Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 15/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 15/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Tankokin mai biyu sun kama da wuta bayan taka naƙiya a mashigar Hormuz

    Dakarun juyin-juya hali na Iran (IRGC) ta ce wasu tankokin dakon mai guda biyu sun kama da wuta bayan sun taka naƙiyoyin a mashigar Hormuz.

    A cikin wata sanarwa da dakarunsuka fitar, sun ce lamarin ya faru ne a sa’o’i kalilan da suka gabata, inda tankokin guda biyu da ke bi ta wata hanya a kudancin mashigin Hormuz suka fuskancii fashewa bayan sun taka nakiya.

    IRGC ta kuma ce tankokin sun yi yunkurin bi ta mashigar Hormuz ne “a ɓoye”, inda suka kashe na’urorin bayyana ainihin inda suke.

    BBC ba tabbatar da iƙirarin ba kawo yanzu.

    A ɗaya gefe, Cibiyar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta sanar a ranar Lahadi cewa hukumomin Indiya sun ba da rahoton kai hari kan wani jirgin dakon mai a mashigar Hormuz.

    Rahotanni sun ce an kai wa jirgin harin ne yayin da yake ketare Tekun Fasha, kafin ya shiga mashigar Hormuz.

    Ƙasashen Iran da Amurka dai na ikirarin iko da mashigar Hormuz.

  2. Yemen ta fara janye sojojinta daga yankin Bab al-Mandab

    Gwamnatin Yemen ta sanar a yau Lahadi cewa ta fara janye dakarunta daga yankin da ke kusa da mashigar ruwan Bab al-Mandab domin mayar da hankali wajen kare babban sansaninta da ke Aden.

    Ana kallon wannan janyewar a matsayin babban koma baya ga ƙawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta a yaƙin da suke yi da mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran.

    A cikin wata sanarwa, gwamnatin Yemen ta ce rundunar Soji da ke Kudancin Yemen sun fara janye wa daga filin jirgin Dhabab da kuma yankin Bab al-Mandab da ke yammacin lardin Taiz."

    Sanarwar janyewar ta kawo karshen wani farmakin ƙwato yankuna da gwamnatin Yemen ta kwashe makonni shida tana yi domin sake karɓe yankunan gaɓar teku da ke kusa da kofar shiga Tekun Bahar Maliya, waɗanda mayakan Houthi suka ƙwashe tare da matsa lamba kan fitar da man fetur daga Saudiyya.

    Janyewar ya ƙara nuna cewa Houthi za su iya ci gaba da kutsa kai zuwa Aden, tare da kara jefa Saudiyya cikin wani mawuyacin hali wajen dakile hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da ƙungiyar ke kai wa.

    Tun shekara ta 2015 ne dakarun gwamnatin Yemen suke da sansani a Aden da ke kudancin ƙasar, bayan da mayakan Houthi suka ƙwace Sanaa, babban birnin kasar.

    Zuwa yanzu, Saudiyya da mayakan Houthi ba su yi wani martani kan lamarin ba.

  3. An ceto mutum 19 a hannun ƴanbindiga a Zamfara

    Ƴansanda

    Rundunar ƴansanda a jihar Zamfara ta ce ta ceto mutum 19 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara, bayan shafe kwanaki 22 a hannun ƴanbindiga.

    An yi garkuwa da mutanen ne a ƙauyen Tungar Haki da ke karamar hukumar Gusau, kafin tafiya da su zuwa wani wuri a ƙauyen Kungurmi.

    Ƴansandan sun ce an ceto mutanen ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Asabar, a wani samamen haɗin gwiwa da jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane da jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS da kuma mafarauta suka gudanar.

    Sun ce an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan inda aka ɓoye mutanen.

    A cikin wata sanarwa da kakakin ƴansanda a jihar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, ya ce an gano dukkannin mutanen 19 cikin koshin lafiya, kuma tuni aka haɗa su da iyalansu.

