Faransa za ta ƙara tallafa wa DR Congo kan yaƙi da Ebola
Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya bayyana cewa Faransa za ta ƙara yawan kuɗaɗen tallafi ga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo domin taimakawa ƙoƙarin yaƙi da cutar Ebola.
A yayin ziyararsa zuwa Bunia a ranar Asabar, birnin da aka tabbatar da cutar ta bullar tun da fari, kuma yankin da ya fi fama da ita a gabashin DR Congo, Barrot ya bukaci hukumomi da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da taka-tsantsan domin hana yaɗuwar cutar.
Tun daga watan Janairu zuwa Yulin wannan shekara, Faransa ta riga ta ware dala miliyan 15.1 domin taimakawa yaƙi da cutar Ebola.
Tun bayan ziyarar da Shugaba Emmanuel Macron ya kai DR Congo a shekarar 2023, Faransa ke ba da gudummawar jin kai, tallafa wa binciken likitanci da sauran nau’o’in taimako. Ana sa ran batun Ebola zai kasance cikin muhimman manufofin wani taron jin kai da za a gudanar nan gaba.
Barrot ya ce: "Ga wasu mutane ko shugabannin siyasa, Ebola na iya zama kamar wata matsala mai nisa. Amma cutar na iya dawowa cikin sauri. Hakkinmu shi ne mu hana sake ɓullarta."
Ya kuma rage fargabar da ake yi cewa cutar na iya yaɗuwa bayan an ba da rahoton gano wani mutum mai ɗauke da ita a Faransa, tare da yabawa ma’aikatan lafiya da na agaji saboda ƙoƙarinsu na dakile annobar.
A wani bangaren kuma, hukumomi a arewa maso gabashin DR Congo sun yi gargadin cewa har yanzu wasu mazauna yankin na ci gaba da yin watsi da dokoki da matakan kariya da aka kafa domin dakile yaɗuwar cutar Ebola.
A ranar Laraba, jami’ai sun bayyana cewa wani asibiti da wata makaranta a birnin Kisangani har yanzu suna rufe bayan an tabbatar da kamuwar wasu daga cikin ma’aikatansu da cutar.
Tun bayan ɓullar annobar a watan Mayun wannan shekara, an tabbatar da sama da mutane 8,000 da suka kamu da Ebola, yayin da fiye da 4,000 suka rasu sakamakon cutar.