
Paris St-Germain na son ɗauko dan wasan Atletico Madrid Pablo Barrios, kan euro miliyan 70 (£59m) a watan Janairu. (Fichajes - in Spanish)
Tottenham na sa ido da kyau, kan ɗan wasan Benfica Vangelis Pavlidis, inda suka sa shi cikin ƴan wasan da za su siya a watan janairu mai zuwa. (Caughtoffside)
Bayern Munich na harin ɗan wasan Brighton Luka Vuskovic, 19, akuma yana cikin ƴan wasan da suke son ganin lallai sun ɗauke shi a 2027, yayin da Chelsea da Barcelona sum ake sa ido akan sa. (Teamtalk)
Ɗan wasan Barcelona Dani Olmo, na cikin ƴan wasan da Bayern Munich ke son ɗaauka. (beIN Sports)
Da alama akwai yiwuwar dole sai Manchester United ta siyi ƴan wasa gaba da na bayan a watan Janairu mai zuwa, saboda yadda ta ke fama da ƙarancinsu a ƙungiyar. (Sun)




