    Kwamishinan ƴansanda a jihar, Ahmad Muhammad Bello, ya yaba wa haɗin gwiwar jami’an tsaron da suka kai ga ceto mutanen.

    Ya kuma sake jaddada kudurin rundunar na ci gaba da yaƙi da matsalar garkuwa da mutane da sauran laifuka, tare da kira ga mazauna jihar da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci.

  4. Guatemala ta ayyana dokar ta-ɓaci a wasu yankunan gabashi na ƙasar

    Guatemala

    Guatemala ta ayyana dokar ta-ɓaci a wasu yankuna na gabashin ƙasar domin tunkarar sabon tashin hankalin da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi.

    Dokar za ta bai wa jami’an tsaro ƙarin iko na tsawon kwanaki 30 a lardunan Zacapa da Izabal.

    Matakin zai taƙaita tarukan jama’a, sannan zai bai wa hukumomi damar kama mutane tare da shiga gidaje ba tare da sammacin ba.

    A makon da ya gabata, wasu ƴanbindiga suka kashe ɗan majalisar dokokin ƙasar, Julio Portillo, da kuma jami’an ‘yan sanda uku a garin Rio Hondo da ke jihar Zacapa.

    A cikin shekara guda da ta gabata, an samu ƙaruwar tashe-tashen hankula a Guatemala, ciki har da rikice-rikicen iko tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba da kuma kashe-kashen da ke da nasaba da siyasa gabanin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar a watan Yunin shekara mai zuwa.

  5. Ƴanbindiga sun hallaka mai taimaka wa gwamnan Zamfara Nasiru Kaura

    Ƴanbindiga

    Ƴanbindiga sun kashe babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a garin Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.

    Rahotanni sun ce an harbe Nasiru Sani Kaura ne lokacin da 'yan bindigar suka kai hari yankin Low Cost da ke Kaura Namoda da sanyin safiyar Lahadi.

    Mazauna yankin sun ce maharan sun kutsa cikin unguwar ne a lokacin da Musulmai ke gudanar da Sallar Asuba, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa jama'a suka yi ta gudu don neman tsira.

    Mutuwarsa ta jefa al'ummar Kaura Namoda da sauran sassan jihar cikin jimami.

    Daga bisani an yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

    Wannan kisan ya sake nuna irin matsalar tsaro da Kaura Namoda da kuma sauran yankunan Zamfara ke ciki, inda al'ummomi ke ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga.

    Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

  6. Mulki zai koma Arewa bayan Tinubu ya kammala wa'adinsa na biyu - Bichi

    Abba Bichi

    Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi, ya buƙaci al'ummar Arewacin Najeriya su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin ya sake samun wa'adin mulki karo na biyu, inda ya ce bayan ya kammala wa'adin da kundin tsarin mulki ya tanada, mulki zai koma Arewa.

    Ɗan majalisar daga jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Bichi a majalisar wakilai ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ranar Lahadi.

    Bichi ya ce ya dace a bar Kudu ta kammala wa'adin shekaru takwas kafin a sake mayar da mulki yankin Arewa.

    Ya ce Arewa ta riga da ta yi shekara takwas a mulki lokacin marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari, yayin da Kudu ta yi shekara huɗu kacal a karkashin shugaba Tinubu.

    "Mun yi wa'adin mu na shekara takwas a karkashin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Yanzu sun yi shekara huɗu, a bar su su kammala sai mu sake karɓa.

    "A bar Shugaba Tinubu ya kammala wa'adinsa na biyu, sannan mulki ya koma Arewa. Tinubu na son arewa kuma ya yi wa yankin abubuwa masu kyau."

    Bichi ya kuma yi watsi da zarge-zargen cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da Arewacin Najeriya, inda ya ce yankin ya amfana matuka daga manufofin gwamnati da ayyukan more rayuwa da sauran tsare-tsaren tallafi da gwamnatin ta aiwatar.

  7. An yanke wa mutum uku hukuncin kisa kan kai hari coci a Jordan

    Jordan
    Bayanan hoto, Mutum tara ne suka mutu a harin da aka kai cocin Orthodox a watan da ya gabata

    Wata kotu a ƙasar Jordan ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa bayan samunsu da laifin kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane a wani coci da ke kudancin Amman, babban birnin ƙasar, a watan da ya gabata.

    Mutane tara ne suka mutu yayin da wasu 34 suka jikkata sakamakon harbin.

    An same su da laifuffuka da dama da suka shafi ta'addanci, ciki har da kisan kai, haɗa baki da kuma yaɗa tsattsauran ra'ayi.

    Kotun koli a Jordan za ta sake yin duba hukuncin.

    An kama waɗanda ake zargin kwanaki uku bayan kai harin, bayan wani artabu da jami'an tsaro a wani gida a lardin Karak.

    Ba kasafai ake kai Irin waɗannan hare-hare a Jordan ba, inda Kiristoci ke da kusan kashi uku cikin 100 na al'ummar ƙasar.

    Bayan harin, Jordan ta kai harin ramuwa a kan iyaka da Siriya, inda ta ce ta kai wa wuraren da mayakan da suka kai harin ke alaƙa da su.

  8. Masana'antun sarrafa tufafi a Bangladesh sun yi barazanar rufewa

    Bangladesh

    Masu masana'antun sarrafa tufafi a Bangladesh sun yi gargaɗin cewa za su rufe masana'antunsu daga yau Lahadi idan ma'aikata ba su zo wurin aiki ba, hakan kuma na nufin ba za a biya su albashi ba.

    Ma'aikatan masana'antun sarrafa tufafi sun gudanar da jerin zanga-zanga, inda suke neman a biya su mafi karancin albashin na kimanin dala 240.

    Sama da Mutane miliyan huɗu, waɗanda akasarinsu mata ne, ke aiki a masana'antun sarrafa tufafi na ƙasar Bangladesh - suna samar da kayan sawa ga shahararrun shagunan sayar da kayayyaki irin su Primark da Zara da Sainsbury's da ASDA.

    A shekarar da ta gabata, ƙasar ta fitar da kayan sawa da darajarsu ta kai kimanin dala biliyan 38 zuwa kasasen waje

    Gwamnati ta kafa kwamitin daidaita albashi domin tattauna buƙatun ƙungiyoyin ma'aikatan.

  9. Obi mutum ne mai gaskiya, ba ya cin hanci - Kwankwaso

    Obi da Kwankwaso

    Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, a matsayin mutum mai gaskiya wanda ba ya cin hanci.

    Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyar na Jami'ar Skyline da ke Kano.

    Ya ce wannan hali na rashin cin hanci yana da matuƙar muhimmanci wajen shugabantar ƙasa.

    "Abu ɗaya da na lura da shi cikin watannin nan da muka shafe muna aiki tare shi ne Peter Obi ba ya cin hanci. Ba mutum ba ne da za ka yi tunanin ana iya danganta shi da cin hanci, kuma wannan abu ne mai muhimmanci ƙwarai wajen tafiyar da mulki a wannan ƙasa," in ji shi.

    Kwankwaso ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin NDC za ta ba ilimi fifiko tare da ƙoƙarin samar da ilimi kyauta domin tabbatar da cewa babu wani yaro da ya rage ba ya zuwa makaranta saboda matsalar kuɗi.

    "Muna da ra'ayi iri ɗaya musamman kan harkar ilimi. Mun yi imanin cewa idan muka haɗa kai, zai yi wuya a ga wani yaro a wannan yanki ko wani wuri a ƙasar nan yana yawon bara saboda neman abin da zai ci.

    A nasa jawabin, Peter Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da masana'antun da suka mutu a Kano domin bunƙasa harkokin tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.

    Ya bayyana Kano a matsayin cibiyar cigaban tattalin arziƙin Najeriya, yana mai cewa duk wani yunƙuri na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar dole ne ya fara daga jihar.

