An kama tsohuwar uwargidan shugaban Sri Lanka kan zargin almundahana
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin yaƙi da cin hanci da
rashawa na Sri Lanka sun kama tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar, Shiranthi
Rajapaksa, bisa zargin wata ƙungiyar agaji da ke da alaƙa da ita ta karkatar da
kuɗin da aka ware domin tallafa wa asibitin yara.
Masu bincike na son yi wa matar
tsohon shugaban ƙasar Mahinda Rajapaksa, mai shekara 73, tambayoyi dangane da
gudummawar dala 30,000 da ƙungiyar agaji ta Siriliya Saviya ta tara domin sayen
wata na'urar gwaji ta musamman da aka yi nufin bai wa wani asibitin gwamnati na
masu fama da cutar kansa.
Jami'ai sun ce tuni gwamnatin
China ta bayar da irin na'urar a matsayin gudummawa.
Sai dai Shiranthi Rajapaksa ta
musanta aikata ba daidai ba, tana mai cewa ba a karkatar da kuɗin ba.
Mene ne ke ruruta wutar rikici a jam'iyyar APC a Kano?
Asalin hoton, Social Media/Multiple
Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya, na neman faɗawa cikin cikin gida a Jihar Kano da ke Arewacin ƙasar, ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar ke fatan samun ƙuri'u maso yawa a zaɓen da ke tafe.
Takun saƙa da gugar zana da kuma shaguɓe na neman dabaibaye siyasar jihar, ko da yake rikici ne da ake yi a cikin duhu.
Rikici ne da yake neman girmama tsakamin mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin da Ɗan Majalisar Tarayya na yankin Bichi, Abubakar Kabir Abba Bichi.
Rahotanni sun ambato cewa, duk da cewa akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa tsakanin jiga-jigan siyasar biyu, amma lamarin ya ƙara tsami ne bayan da mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo ya yi wasu kalamai masu kama da jirwaye da kamar wanka a wani taro da ya gudana a Bichi.
Garo ya bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda yake cewa duk wanda ya taɓa Abba Bichi sai ya ji su "ba a Bichi ba ko a Kabo ne".
Wannan zance ya haifar da maida martani daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau Jibrin.
A wani bidiyo na daban kuma an ga shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi na mayar da martani cikin kan masu ingiza rikicin da yake tsakaninsa da Sanatan.
Dole Iran ta rage inganta Uranium ɗinta don kawo ƙarshen yaƙi - JD Vance
Asalin hoton, Reuters
Mataimakin shugaban Amurka J.D.
Vance ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Washington na ci
gaba da tattaunawa da shugaban Iran da kuma ministan harkokin wajen ƙasar.
Vance ya ce kawo ƙarshen yaƙin na
buƙatar Iran ta rage yawan sinadarin uranium da take tacewa sosai, maimakon
kawai ta yi alƙawarin rage shi nan gaba.
A wata hira da Reuters bayan
halartar taron yaƙin neman zaɓe na jam'iyyar Republican a Alaska, Vance ya ce
Washington ba ta da tabbacin yadda Tehran za ta ɗauki matsaya a tattaunawar da
ake yi kan shirinta na nukiliya.
A cewar mataimakin shugaban
Amurkan, babban makasudin yaƙin shi ne hana yaɗuwar makaman nukiliya a Gabas ta
Tsakiya.
Vance ya kuma yi watsi da
rade-radin cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2028, yana mai cewa a
yanzu hankalinsa yana kan ganin jam'iyyar Republican ta yi nasara a zaɓukan tsakiyar
wa'adi.
An daƙile harin makami mai linzami da Houthi ta harba birnin Riyadh
Ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke
jagoranta a yaƙin da ake yi da mayaƙan Houthi a Yemen, ya ce sun dakile wani
makami mai linzami da ƙungiyar, wadda Iran ke marawa baya, ta harba zuwa birnin
Riyadh.
Ƙungiyar Houthi ta ce ta kai
hare-hare kan filayen jiragen sama biyu na Saudiyya da kuma wani sansanin sojin
sama.
Kazalika, ta ce ta kai hari kan
filin jirgin saman birnin Aden da ke Yemen.
Gwamnatin Yemen da ƙasashen
duniya suka amince da ita, ta ce wani makami mai linzami ya faɗa kan titin
saukar jiragen sama na filin jirgin, jim kaɗan kafin wani jirgin sama daga
Masar ya sauka.
An kwashe ma’aikatan jirgin ruwa 10 da suka jikkata a mashigar Hormuz
Rundunar sojin saman Oman ta kwashe ma’aikatan wani jirgin
dakon mai su 10 da suka jikkata, bayan da aka kai wa jirgin mai tutar Panama
hari a mashigar Hormuz.
A cewar Ma’aikatar Tsaron Oman, an kai wa jirgin ruwan mai
suna On Peace hari ne ranar Talata, kimanin kilomita 17 daga tashar ruwan Lima
da ke Oman.
Harin ya haddasa
gobara a saman jirgin.
Ma’aikatar Tsaron
Oman ta ce an kwashe ma’aikatan jirgin zuwa wani asibiti a Khasab, inda ake
kula da su.
