Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 4 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Amurka ta gabatar da shawarwari ta hannun masu shiga tsakani - Qalibaf

    .

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce "Amurkawa da ke faɗin wani abu daban a kafafen yaɗa labarai, a kwanakin baya sun gabatar da wasu shawarwari ta hannun masu shiga tsakani".

    Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a zaman majalisar na yau.."

    Ba tare da bayyana cikakken bayani kan waɗannan shawarwari ba, Mista Qalibaf ya ce wa ɓangaren Amurka: "Zamanin jan lokaci da gindaya buƙatu daga ɓangare guda ya ƙare."

    Ya ƙara da cewa:"Har sai an cika sharuɗanmu guda bakwai da suka samo asali daga Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad, ba za a buɗe mashigar ruwan Hormuz ba."

    Mista Qalibaf, wanda ya kasance babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar Islamabad, ya ce:"Ba mu cika da murna ko kuma tsoro ba. Muna yaƙi kuma muna tattaunawa a lokaci guda. Muna nan a fagen daga da dukkan ƙarfimmu, kuma za mu fuskanci abokan hamayya da sabbin abubuwan mamaki. Haka kuma muna amfani da hanyoyin diflomasiyya domin ƙarfafa matsayinmu a fagen soja da kuma tabbatar da haƙƙoƙin al’ummar Iran."

  2. An yi bikin wayar da kan mata kan lalurorin mahaifa

    ,

    Mata masu lalurar Polyendocrine metabolic Ovarian Syndrome (PMOS), kan yi fama da rikicewar sinadaran jiki, sai dai likitoci na ganin abubuwan da mata kan yi amfani da su na yau da kullum kamar man shafawa da kayan kwaliyya da robobin abinci kan taimaka wajen ta’azzara matsalar.

    Waɗannan sinadarai kan kwaikwayi sinadaren jiki, ko su toshe wasu sinadaran, lamarin da ke kara ta’azzara alamonin cutar kamar samun gemu, da kiba mai tsanani, da rikiciwar a'alada da ma rashin haihuwa.

    .
    .

    Hakan ne ya sa wasu mata masu lalurar karkashin kungiyar The Cysterhood ,suka shirya taron kara wa juna sani kan illolin wadannan abubuwan amfani, da kuma abubuwan da za su yi maye gurbinsu da su domin kare lafiyarsu.

    A yayin taron, kwararriyar likita Dr Jamila Aliyu Dikko ta bayar da shawarar rage amfani da robobi masu sinadarin Bisphenol A, da daina amfani da mayuka ko turare masu sinadaren Phthalates, domin sukan toshe ko kwaikwayi sinadarai masu amfani na jikin mace kamar estrogen da testosterone da sauransu.

    An ware watan Satumban kowacce shekara domin wayar kan al'umma game da wannan lalura, sai dai duk da haka akwai karancin ilimi kanta.

    Wasu daga cikin matsalolin da masu lalurar ke fuskanta sun haɗa da tsangwama, rashin iya gano cutar da wuri daga wajen likitoci.

    Alƙaluma sun nuna cewa lalurar na shafar mace 1 cikin 10, kuma zuwa yanzu kashi 70 na mata masu lalurar ba su san suna dauke da ita ba.

  3. Ministan Man Fetur na Iran Mohsen Paknejad ya yi murabus

    Mehdi Tabatabaei, mataimakin daraktan sadarwa da yaɗa bayanai na ofishin Masoud Pezeshkian, ya sanar da cewa an amince da murabus ɗin Ministan Man Fetur, Mohsen Paknejad.

    A cewarsa, shugaban ƙasa Hamid Borad ya fitar da wata doka inda ya naɗa shi a matsayin riƙon ƙwarya na Ministan Man Fetur har zuwa lokacin da za a naɗa cikakken minista.

    Ba a bayyana dalilan murabus ɗin Mista Paknejad a cikin sanarwar ba. Haka kuma, ba a bayar da ƙarin cikakkun bayanai kan wanda zai maye gurbinsa na dindindin ba.

  4. An dawo da sabin ɗin intanet a yankin Tigray na Habasha

    l

    Sojojin gwamnatin tarayya sun karɓi iko da Mekelle, babban birnin yankin Tigray na Habasha, bayan dakarun Tigray sun janye daga birnin. Haka kuma, an dawo da hanyoyin sadarwar wayar tarho da intanet a wasu sassan yankin.

    Kungiyar Tigray People's Liberation Front TPLF ta ce ta janye dakarunta daga Mekelle ne domin kauce wa asarar rayukan fararen hula. Ta kuma ce gwamnatin yankin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na wucin gadi daga wani wuri na daban.

    Mazauna yankin sun ce yanzu an dawo da sabis na intanet da hanyoyin sadarwar tarho a wasu sassan Tigray bayan shafe mako guda ana fama da katsewar sadarwa.

    Sabbin faɗace-faɗacen sun ƙara tayar da fargabar cewa rikicin na iya bazuwa fiye da iyakokin Habasha, ganin cewa tashin hankali ya riga ya yi ƙamari a yankin Kusurwar Gabashin Afrika.

    Habasha ta zargi ƙasashen Eritrea, Masar da Sudan da goyon bayan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke adawa da gwamnati.

    Tarayyar Afirka AU ta yi kira ga dukkan ƙasashe da su nuna matuƙar haƙuri tare da kauce wa duk wani mataki da zai ƙara ruruta wutar rikicin. Haka nan ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi irin wannan kira. Ta kuma yi gargaɗin cewa tashin hankalin da ke tsakanin Habasha da Eritrea na iya kawo cikas ga haɗin gwiwar da Amurka ke yi da ƙasashen yankin.

    Sabon tashin hankalin ya sake tuno da mummunan yaƙin da ya addabi arewacin Habasha tsakanin shekarun 2020 zuwa 2022. Tarayyar Afirka ta kiyasta cewa fiye da mutane rabin miliyan ne suka rasa rayukansu a wannan rikici.

  5. An harbi wani jirgin dakon mai a mashigar Hormuz

    Hormmuz

    Wata ƙungiyar tsaron harkokin jiragen ruwa ta Birtaniya ta ce an harbi wani jirgin dakon mai da wani abin fashewa da ba a san ko daga ina ya fito ba a sabon rikicin da ya faru a Mashigar Hormuz.

    Ƙungiyar UK Maritime Trade Operations (UKMTO) ta bayyana cewa dukkan ma'aikatan jirgin suna cikin ƙoshin lafiya, kuma babu wani rahoton gurɓata muhalli da aka samu sakamakon harin. Sai dai ta ce an samu lalacewa a dakin injinan jirgin.

    Wannan shi ne karo na uku cikin kwana biyu da aka samu irin wannan hari a yankin Mashigar Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga safarar mai a duniya.

    A sabbin kalamai da suka fito daga Tehran, Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya sake jaddada cewa ba za a sake buɗe Mashigar Hormuz gaba ɗaya ba har sai an cika sharuɗɗa bakwai da aka tanada a yarjejeniyar wucin gadi da aka kulla da Amurka a watan Yuni.

  6. An saki wasu Iraniyawa da ake tsare da su a gidajen yarin UAE

    ,

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce an saki wasu fursunonin Iraniyawa da ake tsare da su a gidajen yarin Haɗaɗɗiay Daular Larabawa UAE.

    Mista Esmail ya ce sakin na su ya biyo bayan tattaunawar da aka gudanar tsakanin ƙasashen biyu a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UN General Assembly).

    Ya ce “Sakin wasu daga cikin ’yan ƙasarmu a daren jiya labari ne mai daɗi kuma mai muhimmanci a gare mu. Ya kamata mu gode wa hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa saboda haɗin kan da suka bayar wajen ganin hakan ya tabbata.”

    Ba a bayyana adadin mutanen da aka sako ba a hukumance.

