Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 07/09/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 07/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Yaƙinmu da Rasha zai iya ci gaba har zuwa lokacin hunturu - Zelensky

    Volodymyr Zelensky ya ce yana sa ran ci za a ci gaba da gwabza yaƙi da Rasha har cikin lokacin hunturu.

    Ya bayyana haka bayan tattaunawarsa ta farko da jakadun Donald Trump a Kyiv-Jared Kushner da Steve witkoff.

    ''A yanzu mutane da dama a nan na shiryawa don tsananin da wannan rikici zai yi da kuma tsananin faɗa a lokacin hunturu,'' in ji shi.

    Amurkawan sun fara tattaunawa ta biyu da Shugaban Ukraine bayan sun yiwa ƙasashen ƙawance ƙarin haske.

    Mista Zelensky ya jaddada buƙatar ƙulla yarjejeniyar sulhun da ba za ta bai wa Rasha damar sake kai wani hari ba.

  2. Iran ta ce za ta sanar da sabon yankin tsaro a mashigar Hormuz

    Mohsen Rezaei

    Babban jami'in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya ce Iran za ta sanar da sabon yankin da aka sanya wa tsaro a wajen mashigin Hormuz.

    Ya ce yankin zai kai har zuwa wasu sassan Tekun Fasha.

    Duk jirgin ruwan da ya shiga yankin da nufin ketare mashigin ruwan, za a saka shi cikin jerin wadanda aka sanyawa takunkumi.

    Tun da farko, mai shiga tsakani na Iran Mohammad Ghalibaf, ya yi gargadin cewa Iran za ta dauki matakin mayar da martani mai tsanani cikin kan Amurka cikin gaggawa.

  3. Sallama

    Assalamu alaikum, masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu d asafiyar wannan rana da Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoronka, kamar yadda Hausawa ke yi wa kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.