Afcon 2027: Super Eagles ta samu gagarumar nasara a kan Tanzania

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye daga BBC Hausa daga 9 zuwa 14 ga watan Nuwambar 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Afcon 2027: Super Eagles ta samu gagarumar nasara a kan Tanzania, Super Eagles

    Tolu Arokodare

    Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu muhimmiyar nasara a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Nahiyar Afirka ta AFCON 2027, bayan da ta doke Tanzania da ci 3-1 a wasan rukuni na 12 da aka buga a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo ranar Juma'a.

    Najeriya ta fara wasan da karfin gwiwa da cin kwallo cikin mintuna biyu da fara karawar ta hannun Alhassan Yusuf, wanda ya samu tamaula daga wajen Ademola Lookman, lamarin da ya sanya magoya bayan cikin murna tun da wuri.

    Sai dai Tanzania ba ta bari aka ci gaba da matsa mata lamba ba, domin ta dawo ta farke kwallon a minti na 32 ta hannun Alphonce Msanga, kenan wasan ya koma 1-1 kuma haka aka je hutu.

    Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Najeriya ta kara nuna kwarewa da sa matsi ga tawagar Tanzania.

    Daga nan Super Eagles ta kara ta biyu ta hannun Tolu Arokodare a minti na 52, sannan ya ci na uku saura minti 30 a tashi daga karawar, kuma haka aka tashi Najeriya ta yi nasarar cin 3-1.

    Da wannan sakamakon Super Eagles tana ta biyu a teburin rukuni na 12 da maki shida daga wasa uku, tana da tazarar maki daya tsakani da Guinea Bisau, wadda take kan teburi.

    Tawaga daya ce za a dauka a wannan rukuni daga karshe domin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2027 da za a yi a Kenya da Tanzania da kuma Uganda.

  2. Man Utd ta naɗa Pochettino a matsayin sabon mai horsawa

    Mauricio Pocchentino
    Bayanan hoto, Mauricio Pocchentino

    Ƙungiyar Manchester United ta naɗa Mauricio Pochettino a matsayin sabon mai horas da ƙungiyar, kwana ɗaya bayan korar Michael Carrick wanda bai yi ƙarƙo ba a muƙamin.

    Pochettino ya sanya hannu kan kwantarin shekara biyu da rabi da ƙungiyar ta birnin Manchester, wanda hakan ke nufin zai yi aiki har zuwa shekara ta 2029, kamar yadda aka tabbatar wa BBC.

  3. Za a ci gaba da Nations League daga ranar Alhamis, Nations League

    Nations League

    Za a ci gaba da wasannin Nations League da za a yi karawa da dama a nahiyar Turai – daga ciki fafatawar da za ta ja hankali - Turkiya da Belgium, Italiya da France, Jamuhuriyar Czech da Sifaniya da kuma wanda Ingila za ta yi wa Croatia masauki a Wembley.

    A wasan farko da suka buga a gasar a farkon makon Octoba, Ingila ce ta je ta sharara 7-0.

  4. Tuchel ya ce yana sha'awar komawa kociyan kungiya, Thomas Tuchel

    Thomas Tuchel

    Thomas Tuchel ya ce yana son komawa horas da kungiya tamaula a nan gaba, amma ya jaddada cewa babu wani aikin da zai sa ya bar jagorantar Ingila kafin gasar Euro 2028.

    Tsohon kocin, Paris St Germain da Chelsea da Bayern Munich ya fara aikin kociyan kasa a karon farko, bayan da ya maye gurbin Sir Gareth Southgate a farkon shekarar da ta gabata.

    Kociyan ya tsawaita kwantiran ci gaba da horar da Ingila a watan Fabrairu da zai kare bayan gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2028.

    Tuchel ya kai Ingila gasar kofin duniya da ta kare a mataki na uku, an yi ta dangantashi da aikin Manchester United a baya.

  5. Harry Kane zai kafa tarihi a wasan Ingila ranar Alhamis, Harry Kane

    Harry Kane

    Ana sa ran Harry Kane zai kafa tarihin mafi buga wa Ingila tamaula a karawar da za ta kece raini da Croatia a Wembley.

    Ingila wadda ta caskara Croatia 7-0 a wasan farko za ta karbi bakuncin Croatia a karawa ta biyu a Nations League ranar Alhamis

    Kane zai yi wa Ingila wasa na 126 tun bayan da ya fara taka mata leda ranar 27 ga watan Maris din 2015 - yanzu yana da sama da shekara 11 a Three Lions.

    Peter Shilton ne yake rike da bajintar mai wasa 125 a shekara 20 da ya yi wa Ingila wasanni daga 1970 zuwa 1990.

    Kane ya yi wasa 18 a Gasar cin kofin duniya, yana biye da mai tsaron raga, Jordan Pickford da tazarar wasa daya.

    Mai taka leda a Bayern Munich shi ne kan gaba a yawan buga wa Ingila European Championship sau 18, yana kan-kan-kan da cin kwallo bakwai iri daya da na Alan Shearer.

  6. Ngumoha ya ce Kane abin koyi ne a matasan Ingila da duniya, Rio Ngumoha

    Rio Ngumoha

    Matashin dan wasan Liverpool, Rio Ngumoha, ya ce nasarar da Harry Kane ya samu ta lashe Ballon d'Or za ta iya zama abin ƙarfafagwiwa ga sabon ƙarni na 'yan wasan ƙwallon ƙafar Ingila, ciki har da shi kansa, domin su bi sawun mai taka leda a Bayern Munich,

    An bai wa Kane babbar kyautar ƙwallon ƙafa a watan da ya gabata, inda ya zama ɗan Ingila na farko da ya lashe ta tun bayan Michael Owen a shekarar 2001.

    Ngumoha, wanda aka kira cikin tawagar Ingila domin wasannin Nations League na wannan mako da Croatia da Sifaniya, ya ce Kane abin koyi ne a gare shi.

  7. Za a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin Afirka, Afcon 2026

    Afcon

    Za a a ci gaba da wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kenya da Tanzani da Burundi a 2027.

    Za a ci gaba da fafatawar a ranar Alhamis.

    Daga cikin wasannin da za a buga Guinea da Eritrea, Jamhuriyar Congo da Saliyo, Equatorial Guinea da Zimbabwe, Kamaru da Namibia, Senegal da Sudan da karawar rukuni na uku tsakanin Ivory Coast da Gambia da na Ghana da Somalia.

    Tawagar Ivory Coast ce ta daya a rukunin da maki 6 iri daya da na Gambia ta biyu da Somali da ba ta da maki ta uku da itama Ghana Black Stars ta hudun teburi da sifili.

  8. Sakamakon damben gargajiya daga Ado Bayero Square a Kano, Damben Gargajiya

    Damben gargajiya

    Ga sakamakon wasannin damben gargajiya da aka dambata a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

    A wasan Dogo Dan Zakarkala ya buge Shagon Buhari

    Garkuwan Bahagon Buma ya yi nasara a kan Dogon Ebola

    Sauran wasa uku canjaras aka tashi

    • Bi Sallah da Garkuwan Alasan
    • Autan Dogon Sani da Bille
    • Mahaukaci Shagon Babba da Dogon Sharif
  9. An sanar da inda za a buga gasar kofin duniya ta mata a 2031 da 2035, Fifa Women World Cup

    Fifa

    An amince da hadakar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata ta 2031 da kuma 2035, bayan da suka cika ka'idojin da aka gindaya - kamar yadda Fifa ta sanar.

    Za a yi gasar 2031 a Amurka da Mexico da Costa Rica da kuma Jamaica, inda aka gabatar da filaye 20 a birane 20.

    Ita kuwa gasar kofin duniya ta 2035 ana sa ran gudanar da ita a Ingila da Arewacin Ireland da Scotland da Wales a filaye 19 a birane 15.

    Tawaga 48 ce za ta fafara a karon farko daga gasar 2031 mai rukuni 12 dauke da hurhudu kowanne.

    Za a buga gasar kofin duniya ta mata a shekara mai zuwa da Brazil za ta shirya wasannin daga ranar 24 ga watan Yuni zuwa 25 ga watan Yuli.

  10. Crystal Palace ta kori Sage bayan jan ragamar wasa 16, Crystal Palace

    Sage

    Crystal Palace ta sallami kocinta, Pierre Sage bayan watanni biyar kacal yana jan ragamar ƙungiyar, yayin da take ta karshen teburin Premier League.

    Tsohon kocin Brentford da Tottenham Hotspur, Thomas Frank, na tattaunawa da Palace, domin maye gurbinsa..

    Rashin nasarar da Palace ta yi da ci 3-1 a hannun Liverpool ranar Lahadi ita ce ta huɗu a jere da ƙungiyar ta yi a gasar Premier League.

    Eagles ta yi nasara biyu kacal daga wasa 10 da fara kakar nan, sannan kuma ita ce ƙungiyar da aka fi zura wa ƙwallaye a gasar da 24 a raga.

    Har ila yau, Palace tana matsayi na 21 a teburin ƙungiyoyi 36 a Europa League, bayan samun nasara ɗaya kacal daga wasanninta huɗu.

    A cikin wata sanarwa kungiyar ta ce mambobi uku na tawagar masu horarwa ta Sage, wato Jamal Alioui, Damien Della Santa da Sandy Guichard, su ma sun bar kulob ɗin.

    Sage shi ne koci na biyu a Premier League da aka sallama a wannan kakar, bayan Michael Carrick wanda Manchester United ta sallama ranar Alhamis.

    Bafaranshen mai shekaru 47 ya karɓi aikin ne kan kwantiragin shekaru uku a watan Yuni, bayan tafiyar Oliver Glasner a ƙarshen kakar wasan da ta gabata.

    A baya ya jagoranci Lens zuwa matsayi na biyu a Ligue 1 tare da lashe French Cup karo na farko a tarihin kungiyar mai shekaru 120.

    Sai dai ya gaza maimaita nasarorin da Glasner ya samu a Crystal Palace. Glasner, wanda yanzu shi ne kocin Nottingham Forest, ya jagoranci Palace zuwa lashe kofin FA Cup na farko da kuma Europa Conference League.

  11. Kane zai kafa tarihi a tawagar Ingila ranar Alhami, Harry Kane

    Harry Kane

    Harry Kane na dab da zama ɗan wasan da ya fi kowa buga wa Ingila wasanni da zarar ya yi karawar da tawagar za ta buga da Croatia a Nations League ranar Alhamis.

    Kane zai buga wa Ingila wasa na 126 tun bayan da ya fara taka mata leda ranar 27 ga watan Maris din 2015 - yanzu yana da sama da shekara 11 a Three Lions.

    Peter Shilton ne yake rike da bajintar mai wasa 125 a shekara 20 da ya buga wa Ingila wasanni daga 1970 zuwa 1990

    Shilton ya buga wasa 80 a manyan gasa da 45 a sada zumunta, yayin da Kane ya yi wasa 19 na sada zumunta. Sai dai da zuwan gasar Nations League a shekarar 2018, wasannin sada zumunta sun ragu, kuma wasanni 27 da Kane ya buga a Nations League sun bayyana bambancin.

    Kane ya yi wasa 18 a Gasar cin kofin duniya, yana biye da mai tsaron raga, Jordan Pickford da tazarar wasa daya.

    Mai taka leda a Bayern Munich shi ne kan gaba a yawan buga wa Ingila European Championship sau 18, sannan yana kan-kan-kan da cin kwallo bakwai iri daya da na Alan Shearer.

  12. Faransa ta gayyaci Mayulu a karon farko domin buga Nations League, Nations League

    Senny Mayulu

    Dan wasan Paris St Germain, Senny Mayulu, ya karbi goron gayyata a karon farko cikin babbar tawagar Faransa a ranar Laraba kafin wasan Nations League da Italiya da Turkiya.

    An ba Mayulu wannan dama ne saboda rawar da yake takawa a makonni biyu da suka gabata, inda ya zura kwallaye uku tare da bayar da biyu aka zura a raga a wasa hudu baya da ya buga wa PSG a dukkan fafatawa.

    Da farko an shirya Mayulu zai buga wa tawagar Faransa ta 'yan kasa da shekara 21 tamaula, amma daga baya aka kira shi zuwa babbar tawagar domin maye gurbin Aurelien Tchouameni, wanda yake jinya.

    Faransa, wadda ke jan ragamar rukuni na A bayan wasa hudu, za ta kara da Italiya a Milan ranar Alhamis kafin ta karbi bakuncin Turkey ranar Lahadi.

  13. Amurka ta soke ganawa da manema labarai da Pochettino, Mauricio Pochettino

    Man United

    Tawagar kwallon kafa ta Amurka ta soke ganawa da manema labarai da aka shirya yi ranar Laraba, yayin da Manchester United ke shirin yunƙurin ɗaukar babban kocinsu, Mauricio Pochettino.

    Press Association ta fahimci cewa an riga an samar da tsarin da zai bai wa ɗan ƙasar Argentina damar komawa United idan aka sallami babban kocin yanzu,

    Michael Carrick na fuskantar kalubale bayan da kungiyar ke yankin faɗuwa daga gasar, saboda mummunan sakamako a karon farko tun bayan 1986.

    An fahimci cewa Pochettino, wanda aka dauki hotonsa yana jagorantar atisayen tawagar Amurka kamar yadda aka tsara a yammacin Laraba, yana sha’awar karbar aikin Old Trafford, wanda aka yi ta danganta sunansa da mukamin a lokutan baya.

    Pochettino tsohon kocin Tottenham da Paris St Germain da Chelsea ya sanya hannu kan sabon kwantiragin wata uku da suka gabata domin ci gaba da zama kocin Amurka har zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2030, kuma US Soccer za a biyata diyya idan ya amince da komawa Manchester United.

    PA ta fahimci cewa US Soccer ta riga ta shirya yiwuwar tafiyar Pochettino kuma tana da tsarin maye gurbinsa idan hakan ya tabbata.

    Tun farko an tsara cewar Pochettino zai gana da manema labarai kan wasan da Amurka za ta kara da Nations League zagayen kwata fainals da Haiti.

    Duk da jita-jitar da ke kewaye da Carrick, ya je atisaye a United kamar yadda ya saba a cibiyar horaswa ta United da ke Carrington a safiyar Laraba.

    Ya bar Carrington da yammacin ranar Laraba ba tare da an sanar da wani hukunci kan makomarsa ba.

    An tattauna matsayinsa a wani taro a Monaco da babban jami’in gudanarwa Omar Berrada da daraktan kwallon kafa Jason Wilcox suka yi tare da shugaba, Sir Jim Ratcliffe ranar Laraba.

  14. Tinubu ya bai wa tawagar Flamingos da suka lashe kofin duniya kyautar miliyan 100 kowacce

    Flamingos

    Shugaba Bola Tinubu ya bai wa kowace daga cikin tawagar mata ta Najeriya yan kasa da shekara 17 da ake wa lakabi da Flamingos da suka lashe gasar kofin duniya, kyautar kuɗi naira miliyan 100.

    Uwargidan shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta sanar da bayar da kyaututtukan a wani taro da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    An kuma ware naira miliyan 100 ga babban mai horar da ƙungiyar, yayin da kowane mamba na tawagar masu horarwa da sauran ma’aikatan za su karɓi naira miliyan 50.

    Sanata Oluremi ta yaba wa ƙungiyar kan nasarar da ta samu ta hanyar lashe wasanni shida a jere, tare da nuna ladabi da girmamawa bayan kammala wasan ƙarshe.

    Ta ce wannan nasara za ta zama abin ƙarfafawa ga matasa mata, tare da nuna musu cewa za su iya cimma burinsu har a matakin duniya.

    Har ila yau, ta yaba wa masu horar da ƙungiyar da kuma magoya baya saboda gudunmawar da suka bayar wajen samun wannan nasara.

    Ƙungiyar Flamingos ta lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 karo na farko a tarihi bayan ta doke Japan 2-1 a wasan ƙarshe da aka buga ranar 7 ga Nuwamba.

  15. McTominay ya ce an yi masa magani kan matsalar zuciya, Scot McTominay

    McTominay

    Dan wasan Scotland,Scott McTominay ya ce an yi masa magani kan wata matsalar zuciya kwanaki biyu kafin wasan farko da kasarsa za ta buga a World Cup da Haiti a watan Yuni.

    Dan wasan mai shekara 29, an yi masa karamar tiyata a zuciya a watan Satumba, lamarin da ya sa bai yi wasannin kasa da kasa na baya.

    Scotland tana matsayi na uku a rukuni na B1 na Nations League da maki hudu daga wasanni hudu, maki uku a bayan Slovenia da kuma maki takwas a bayan jagorar rukuni Switzerland.

    Za ta karbi bakuncin Arewacin Macedonia ranar 13 ga Nuwamba kafin ta je Switzerland bayan kwana uku tsakani.

  16. ''Mbappe na fuskantar yadda Faransa za ta yi abin kirki a Nations Leageu'', Kylian Mbappe

    Kylian Mbappe

    Kyaftin din Faransa, Kylian Mbappe ya mayar da hankali kan taimaka wa kasarsa kafin wasannin Nations League da Italy da Turkey, kamar yadda takwaransa, Ibrahim Konate ya bayyana.

