Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Juan Mata ya yi ritaya daga taka leda yana da shekara 38

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye daga BBC Hausa daga 16 zuwa 22 ga watan Nuwambar 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An ƙi amincewa da buƙatar sauya ranar shari’ar zargin cin zarafi da ake yi wa dan wasan tawagar Ingila, Ivan Toney, domin halartar gasar Euro 2028 idan har kasar ta gayyace wasannin.

    Ana zargin ɗan wasan mai shekaru 30 da yi wa Saber Da Silva gware da naushi a wani fada da ya kaure a tsakaninsu a wani gidan rawa da ke Wardour Street, tsakiyar London, a ranar 6 ga watan Disamba.

    Toney ya musanta zargin a wani zaman kotu a watan da ya gabata, kuma an sanya ranar 12 ga watan Yunin 2028 domin fara shari’ar da ake sa ran za ta ɗauki tsakanin kwanaki uku zuwa huɗu.

    Wannan ranar kuwa ta zo ne kwanaki uku za a fara Euro 2028.

    Za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai, wato European Championship a shekarar 2028 tsakanin ranar 9 ga watan Yuni zuwa 9 ga watan Yuli.

    Toney ya fara buga tamaula tare da Northampton, sannan ya koma Wigan da Peterborough kafin Brentford ta dauke shi a shekarar 2020.

    Ya ci ƙwallaye 72 a cikin shekaru huɗu da ya shafe tare da Bees kafin ya koma Al-Ahli ta Saudi a shekarar 2024.

  2. Pochettino ya isa Manchester United ranar Laraba, Manchester United

    Mauricio Pochettino ya isa cibiyar horaswa ta Manchester United da ke Carrington a yammacin ranar Laraba, yayin da ya fara aiki a matsayin sabon babban kocin ƙungiyar.

    Dan ƙasar Argentina ya karɓi ragamar aiki a hukumance ranar Laraba, bayan kammala aikinsa na ƙarshe a matsayin kocin tawagar Amurka a Cincinnati ranar Talata.

    An fahimci cewa Pochettino ya sanya hannu kan kwantiragin da zai kai har zuwa bazarar shekarar 2029. Ya isa Manchester a safiyar Laraba kafin a kai shi kai tsaye zuwa cibiyar horaswa ta kungiyar, domin ganawa da ma'aikatan United da kuma fara shirye-shiryen wasan Premier League da Liverpool ranar Lahadi.

    An sanar da naɗinsa a ranar Juma’ar da ta gabata, sa’o’i kaɗan, bayan da United ta tabbatar da sallamar Michael Carrick, sakamakon fara kakar tamaula mafi muni da United ke yi a bana a karon farko tun bayan 1986.

  3. Kozo Tashima ya mika takardar takarar shugaban Fifa, Fifa

    Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Japan (JFA), Kozo Tashima, ya ce ya gabatar da takararsa domin takarar shugabancin FIFA a ranar Laraba, bayan samun goyon bayan hukumomin kwallon kafa na kasashe biyar.

    Za a rufe karɓar takardun takara domin zaɓen shugaban FIFA da ƙarfe 22:59 GMT na ranar Laraba, watanni huɗu kafin babban taron FIFA karo na 77 da za a gudanar a Rabat ranar 18 ga watan Maris, inda za a gudanar da zaɓen.

  4. Juan Mata ya yi ritaya daga taka leda yana da shekara 38, Juan Mata

    Tsohon ɗan wasan tawagar Sifaniya, Juan Mata ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa yana da shekaru 38.

    Mata, wanda ya buga wasa 41 a matakin ƙasa da ƙasa, yana cikin tawagar Sifaniya da ta lashe Gasar Kofin Duniya ta 2010, sannan ya taimaka wa ƙasar daukar Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai shekaru biyu bayan haka lokacin da ya ci ƙwallo a nasarar 4-0 da suka yi kan Italy a wasan ƙarshe.

    Wanda ya fara taka leda daga makarantar matasa ta Real Madrid, ya koma Valencia a shekarar 2007 kafin ya je Chelsea a watan Agustan 2011, inda ya lashe Champions League da Europa League da kuma FA Cup.

    Mata ya koma Manchester United a watan Janairun 2014, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe Europa League da FA Cup da League Cup kafin ya bar Old Trafford a shekarar 2022.

    Daga baya ya buga wa ƙungiyoyin Galatasaray ta Turkiyya da Vissel Kobe ta Japan, kafin ya koma ƙungiyar Australia wato Western Sydney Wanderers da Melbourne Victory.

    An zaɓi Mata a matsayin gwarzon dan wasan Chelsea a dukkan kakar wasanni biyu da ya yi a Stamford Bridge. Ya buga wasan lig 82 tare da kungiyar, inda ya ci ƙwallaye 18.

    A Manchester United kuwa, ya ci ƙwallaye 51 a wasa 285 kafin ya bar ƙungiyar bayan karewar kwantiraginsa.

