Rui Pinto ɗan ƙasar Portugal mai shekara 37 wanda ya kafa shafin tonon-silili a harkokin kwallon kafa da ake kira Football Leaks, mutum ne da ya shahara wajen fallasa sirrin harkokin ƙwallon ƙafa.
Ana kallonsa a matsayin mutumin da ya taka muhimmiyar rawa wajen bankado bayanan da suka kai ga binciken da aka yi wa Manchester City kan zargin karya dokokin kuɗi na gasar Premier League.
An haifi Pinto a Vila Nova de Gaia, kusa da birnin Porto a Portugal. Duk da cewa bai samu ilimi mai zurfi ba a fannin kwamfuta, amma bisa hazakarsa ya koyi yawancin dabarunsa da kansa.
Malaminsa na ilimin ƙasa (Geography) a makaranta ya taɓa bayyana shi a matsayin ɗalibi mai ƙwarewa da baiwa sosai a harkar kwamfuta.
Tsakanin 2016 da 2018, Pinto ya fitar da sama da takardu miliyan 70 na sirri ga wasu ƙungiyoyin 'yan jarida masu bincike na Turai.
Takardun sun shafi wasu daga cikin manyan ƙungiyoyi, 'yan wasa da hukumomin ƙwallon ƙafa a duniya.
Daga cikin bayanan da ya fallasa akwai takardun da ake zargin sun nuna cewa Manchester City ta karya dokokin kuɗi tsakanin 2009 da 2018.
Pinto ya kafa shafin Football Leaks a shekarar 2015 da sunan bad-da-bami na "John", yana mai cewa manufarsa ita ce fallasa rashin gaskiya a harkar ƙwallon ƙafa.
Sai dai an gano asalinsa a shekarar 2019 bayan kama shi a Budapest bisa zargin aikata laifukan kutse ta intanet da ƙoƙarin karɓar kuɗi ta hanyar matsin lamba.
An mayar da shi Portugal a 2019, inda daga baya kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin je-ka-ka-gyara-halinka na shekara huɗu a 2023 saboda samun takardu ba bisa ƙa'ida ba da wasu laifukan intanet.
Sai dai a wata shari'ar ta daban a 2026, an wanke shi daga tuhume-tuhume 241 bayan kotu ta ce ba su da inganci.
Bayanan da Pinto ya fallasa sun kuma bayyana albashin fitattun 'yan wasa irin su Lionel Messi da Neymar, sannan sun sake jawo hankalin duniya kan wata ƙara da aka taɓa shigar wa Cristiano Ronaldo a Amurka, wadda daga baya aka yi watsi da ita.
Tun daga watan Agustan 2020, Pinto ya kasance ƙarƙashin kariya kasancewarsa sheda wanda ke da tarin bayanai na sirri, bayan ya amince ya bai wa hukumomin Portugal damar shiga miliyoyin takardun da yake da su.
Amma a baya-bayan nan an janye wannan kariya bayan 'yan sanda sun ce haɗarin da zai iya fuskanta ya ragu, duk da cewa an kai masa hari a watan Afirilu.
Bayan hukuncin da aka bayyana kan lamarin Manchester City, Pinto ya sanya sako a shafukan sada zumunta, inda ya bayyana shi da cewa:
"Muhimmin hukunci a tarihin ƙwallon ƙafar Ingila."
"Shekaru da dama na yaudara, da ƙarya da maguɗi za su fuskanci sakamako a ƙarshe."
Haka kuma, sa'o'i kaɗan kafin a janye kariyar da ake ba shi, ya soki shugaban FIFA Gianni Infantino, yana mai cewa ya zama "matsala ga ƙwallon ƙafa" kuma bai kamata ya ci gaba da taka rawa a makomar wasan ba.