    Mista Baghaei ya bayyana fatan cewa: “Sauran Iraniyawan da har yanzu suke cikin kurkuku za a sake su nan ba da jimawa ba.”

    Ba a bayyana dalilin da ya sa aka tsare waɗannan mutanen ba, amma kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran ya ruwaito cewa an tsare su ne tsawon shekaru a gidajen yari na UAE bisa zarge-zargen da ya bayyana a matsayin marasa tushe. Rahoton ya kuma ce akwai wasu mata Iraniyawa cikin waɗanda aka sako.

    Rahoton ya ƙara da cewa:“Ana ci gaba da bin hanyoyin shari’a da na diflomasiyya domin tabbatar da haƙƙoƙin waɗannan ’yan ƙasa.”

    A cikin watannin baya-bayan nan, an sako wasu Iraniyawa da dama daga gidajen yari na UAE, inda dukkansu aka bayyana a matsayin masunta. An saki mutum 55 a watan Yuli, sannan mutum 10 a watan Satumba.

  7. Amurka ta buƙaci Habasha da mayaƙa su zauna lafiya

    Habasha

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke da hannu a rikicin yankin Tigray da su ajiye makami, yayin da dakarun gwamnatin Habasha ke ci gaba da ƙarfafa ikonsu a kan babban birnin yankin, Mekelle.

    Ana sa ran shugabannin wasu ƙasashen maƙwabtan Habasha za su gudanar da wani taro a ƙasar Masar daga baya a ranar Lahadi domin tattauna halin da ake ciki.

    Gwamnatin Addis Ababa ta zargi Masar da kuma Eritrea da goyon bayan mayaƙan Tigray, waɗanda suka ƙaddamar da wani farmaki kwana goma sha ɗaya da suka gabata.

    Rahotanni sun ce mayaƙan Tigray sun janye daga wasu yankuna domin rungumar dabarar yaƙin sunƙuru, a ƙoƙarinsu na ci gaba da fafatawa.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kuma bayyana cewa rikicin da ke kara ta'azzara tsakanin Habasha da Eritrea na da yiyuwar haddasa rashin zaman lafiya a ɗaukacin yankin.

  8. Iraq ta ce ta jigilar ganga miliyan biyu na ɗanyen man fetur ta mashigar Hormuz

    Hormuz

    Kamfanin jiragen dakon mai na Iraq ya sanar da cewa ya yi jigilar ganga miliyan biyu na ɗanyen man fetur na ƙasar ta hanyar Mashigar Hormuz ta amfani da wani babban jirgin dakon mai.

    Babban daraktan kamfanin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wannan shi ne karo na farko da kamfanin ya gudanar da irin wannan aiki cikin shekaru masu yawa da suka gabata.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, wannan sanarwar na nufin cewa kamfanin zai fara jigilar ɗanyen mai kai tsaye ta cikin mashigar, maimakon tsarin da aka saba amfani da shi na isar da man a tashar jiragen ruwa ta Basra.

    Babban Manajan kamfanin, Ali Qais Abdul Jabbar, ya ce wannan mataki na iya bai wa Kamfanin Kasuwancin Man Fetur na Iraki na gwamnati damar cin moriyar ingantattun damar sayarwa da kuma samun farashi mafi kyau a kasuwa.

    A baya, Iraq ta samu izini daga Iran na bai wa jiragen dakon man Iraki damar ratsa Mashigin Hormuz, wani mashigi da Iran ta takaita zirga-zirga a cikinsa yayin zaman dar-dar da ta yi da Amurka.

  9. Za mu ƙara ƙarfi da saurin makamanmu masu linzami - Iran

    Iran

    Kakakin rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya ce an yanke wannan shawara ne bisa darussan da aka koya daga yakin da aka yi kwanan nan.

