Yadda al'umomi a jihar Neja ke gudun hijira a Jamhuriyar Benin saboda ƴanbindiga

Hoton 'yanbindiga sanye da kayan soji dauke da makamai

Asalin hoton, NPF

    • Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Bayanai daga yankin karamar hukuma Borgu ta jihar Neja, sun ce jama'ar garuruwa da dama na yin gudun hijira zuwa garuruwan wasu jihohin kasar, har ma da tsallakawa zuwa makwabciyar kasar, jamhuriyyar Benin, inda suka sami mafaka don guje wa hare-haren 'yan bindiga.

Hakan na faruwa ne duk da matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka domin tabbatar da tsaro a yankin.

Wani mazaunin daya gada cikin garuruwan da ke kan iyakar Najeriya da jamhuriyyar Benin, ya yi wa BBC bayani kan wannan mawuyacin hali da ya ce suna ciki:

''To ba ka da gida an kone, ba ka da gona an hana ka noma, to ya za ka yi da rayuwarka? Ka ga dole ka kaura.''

Gudun hijirar da jama'ar garuruwan ke yi dai ta samo asali ne daga gagarumin hari na baya-bayan nan da 'yan bindiga suka kaddamar a wasu garuruwa, in ji mutumin yankin:

''Juma'ar waccan da ta wuce sun kwashi jama'a kusan 500, ranar Juma'a a garuruwan da suka hada da Dekara da wani gari Masaka da Maciyar-gyada da Gizan-zana da Sabon-gida.''

''Sannan an yanka kusan mutum 35 yanda ka sana ana yanka dabba, kuma an tafi da kimanin mutum 500 kowa ya gan su a midiya kuma suna hannunsu har yanzu.''

Bayanan dai sun nuna cewa al'ummomin garuruwan da ke cikin wannan garari sun kai akalla goma sha biyar, kamar yadda mazaunin yankin ya sheda wa BBC.

Ya ce garuruwan sun hada da, Maciyar-Gyada da Masaka da Ikara da Gidan-Zana da Sabon-Gida da Kokani da Konkonso da Aljana da Tungan-Makeri da Damago da sauransu.

Sai dai kuma dangane da matakan tsaro wasu daga cikin al'ummomin yankin sun ce sojoji suna bakin kokarinsu:

''Don an kai sojoji yanzu haka. Akwai wani sabon sansanin soja da aka bude suna wajen yanzu haka,'' in ji wani dan yankin.

Yadda hare-haren suka kasance

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Juma'a 21 ga watan Agustan nan da ya kare na 2026, 'yan bindiga da ake kyautata zaton suna da alaƙa da ƙungiyar Lakurawa ko kuma Mahmuda suka kai hare-hare a ƙauyuka huɗu da ke ƙaramar hukumar ta Borgu a jihar ta Neja.

Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Gbeji (Gidan-Zana), Kpenya, Giyan Gbasu da Dekara.

A ƙauyen Dekara, wanda shi ne mafi girma a cikin yankunan da aka kai wa hari, maharan sun kutsa cikin babban masallacin garin yayin da jama'a ke gudanar da sallar Juma'a, inda suka yi garkuwa da fiye da mutum 60, kamar yadda jami'ai da mazauna yankin suka bayyana.

Kwana biyu bayan harin, wani hoton bidiyo ya fara yawo a kafafen sada zumunta, inda aka ga mutane da dama daga cikin waɗanda aka sace suna zaune tare a wani fili.

Bidiyon ya nuna tsofaffi da yara ƙanana a cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, yayin da wani mutum da ba a gani a bidiyon ba ke kira ga iyalansu su fito su gane 'yan uwansu daga cikin mutanen da ake tsare da su.

Wannan salo ya yi kama da dabarar da aka yi amfani da ita bayan harin da aka kai Woro a Jihar Kwara a watan Fabarairun da ya wuce (2026), lokacin da maharan suka wallafa bidiyon waɗanda suka kama tare da iƙirarin riƙe fiye da mutum 170.

Wannan ne karo na uku cikin 'yan lokutan nan da Dekara da ƙauyukan da ke kewaye da ita suka fuskanci irin wannan hari.

A wani harin da aka kai a baya, mazauna yankunan sun tsere gaba ɗaya, inda wasu suka samu mafaka a wasu garuruwa a jihar ta Neja da ma Kwara, yayin da wasu suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Benin.

Sai dai babban abin da ke jan hankali shi ne yadda harin ya sake faruwa makonni kaɗan bayan wani babban aikin ceto da hukumomin tsaro suka yi.

A ranar 5 ga Agustan 2026, jami'an tsaron Najeriya sun kuɓutar da mutum 308 da aka tsare a cikin dajin Kainji.

Daga cikinsu, mutum 163 sun fito ne daga Woro a karamar hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, yayin da mutum 145 suka fito daga al'ummomin Borgu da suka haɗa da Kasuwan Daji, Konkonso da Pissa a Jihar Neja.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aikin a matsayin mafi girman aikin ceto da aka taɓa yi a rana guda a tarihin ƙasar.

Sai dai kwanaki 16 kacal bayan wannan nasara, rahotanni sun nuna cewa maharan sun sake komawa, inda suka kai hari a masallatai da wasu garuruwa a yankin na Borgu tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Lamarin na ƙara sa fargaba da damuwa kan yadda za a tabbatar da tsaro mai ɗorewa a yankunan da ke fama da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai duk da nasarorin da jami'an tsaro ke samu a wasu lokutan.

Kokarin da BBC ta yi na jin ta bakin shugaban karamar hukumar ta Borgu, Abdullahi Mohammed Nasir, dangane da halin da ake ciki, hakan bai samu ba, saboda kasa samun sa ta waya.