Guinea-Bissau ta doke Super Eagles 3-0 a wasan neman gurbin AFCON, Afcon 2027

Asalin hoton, Getty Images
Guinea-Bissau ta doke Super Eagles ta Najeriya da ci 3-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON 2027 da aka buga a ranar Talata.
An buga karawar a filin Estádio Nacional 24 de Setembro da ke Bissau, inda Guinea-Bissau ta yi amfani da damar da ta samu wajen ɗaukar maki uku.
Franculino Djú ne ya fara sa Guinea-Bissau a gaba a minti na 15, bayan da ya samu damar zura kwallo a ragar Najeriya ta wuce Stanley Nwabali.
Super Eagles ta yi ƙoƙarin farkon da aka fara zura mata tun kan hutu, amma sai ta kasa amfani da duk wata damar da ta samu a fafatawar.
Najeriya ta shiga wasan ne bayan doke Madagascar 2-1 a wasan farko a cikin rukuni a Uyo ranar Juma'a.
George Ilenikhena ne ya farke wa Najeriya daf da za a yi hutu, kafin Moses Usor ya ci kwallon da ta bai wa Super Eagles nasara hada maki uku a zagaye na biyu..
Sai dai kuma a wasan da Najeriya ta je Bissau, ta samu kanta cikin mawuyacin hali, bayan da aka zura mata kwallo tun kan hutu, kuma ta kasa farkewa a lokacin.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Guinea-Bissau ta ƙara matsa lamba, inda Mama Baldé ya zura ƙwallo ta biyu a minti na 66, sannan kuma Álvaro Djaló ya ci na uku daf a tashi a wasa na biyu a rukuni na 12 a neman shiga gasar kofin Afirka ta 2027.