    Mbappe ya koma cikin tawagar Faransa bayan ya rasa karawa uku a baya saboda jinya, sannan kuma bayan ya kasa lashe kyautar Ballon d'Or ya kuma fuskanci kalubale daga China, saboda kalamansa da suka shafi Mao Zedong wanda ya kafa kasar China ta zamani.

    Dan wasan na Real Madrid mai shekara 27 ya zo na biyu bayan kyaftin din Ingila, Harry Kane ya lashe kyautar Ballon d'Or 2026.

    Tuni Mbappe ya nemi afuwa kan wasu kalamai da ya yi a wata hira inda ya yi magana kan wani shahararren hoton barkwanci na intanet da aka hada fuskarsa da ta Mao.

    Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a China, wanda ya sa kamfanoni da dama suka dakatar da hulda ta kasuwanci da Mbappe, yayin da aka daina nuna wasannin gasar Sifaniya a kafafen yada labarai na gwamnati.

  17. An tabbatar da Alcaraz da Zverez za su shiga Laver Cup 2027, Laver Cup 2027

    Carlos Alcaraz

    Carlos Alcaraz da Alexander Zverev su ne 'yan wasan farko da aka tabbatar za su wakilci Turai a gasar Laver Cup ta 2027 da za a gudanar a Los Angeles, kamar yadda masu shirya gasar suka sanar a jiya Talata.

    Za a gudanar da wasannin karo na 10 da za a yi tata burza a Los Angeles daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Satumba.

    Tawagar Duniya kuwa tana kunshe ne da 'yan wasan da ba daga Turai ba.

    Gasar ta shekara-shekara, wadda aka kaddamar a shekarar 2017, an kirkiro ta ne domin ta zama kwatankwacin Ryder Cup ta wasan kwallon golf amma ta fannin tennis.

  18. Sakamakon damben gargajiya a Ado Bayero Square, Damben Gargajiya

    Damben gargajiya

    Sakamakon wasannin damben gargajiya da aka dambata a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

    Sai dai wasannin sun ci yan kallo, domin babu dan damben da ya je kasa a fafatawar.

    • Dan Yalon Alsan da Shagon Shagon Wada Hadejia
    • Dogon Messi da Mai Karfin Ali Zuma
    • Autan Yar Biyar da Mahaukaci Shagon Babba
    • Da na Dogo Dan Zakarkala da Shagon Habu Cingam
  19. Maurinho yana son Cucurella ya zana shi a jikinsa kamar yadda ya yi na kociyan Sifaniya, Jose Mourinho

    Jose Mourinho

    Kocin Real Madrid, Jose Mourinho na son Marc Cucurella ya zane fuskarsa a jikinsa kamar yadda ya yi na fuskar kocin Sifaniya, Luis de la Fuente.

    Tun kafin fara gasar cin kofin duniya tsohon dan wasan Chelsea ya yi alkawarin idan suka lashe kofin duniya zai zana fuskar kocin tawagar a jikinsa - kuma hakan ya yi kan fara kakar bana.

    Bayan komawarsa Real Madrid a watan Yuli, Cucurella ya tabbatar da cewa sabon koci, Mourinho ya ba shi shawarar ya yi makamancin wannan karramawa a gare shi.

    Cucurella ya taba cika wani alkawari da ya yi na rina gashinsa zuwa launin ja bayan Sifaniya ta lashe European Championship a 2024.

  20. Iraki ta hana jirgin yan kwallon Iran sauka a Basra

    Kasar Iraki ta hana wani jirgin sama da ke dauke da tawagar kwallon kafa ta Iran sauka a filin Basra a ranar Talata.

    Wannan wani mataki ne da Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta kasar ta dauka bisa alaƙa da takunkumin Amurka kan kamfanonin jiragen saman Iran.

    Nan take Jirgin ya koma Iran sannan daga bisani tawagar kwallon kafar ta tafi Basra a motar bas.

    Sun je Iraki ne domin shiga wata gasa a birnin a Basra da ya hada da mai masaukin baki Iraki da Lebanon da kuma Falasdinu.

    Wani jami’in sufurin jiragen sama na Iraki ya ce an dauki wannan mataki ne saboda kasar ba za ta iya sanya kanta cikin hadarin karya takunkumin Amurka kan kamfanonin jiragen saman Iran ba.