Ana ci gaba da aikin gano gawawwakin sojin Najeriya 25 da suka mutu a hatsarin jirgi
Asalin hoton, Ondo SEMA
An ci gaba da zaman makoki na kwana uku a Najeriya bayan
mutuwar mutum 25 a wani hatsarin jirgin sojin ƙasar. Tun daga ranar Litinin ake
ci gaba da aikin gano jirgin da kuma gawarwakin waɗanda suka mutu.
Hatsarin ya faru ne a Igbokoda, wani yanki mai ruwa da ke
jihar Ondo, inda yanayin fadama ya sa isa wurin da jirgin ya faɗi ke da matuƙar
wahala.
Tawagar BBC da ta
je wurin ba ta ga wata alama ta jirgin ko gawarwakin ba. Ana kyautata zaton
cewa jirgin da gawarwakin sun nutse ne cikin fadamar.
Sojoji sun kawo
wata mota ta musamman domin taimakawa wajen fito da tarkacen jirgin.
Sai dai kai kayan
aikin daga titi har zuwa inda fadamar take ya kasance abu mai wahala. Rundunar
sojin ta ce tana ƙoƙarin nemo hanyar da za ta kai ga wurin da jirgin ya faɗi.
An hana ’yan
jarida da mazauna yankin shiga cikin fadamar yayin da aikin ceto da fito da
tarkacen ke gudana.
Wasu daga cikin
mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa mutuwar mutanen ta girgiza su sosai,
musamman ganin cewa waɗanda suka mutu jami’an soja ne da ke aikin kare ƙasar.
Jirgin da
hatsarin ya rutsa da shi samfurin ATR 42 ne, irin jirgin da wasu rundunonin
soja ke amfani da shi wajen sintiri da sa ido a teku.
Najeriya na
dogaro da sintirin jiragen yaƙi a sama don lura da dogon gabar tekunta da ruwan
da ke ƙarƙashin ikonta, da kuma tallafa wa ayyukan soji na yaƙi da ƙungiyoyin
masu ɗauke da makamai.
Rashin jirgin da
ake amfani da shi wajen wannan aikin na iya janyo matsin lamba kan sauran jiragen rundunar, a daidai lokacin
da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
Rundunar sojin
saman Najeriyar na taka muhimmiyar rawa a ayyukan yaƙi da ƙungiyoyi masu ɗauke
da makamai da kuma sa ido kan iyakokin ƙasar da ruwanta.
Messi ya buga wasansa na ƙarshe a tawagar Argentina
Asalin hoton, Getty Images
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Lionel Messi,
ya buga wasansa na ƙarshe a tawagar ƙasar Argentina.
Messi ya ci kwallo daga bugun fenariti tare da taimakawa
wajen zura sauran kwallaye biyu a wasan da Argentina ta doke Benin da ci 3-0 a
wani filin wasa da ya cika maƙil da magoya baya a birnin Buenos Aires
Da yake magana bayan wasan, Messi ya ce wakiltar Argentina
ita ce mafi girman abin alfahari da zai iya samu a rayuwarsa ta wasanni.
Tun da farko ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa
wasa bayan Argentina ta sha kashi a hannun Spaniya a wasan ƙarshe na gasar
Kofin Duniya.
Sai dai Messi ya ce zai ci gaba da taka leda a matakin
ƙungiyoyi a ƙasar Amurka.
Shekara uku da hare-haren Hamas na 7 ga Oktoban 2023 kan Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
An yi shiru na tsawon minti guda a faɗin Isra’ila domin tunawa
da cika shekaru uku da harin ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin
mutuwar mutane sama da 1,100 a wani farmaki da ƙungiyar Hamas ta jagoranta daga
Zirin Gaza.
A yayin harin, an
kuma yi garkuwa da mutum 251.
Haka kuma ana
gudanar da tarukan tunawa da waɗanda suka mutu a birane daban-daban na duniya.
A martanin da
Isra’ila ta mayar, sama da mutane 74,000
ne suka mutu a Gaza, yayin da hare-haren suka lalata manyan sassan Zirin Gaza
da mayar da su kufai da baraguzan gine-gine.
Matar da ta ƙi mutuwa bayan yi mata allurar kisa ta farfaɗo - Lauyoyinta
Asalin hoton, Tennessee Department of Corrections
Lauyoyin Christa Pike, Ba’amurkiyar da ta tsallake rijiya da
baya bayan yunƙurin aiwatar da hukuncin kisa da ya ci tura a makon da ya gabata
a kan ta, sun ce ta farfaɗo kuma tana iya magana.
Sun ce tana karɓar kulawar likitoci na musamman, amma har
yanzu hannayenta a daure suke duk da tana kwance a asibitin.
Wakilin BBC ya ce har yanzu akwai tambayoyi da dama da ke
buƙatar amsa a kan halin da ta ke ciki, to amma duk da haka sun ce samun
sauƙinta sosai zai ɗauki lokaci.
Lauyoyin sun sake kira da a sassauta hukuncin kisan da aka
yanke mata.
An dai yi yunƙurin yi mata allurar kisa har sau biyu, amma
dukkan yunƙurin bai yi nasara ba.
Assalamu alaikum
Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Laraba.
Ku kasance da wannan shafi don sanin irin wainar da ake toyawa a sassan duniya, inda za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtan ƙasashe.
Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa a kan labaran da muke wallafawa.