'Za a yi makonni kafin tantance waɗanda gobarar jirgin ruwan Philippine ta shafa'

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Hukumomi a Philippine sun ce za a iya ɗaukan makonni ko ma watanni kafin tantance mutanen da gobarar jirgin ruwa ta shafa a makon da ya gabata.
Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar mutum 76.
"Akasarinsu sun ƙone sosai," in ji Richard Allan Mangalip, wani ƙwararren jami'in bincike a hukumar ƴansandan Philippine.
An nemi iyalan mutanen da su taimaka wajen tantance su ta hanyar gwajin DNA da kuma wasu kayayyaki da suka mallaka.
Jirgin ruwan ƙirar MV June Aster ya nufi Coron ne daga Manila a Lardin Palawan, wani fitaccen wajen zuwa hutu, a lokacin da gobarar ta tashi ta inda ake ajiye kaya sannan kuma ta yaɗu zuwa sassan jirgin.
Mutum 43 ne suka tsira yayin da wasu 13 kuma har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Jami'in ya ce suna ta ƙoƙarin abubuwan da za su taya su tantance mutanen sai dai a cewar shi zai yi wuya a iya bayar da wa'adi na tsawon lokacin da za a ɗauka na tantancewar - "zai iya kai wa makonni, ko ma watanni".
Wani jami'in tsaron teku, a ranar Asabar, ya ce abin da suka bai wa muhimmanci a yanzu shi ne tantance mutanen da kuma gano musabbabin gobarar.




