  5. Mai kungiyar Andorra ya ce bai kamata a dakatar da Owono wasa 12 ba, Jesus Owono

    Mai kungiyar FC Andorra, Gerard Pique, ya ce mai tsaron raga Jesus Owono bai cancanci dakatarwar wasa 12 da aka yi masa ba, - bayan taho mu gana da ta kai ga mutuwar ɗan wasan Tenerife, Jesus de Miguel.

    Lamarin ya faru a wani wasan rukuni na biyu a gasar Spain a ranar 2 ga Nuwamba. An kai De Miguel dakin kulawa na musamman daga baya ya rasu washegari.

    Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ne ya dakatar da Owono da c ewar ya yi amfani da karfi fiye da kima da ya haddasa mummunan raunin.

  6. An hukuntan wani dan kallo da ya ci zarafin Kylian Mbappe, Kylian Mbappe

    Wani mai goyon bayan Real Oviedo da ya yi cin zarafin ɗan wasan gaba na Real Madrid, Kylian Mbappe ta hanyar kalaman wariyar launin fata a bara, an same shi da laifi, kamar yadda Real Madrid ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata.

    An ci tarar mutumin da ba a bayyana sunansa ba, an kuma hana shi shiga filayen wasa na tsawon shekaru biyu, sannan an yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 11 amma ba zai je gidan yari ba sai idan ya karya dokar hana shi shiga filayen wasanni nan gaba.

    Lamarin ya faru ne a lokacin nasarar da Real Madrid ta yi da ci 3-0 a kan Real Oviedo a watan Agustan 2025.

    Dokar Spain ta tanadi cewa hukuncin da bai kai shekara guda ba yawanci ana dakatar da aiwatar da shi ga wanda ya yi laifi a karon farko.

    Wannan shi ne hukunci kan samun magoyin baya da kalaman wariya da cin zarafi na 12 da ya shafi wasannin LaLiga tun daga watan Yunin 2024.

  7. Watakila Ingila ta karbi bakuncin wasan karshe a Nations League, Nations League

    Watakila Ingila ta karbi bakuncin wasan ƙarshe na Nations League na wannan kakar bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta nuna sha'awar hakan.

    Za a gudanar da wasannin kusa da na ƙarshe da na ƙarshe a kasa daya a cikin watan Yuni, amma ba a fayyace kowacce ba.

    Baya ga Ingila, an fahimci cewa Spain da Faransa ma suna son shirya wasa hudu da za su rage a karkare kakar bana daga 9 zuwa 13 ga wayan Yuni.

    Tun bayan ƙaddamar da gasar a shekarar 2019, Ingila ba ta taɓa karɓar bakuncin wasan ƙarshe ba, kamar yadda Portugal, Italiya, Netherlands da Jamus suka yi kawo yanzu.

    Ranar Juma'a za a raba jadawalin kwata finals, domin tantance yan hudun karshe - watakila a hada tawagar Ingila da ta Belgium, Netherlands, Denmark ko Norway da za a barje gumi a cikin watan Maris - kafin wasan karshe a cikin watan Yuni a 2027.

  8. Faransa ta amince Diallo ya yi takarar shugan Fifa, Fifa

    An amince da takarar Philippe Diallo ta neman shugabancin FIFA daga Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa.

    UEFA ta sanar a ranar Litinin cewa mai shekara 63 ya samu goyon bayan wakilan mambobinta da ke cikin kwamitin zartarwa da kuma Majalisar FIFA domin ya tsaya takara karbe kujerar Gianni Infantino.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Faransa ma ta ba shi goyon baya a jiya Talata, inda kwamitin zartarwa na FFF ya amince baki ɗaya da takararsa.

    UEFA ta dawo daga rakiyar Infantino sakamakon shirinsa da ya jawo ce-ce-ku-ce na sayar da hannun jari a wani kamfanin da zai ke kula da harkokin Gasar Kofin Duniya ga masu zuba jari masu zaman kansu,

    Hakan ya sa aka fara kiraye kirayen shugaban ya yi murabus, yayin da Uefa ta yi alkawarin fito da wani sahihin ɗan takara da zai fafata da shi.

  9. Romario ya bukaci a kori Ancelotti, yayin ce-ce-ku-ce a tsakaninsu, Brazil

    Babu wanda zai yi hasashen cewa Carlo Ancelotti zai fara fuskantar suka daga wani gwarzon Brazil watanni 18 kacal bayan ya zama kocin tawagar ƙasar.

    Amma Romario, wanda shi ne na huɗu cikin waɗanda suka fi yawan cin ƙwallaye a tarihin Brazil, bayan Neymar da Pele da Ronaldo, ya fito fili ya nemi a sauke fitaccen kocin daga aiki a cikin makon da ya gabata.

    Hakan ya biyu bayan da Brazil ta sha kashi da ci 3-2 a wasan sada zumunta a hannun Japan ranar Juma’a.

    An ba Ancelotti jan kati saboda nuna rashin gamsuwa bayan wasan, wanda shi ne karo na farko da aka kore shi a aikinsa na horas da tawagar ƙasa, yayin da ɗan wasan Barcelona, Raphinha, shi ma ya ga jan kati.

    Bayan rashin nasarar da Brazil ta yi, Romario ya shiga shafukan sada zumunta domin bayyana fushinsa kan tsohon kocin Real Madrid.