    Ya ce: "Makamanmu masu linzami da muka yi amfani da su a lokacin yaƙin, musamman waɗanda ake harbawa daga ƙasa wajen kai hari kan sansanonin abokan gaba a Kuwait, da kuma na ruwa, sun mana amfani da tasiri sosai. Amma mun fahimci cewa akwai buƙatar ƙara sauri da nisan waɗannan makamai, domin yanzu abokan gaba suna can nesa da gaɓar tekunmu, har zuwa kilomita dubu ɗaya."

    An bayyana makamin linzami mai suna Abu Mahdi Al-Muhandis, wanda ake amfani da shi wajen yaƙi da jiragen ruwa, a shekarar 2020. Ma'aikatar tsaron Iran ce ke ƙera shi. An ce nisan da zai iya kaiwa ya wuce kilomita 1,000, kuma an miƙa shi ga rundunar IRGC da kuma sauran rundunonin sojin ƙasar.

    A cikin rundunar soji, ana kuma kiran wannan makami da suna "Talaiyeh", kuma lokacin da aka ƙaddamar da shi, an bayyana shi a matsayin makamin linzami mai ruwa mafi dogon zango da Iran ta taɓa ƙerawa.

  10. An gano jirgin sama da ya ɓace a gaɓar tekun gabashin Amurka

    Amurka

    An gano wasu tarkace daga wani jirgin sama da ya ɓace a gaɓar tekun gabashin Amurka ɗauke da mutane shida a cikinsa.

    Jirgin, wanda ake amfani da shi wajen jigilar marasa lafiya ta sama, na kan hanyarsa daga Bermuda zuwa Boston lokacin da aka rasa sadarwa tsakaninsa da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama a kusa da yankin Nantucket da safiyar ranar Asabar.

    Ana ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto domin gano mutanen da ke cikin jirgin, waɗanda rahotanni suka ce sun haɗa da ƴan ƙasar Canada huɗu da kuma ƴan ƙasar Bermuda biyu.

  11. An gano jirgin sama da ya ɓace a gaɓar tekun gabashin Amurka

    Amurka

    An gano wasu tarkace daga wani jirgin sama da ya ɓace a gaɓar tekun gabashin Amurka ɗauke da mutane shida a cikinsa.

    Jirgin, wanda ake amfani da shi wajen jigilar marasa lafiya ta sama, na kan hanyarsa daga Bermuda zuwa Boston lokacin da aka rasa sadarwa tsakaninsa da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama a kusa da yankin Nantucket da safiyar ranar Asabar.

    Ana ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto domin gano mutanen da ke cikin jirgin, waɗanda rahotanni suka ce sun haɗa da ƴan ƙasar Canada huɗu da kuma ƴan ƙasar Bermuda biyu.

  12. Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya isa Ukraine ba tare da sanarwa ba

    Jamus

    Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya isa ƙasar Ukraine a wata ziyara da ba a sanar da ita tun da farko ba. Ya shaida wa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, cewa Ukraine za ta iya dogaro da cikakken goyon bayan Jamus yayin da hare-haren Rasha ke kara tsananta.

    Merz ya samu rakiyar ministar tattalin arziki ta Jamus, Katherina Reiche, da kuma shugabannin wasu manyan kamfanonin masana’antar tsaro. Ya bayyana cewa in ba a dakatar da injin yaƙin Rasha ba, to wata rana zai iya zama barazana ga Jamus kanta.

    Gwamnatin Berlin ta ware kuɗaɗen tallafin soja da suka kai fam biliyan ɗaya domin taimaka wa Ukraine. Tallafin ya haɗa da kayan kariya da nufin kare ƙasar daga sabbin jiragen yaƙi marasa matuƙa na Rasha.

    A nasa ɓangaren, Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ba da izinin kai hare-hare kan fararen hula bayan da ya kasa cimma nasarar soja a fagen daga.

  13. Sojojin Sudan sun zargi RSF da kashe aƙalla mutum 23 a Kordofan

    RSF

    Mayaƙan RSF a Sudan sun kashe aƙalla fararen hula 23 a yankin Umm Badr da ke jihar North Kordofan a tsakiyar kudancin ƙasar, yayin da faɗa ke ci gaba da zafi a tsakanin su da rundunar sojin ƙasar kan iko da yankin.

