Za a iya ganin sauyi a tawagar Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images
A al'ada, lashe gasar Europa League da kuma samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai kan sanya ƙungiya ta yi siyayya mai ƙarfi.
Sai dai Aston Villa ta fuskanci matsaloli a wannan bazarar, inda ta zama ɗaya daga cikin waɗanda tsarin da ta dade tana suka ya shafa.
Domin tabbatar da cewa ƙungiyar ta bi ƙa'idojin kuɗi na UEFA da na Premier League, an tilasta mata sayar da Morgan Rogers zuwa Chelsea kan kuɗin da ya kafa tarihi na fam miliyan 117.
Ko da bayan haka, an kuma sayar da Youri Tielemans, wanda tare da Rogers ya zura ƙwallo a wasan karshe na Europa League da Freiburg a watan Mayu, zuwa Manchester United.
Villa ta kuma so ta canza salon 'yan wasan bayan hagu da take da su, don haka aka amince Lucas Digne ya koma Paris Saint-Germain, yayin da Matteo Ruggeri daga Atletico Madrid ya zo domin maye gurbinsa.
Sai dai har yanzu akwai babban rashin tabbas game da tawagar Aston Villa, duk da cewa saura kwanaki huɗu kacal su fara kakar wasanni da wasan Brighton.



















