Najeriya ta yi rashin nasara a hannun Malawi da ta zo Wafcon a karon farko

Asalin hoton, XMalawiteam
A karon farko Najeriya ta yi rashin nasara a hannun sabuwar tawagar da ta fara halartar Kofin nahiyar Afrika a karon faro tun bayan fara gasar a 1998.
Tawagar Scorchers da take halartar gasar a karon farko ta kafa tarihi a halartar gasar da ta yi a karon farko inda ta doke gwarzuwar gasar da ta lashe ta sau 10 a tarihi a filin wasa na Al Madina da ke Rabat.
Kwallaye uku da Malawi ta ci a wasan daga hannun Temwa Chawinga da 'yar uwarta Tabita Chawinga sun tabbatar da nasarar da ta samu da ci 3-2 kan Suoer Falcons.
Haduwar da Malawi ta yi da Najeriya ina ce ta 18 da Super Falcons ta yi da sabbin zuwa gasar.
Gabanin wannan wasan Super Falcon ba ta taba rashin nasara ba a hannun sabbin zuwa gasar a wasanni 17 da ta yi a baya, inda ta ci 16 ta yi canjaras daya.




