    Wannan na kunshe ne cikin rahoton kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Sudan, Suna News Agency, a ranar 3 ga Oktoba.

    Rundunar Joint Force, wadda ke ƙawance da sojojin Sudan, ta bayyana cewa RSF ta aikata "mummunan laifi" a Umm Badr ta hanyar kashe fararen hula marasa makami.

    Mai magana da yawun Joint Force, Manjo Mutawakkil Ali Wakil Abuja, ya ce: "Wani bidiyo da ke yawo tare da rahotannin cikin gida sun nuna cewa mayaƙan ƙungiyar (RSF) sun kashe fararen hula, abin da ya saɓa wa duk wata ƙa'idar jin ƙai da kuma dokokin ƙasa da ƙasa."

    Sai dai a gefe guda, ƙungiyar Sudan Founding Alliance (Tasses) ƙarƙashin jagorancin RSF ta zargi sojojin Sudan da dakarun da ke ƙawance da su da kashe aƙalla mutum 23 a birnin Sodari na jihar North Kordofan bayan sun ƙwace yankin daga hannun RSF.

  14. Ƙarfin soja da ƙarin takunkumi ba za su taimaki Amurka ba - Iran

    Iran

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce babu wata mafita ta hanyar soja ko kuma ta hanyar ƙaƙaba ƙarin takunkumi domin warware rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Amurka.

    Araqchi ya ce: "Amurka ta sha kaye a baya, a fagen yaƙi da kuma a diflomasiyya. Yunƙurin amfani da sababbin hanyoyin takunkumi ba zai amfane su da komai ba."

    Da yake jawabi a wani taro da jakadu da kuma masu kula da ofisoshin diflomasiyya na ƙasashen waje da ke Iran, Araqchi ya kara da cewa: "Mafita ɗaya tilo ita ce wacce za a samu ta hanyar tattaunawa, bisa adalci da gaskiya, tare da mutunci da diflomasiyya. Ita ce kaɗai za ta iya samar da mafita ta ƙarshe domin kawo ƙarshen wannan yaƙi da kuma wannan hari da ya saɓawa doka da adalci da aka ƙaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran."

    Yayin da yake magana kan shirin Iran na fuskantar duk wani sabon matakin farmakin soja daga Amurka, Ministan Harkokin Wajen ya ce: "Muna fatan Amurka za ta bi tafarkin hikima da tunani mai kyau. Amma idan har ta sake komawa ga mafitar yaƙi, muna cikin shiri fiye da yadda muka kasance a baya, kuma za mu ɗauki duk matakan da suka dace domin kare kanmu."

  15. Jihohin Najeriya da suke da arzikin man fetur

    Fetur

    Najeriya na daga cikin ƙasashen da suke da ɗimbin albarkatun man fetur, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati tun bayan gano shi.

    A yau, jihohi da dama ne ke samar da ɗanyen mai, musamman a yankin Neja Delta, wanda ya kasance cibiyar harkokin man fetur a ƙasar.

    Sai dai duk da yawan albarkatun da wasu jihohi ke da su, har yanzu ana ci gaba da muhawara kan yadda arzikin man fetur ya shafi ci gaban tattalin arziki da rayuwar al'ummar yankunan da ake haƙo shi.

  16. Ƴansanda sun daƙile harin ƴanbindiga a Sokoto

    Bindiga

    Ƴansanda a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun daƘile wani hari da ake zargin ƴanbindiga ne suka kai ƙauyen Tsabre da ke ƙaramar hukumar Isa a ranar 2 ga Oktoba, tare da ƙwato makaman harba roka guda biyu.

    Hakan na ƙunshe ne a rahoton shafin labarai mai zaman kansa na Premium Times da aka wallafa ranar 3 ga Oktoba.

    Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Ahmad Rufa'i, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na dare agogon Najeriya, lokacin da ɗimbin mutane ɗauke da makamai suka shiga cikin al'ummar yankin tare da buɗe wuta, lamarin da ya haddasa firgici a tsakanin mazauna ƙauyen.

