Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, da hukumomin tsaro su tabbatar da gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun cikin lumana da gaskiya.
Al'ummar Osun za su yi zaɓen gwamnan jihar a ranar Asabar 15 ga Agustan 2026 inda ƴan takara 15 ke fafatawa.
Daga cikinsu akwai gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord, ɗan takarar APC, Munirudeen Bola Oyebamiji, da ɗan takarar ADC, Najeem Salaam.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci masu zaɓe su fito su kaɗa ƙuri'arsu, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen.
Ya ce gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin kare lafiyar jama'a kafin da kuma bayan zaɓen.
Tinubu ya buƙaci INEC ta tabbatar da cewa zaɓen ya kasance cikin tsari, gaskiya, adalci da kuma sahihanci.
Ya kuma ce ya kamata INEC ta yi amfani da wannan zaɓe na Osun, wanda shi ne na ƙarshe cikin zaɓukan da ake gudanarwa kafin babban zaɓe, a matsayin gwaji kan shirinta na babban zaɓen 2027.
Shugaban ya ce ya umarci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro da ke aikin zaɓen su samar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe.