Infantino ya nemi afuwa kan shirin sayar da hannun jarin Kofin Duniya
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya nemi afuwa kan kura-kuran da ya tafka dangane da wani shiri mai cike da ce-ce-ku-ce na sayar da hannun jari a wasu gasannin ƙwallon ƙafa ga masu zuba jari masu zaman kansu.
Sai dai duk da sukar da ya fuskanta, Infantino zai ci gaba da riƙe muƙaminsa bayan ya samu goyon bayan manyan shugabannin FIFA a wani taron da aka gudanar a Maroko.
Da alama ya shirya sake neman kujerar a karo na hudu da za a gudanar da zaɓe a watan Maris na shekarar 2027.
Infantino ya gayyaci mambobin kwamitin gudanarwar FIFA zuwa hedikwatar hukumar ta nahiyar Afirka da ke Maroko a ranar Laraba, domin tattauna batun bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi kan yunƙurin sayar da hannun jari a gasannin ƙwallon ƙafa.