    "Ancelotti, ya isa haka! Ka tattara kayanka ka tafi!" ya rubuta a Instagram.

    "Babu wanda ke musanta tarihin da ka yi. Kana ɗaya daga cikin manyan masu horarwa da duniyar ƙwallon ƙafa ta taɓa gani, amma hakan ya kasance ne a matakin kungiya."

    An fitar da Brazil daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 a zagayen 'yan wasa 16 a hannun Norway, lamarin da ya sa ta kasa kai wa wasan kwata-fainal karo na farko tun shekarar 1990.

    Romario ya yi nuni da wannan ma, inda ya ce ƙasar "ba za ta iya ɗaukar haɗarin sake jefa kasar cikin hadari a wata Gasar Kofin Duniya ba - lokacin ɗaukar mataki shi ne yanzu!"

  10. Rafael Camara zai kara wakiltar Haas a Las Vegas Grand Prix, Formula 1

    A Formula One, ɗan kasar Brazil, Rafael Camara, zai yi wa tawagar Amurka ta Haas tsere karo na biyu a gasar Las Vegas Grand Prix ta ƙarshen mako.

    Matashin mai shekaru 21 ya yi wasansa na farko tare da Haas a gasar Sao Paulo Grand Prix da ta gabata tare da takwaransa, Oliver Bearman.

  11. Andreeva ta lashe WTA Final bayan doke Svitolina, Kwallon tennis

    Matashiyar 'yar wasan Rasha, Mirra Andreeva, ta doke Elina Svitolina ta Ukraine da ci 7-5, 6-3 ranar Lahadi ta lashe WTA Final - gasar kakar karshe da yan wasa takwas dake kan gaba a tennis a duniya suka halarta Indian Wells.

    Andreeva ta jefa raket ɗinta sama sannan ta yi tsallen murna lokacin da Svitolina ta bugo ƙwallo cikin raga a maki na ƙarshe, kafin daga bisani ta rungumi kocinta Conchita Martinez da sauran tawagarta.

  12. Klopp ya ce Infantino ya fi Blatter muni kan tafiyar da Fifa, Jurgen Klopp

    Kociyan tawagar Jamus, Jurgen Klopp, ya ce "ban yi tunanin abubuwa za su iya ƙara muni bayan Sepp Blatter ba, amma wani ya yi nasarar kai su wannan matakin", yayin da ya yi kira da a maye gurbin shugaban Fifa, Gianni Infantino.

    Blatter ya yi murabus daga shugabancin FIFA a shekarar 2015, bayan badakalar cin hanci da rashawa, kuma Infantino ne ya gaje shi a watan Fabrairun 2016.

    Infantino na shirin sake tsayawa takara a watan Maris, amma yana fuskantar matsin lamba tun bayan da ya yi watsi da shirin Fifa Forward Enterprise (FFE), wanda ya haɗa da sayar da hannun jarin Gasar Kofin Duniya da sauran wasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu.

    Infantino ya nemi afuwa ga Majalisar FIFA kan wannan shiri, amma an gaya masa cewa bai dace ya ci gaba da jagorantar hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ba, har sai ya fitar da dukkan takardun da suka shafi lamarin tare da bayar da amsoshin muhimman tambayoyin da za a yi masa.

    An bayyana shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa, Philippe Diallo, a matsayin ɗan takarar Uefa domin kalubalantar Infantino.

    Diallo zai tsaya takara bayan amincewar da Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa (FFF) za ta bayar a hukumance ranar Talata, bayan ya samu cikakken goyon bayan kwamitin zartarwa na Uefa.

  13. Lukaku ya yi ritaya daga buga wa Belgium tamaula, Romelu Lukaku

    Romelu Lukaku ya yi ritaya daga buga wa Belgium wasanni, yana mai cewa ya "ji daɗin kowane lokaci" da ya shafe yana wakiltar kasar.

    Dan wasan mai taka leda a Fenerbahce mai shekara 33 ya fara buga wa Belgium wasa a shekarar 2010, kuma shi ne wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin tawagar ƙasar da 94 a raga a wasa135.

    Shi ne na biyar cikin masu yawan cin ƙwallaye a wasannin ƙasa da ƙasa a duniya a tarihi, bayan Sunil Chhetri, Ali Daei, Lionel Messi da kuma jagora Cristiano Ronaldo, wanda ya ci ƙwallaye 146.

    Lukaku ya ci ƙwallaye takwas a gasar kofin duniya guda huɗu da ya halarta, ciki har da lokacin da Belgium ta kai wasan kwata-fainal a gasar bana, sannan ya ci jimillar ƙwallaye shida a gasar European Championship guda uku.

  14. Jama'a barkanmu da wannan lokacin na labarin wasanni daga BBC Hausa da za muke sanar da ku irin wainar da ake toyawa a fagen wasanni a fadin duniya.

    Za ku iya bayar da gudunmuwarku a BBC Hausa Facebook a lokacin da muke gabatar muku da filin a bbchausa.com.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skipper zan gabatar muku da shirin daga ranar 16 zuwa 22 ga watan Nuwambar 2026.