    "Idan muna son gyara Arewacin Najeriya da kuma Najeriya baki ɗaya, dole ne mu fara daga Kano," in ji Obi.

  10. Isra'ila ta kashe wani babban kwamandan Hamas, Samir Abu Younis

    Gaza

    Sojojin Isra'ila sun kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Hamas.

    Rundunar Tsaron Isra'ila ta ce ta kai hari kan wanda ta kira babban "ɗan ta'adda" na Hamas a cikin Gaza.

    Majiyoyi daga ƙungiyar Hamas sun ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar Samir Abu Younis a yankin Khan Younis, da ke kudancin yankin.

    Sun bayyana cewa shi ne kwamandan rundunar Hamas a birnin Rafah.

    Tun da farko dai Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga Isra'ila da ta ba ƙungiyoyin agaji damar shiga Gaza cikin gaggawa, domin taimaka wa waɗanda mummunar ambaliya ta shafa.

  11. Za a koma haƙo mai a yankin Kolmani idan muka samu nasara - Atiku

    Atiku Abubakar

    Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani, wanda ya ce gwamnati mai ci ta dakatar.

    Haka kuma ya yi alƙawarin dawo da tallafin wutar lantarki tare da farfaɗo da aikin wutar Mambilla da aka yi watsi da shi a yankin Arewa maso Gabas.

    Atiku ya bayyana haka ne yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓensa a jihar Bauchi ranar Asabar.

    Da yake jawabi a wajen taron, ya ce: “Zan dawo da tallafin wutar lantarki. Haka kuma na yi alƙawarin magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas da Najeriya baki ɗaya. Sannan za mu ci gaba da aikin haƙo man fetur a Kolmani domin mu samu ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga," in ji Atiku.

    A nasa ɓangaren, Darakta Janar na Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, Austin Akobundu, ya soki abin da ya bayyana a matsayin gazawar shugabanci da kuma manufofin gwamnatin da ke mulki da ya ce ba su dace ba.

    "Mutane na cikin yunwa a ƙasar nan. Atiku ne zai magance matsalar,” in ji shi.

  12. Cape Verde na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa

    Cave Verde

    A yau Lahadi al'ummar Cape Verde za su fito don kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban kasa.

    Shugaban mai ci na yanzu, José Maria Neves, na fatan yin nasarar samun wa'adi na biyu.

    Yana fafatawa da wasu 'yan takara biyar, ciki har da tsohuwar ministar shari'a, Joana Rosa, wadda ke da burin zama mace ta farko da za ta shugabanci ƙasar.

    Cape Verde, wadda Portugal ta yi wa mulkin mallaka, tana daga yankin yamma da Senegal.

    Muhimman batutuwan da aka fi mayar da hankali a kai yayin yakin neman zaɓen sun haɗa da yanayin rayuwar al'umma, da kuma buƙatar bunƙasa tattalin arziki domin rage yawan matasan da ke barin ƙasar zuwa ƙasashen waje.

  13. Saudiyya ta kakkaɓo makaman linzami da Houthi ta harba Riyadh

    Hayaki na tashi a kan dutse

    Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta, wanda ke yaki da 'yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya a Yemen, ya bayyana cewa ya kakkabo wasu makamai masu linzami guda biyu da aka harba zuwa babban birnin Saudiyya, Riyadh.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, kakakin kawancen, Turki al-Maliki, ya ce tun da farko tsarin tsaron sararin samaniyar Saudiyya ya lalata wasu jirage marasa matuka guda biyu a yankin gabashin kasar.

    A 'yan makonnin nan, 'yan tawayen Houthi sun kai hare-hare da dama kan wasu wurare a Saudiyya.

    A wannan bazarar ne dai kasar Yemen ta sake fadawa cikin yaki, bayan an shafe shekara hudu ana zaman lafiya.

  14. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi bar kan mu da safiyar Lahadi.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.

    Haka kuma, za ku iya ziyartar shafukan mu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke kawo muku.