    Ya ce bayan samun kira ne suka tura jami'an sashen yaƙi da garkuwa da mutane zuwa yankin domin daƙile harin.

    Rufa'i ya bayyana cewa bayan musayar wuta da jami'an tsaro, maharan sun tsere zuwa wani daji da ke kusa. Sai dai bai bayyana ko an samu asarar rayuka ko raunuka a cikin al'umma, jami'an tsaro ko maharan ba.

  17. Sai an cika sharuɗɗanmu bakwai kafin mu buɗe mashigar Hormuz - Iran

    Iran

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya bayyana a zaman majalisar na yau cewa, "Amurkawa, waɗanda a kafofin yaɗa labarai suke faɗin wani abu daban, a kwanakin baya sun gabatar da wasu shawarwari da buƙatun ƙasar ta hannun masu shiga tsakani."

    Ba tare da bayyana cikakken bayani kan waɗannan shawarwari ba, Qalibaf ya ce wa ɓangaren Amurka: "Lokacin ɓata lokaci da ƙaƙaba buƙatun ɓangare ɗaya ya ƙare. Kuma har sai an cika sharuɗɗanmu guda bakwai da suka ginu bisa yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad, ba za a buɗe mashigin Hormuz ba."

    Qalibaf, wanda shi ne ya jagoranci tawagar Iran wajen tattaunawar Islamabad, ya ce: "Ba ma cikin farin ciki sosai kuma ba ma cikin fargaba. A lokaci guda muna yaƙi kuma muna tattaunawa.

    "Muna fagen daga da dukkan ƙarfinmu, kuma za mu fuskanci abokan hamayya da sabbin abubuwan mamaki. Haka kuma muna amfani da hanyoyin diflomasiyya domin ƙarfafa matsayarmu a fagen soja tare da tabbatar da haƙƙoƙin al'ummar Iran."

  18. Mayaƙan TPFL sun fice daga birnin Meƙelle

    Sojojin gwamnatin Habasha tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun ƙwace iko da birnin Meƙelle, wanda shi ne babban birnin yankin Tigray da ke arewacin ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce Mazauna babban birnin yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, yayin da sojojin gwamnatin tarayya ke shiga birnin, mayaƙan ƙungiyar TPLF waɗanda suka fara sabon farmaki kwana goma da suka gabata sun fice daga birnin a cikin manyan motocin soja.

    Gwamnatin yankin Tigray Ta ce ta dauki matakin fice wa daga yankin ne na wani dan lokaci da nufin rage tasirin da fadan zai iya yi kan mazauna yankin.

  19. Yemen ta ƙaddamar da hare-haren martani kan mayaƙan Houthi

    Yemen

    Sojojin Yemen sun bayyana cewa suna kai hare-hare kan ƴan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya a babban birnin ƙasar, Sana'a, da kuma yankin Sa'ada da ya kasance babban sansanin ƙungiyar.

    Wani kakakin sojojin ya ce dakarunsu na kai hare-hare ne kan wuraren da ya bayyana a matsayin masu matuƙar muhimmanci.

    Wakilin BBC ya ce, sai dai kuma, da alama Saudiyya ma ta fuskanci hari, inda aka ga hayaƙi da wuta na tashi daga wata cibiyar man fetur ta kamfanin Aramco.

    Tun bayan fara yakin da ake yi da Iran, kungiyar Houthi ta ayyana takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa kan Saudiyya, inda take kai hare-hare kan wuraren da ke da muhimmanci da kuma jiragen ruwa, tare da kwace muhimman wurare da ke gabar Bahar Maliya.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar wannan shafi, barkan mu da safiyar Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu cigaba da kawo muku labaran kai-tsaye.

    Ku kasance da mu, inda za mu kawo muku labarai masu ƙayatarwa game da Najeriya da ma ƙasashe maƙwabta, da kuma sauran sassan duniya.