Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda aka zane ni a bainar jama'a saboda aikata zina'
GARGAƊI: Wasu bayanan da ke cikin wannan rahoto na iya tayar da hankalin mai karatu.
"Lokacin da suka gabatar da ni a gaban kotun ɗaukaka ƙara, an ɗaure hannayena kuma an rufe mani fuska. Sun yi mani bulala 39 a bainar jama'a. Sun riƙa ƙirga bulalar a kan wata takarda mai ɗauke da sunana, inda suka rubuta yawan bulalar da aka yi mani.''
Kalaman Manizha (wadda muka canza sunan ta saboda ba ta kariya) kenan. Manizha tana daga cikin mata biyu da suka yi hira da BBC a kan yadda jami'an Taliban suka zane su saboda zargin aikata laifuka daban-daban.
BBC ta samu zantawa da biyu daga cikin mata da yawa da kotu, a ƙarƙashin gwamnatin Taliban ta yanke wa hukuncin zaman gidan yari a cikin shekara biyar kuma waɗanda tuni aka zartar masu da hukuncin.
Manizha mai shekara 26 tana zaune ne a wani ƙauye da ke ɗaya daga cikin gundumomin ta Afghanistan. Saboda dalilan tsaro wannan rahoto ya ɓoye wasu bayanai game da rayuwa da wajen zama da iyalai da kuma yanayin da waɗannan mata biyu ke ciki.
Ta bayar da labarin yadda jami'an gwamnatin Taliban suka kama ta tare da saurayin ta:
"Ina soyayya da wani kuma ina fatan zai kai ga ya aure ni, amma abin takaici sai aka kama mu. Ban san yadda Taliban suka gano muna soyayya, ko kuma waye ya kai masu tsegumi ba. Muna cikin mota sai wasu mutane biyu daga hedikwatar ƴansanda suka zo suan tambayar mu: 'me kuke yi? mene ne alaƙar ku? kuma ina za ku je?''
Tun bayan da ta koma karagar mulki a watan Ogustan 2021, gwamnatin Taliban ta koma salon zane masu laifi a bainar jama'a bayan yanke masu hukunci.
A watan Nuwamban 2022, shugaban gwamnatin Taliban, Haibatullah Akhundzada, ya umarci alƙalai su riƙa zartar da haddi kan wasu laifuka da hukuncin su ya haɗa da yanke wasu sassan jiki da jefe masu laifi, a bainar jama'a.
An bayar da wannan umarni a ranar 13 ga watan Nuwamba kuma hakan ya sa an samu ƙaruwar yawan mutanen da aka yankewa irin wannan hukunci cikin sauri.
Kwana biyar bayan wannan umarni, a ranar 19 ga watan Nuwamba gwamnatin Taliban ta zartar da hukunci kan mutane 19 a yankin Takhar, cikin su harda mata 9, kuma an same su da laifuka da suka haɗa da sata da zina da guduwa daga gida inda aka yi masu bulala 39 kowacce.
Kotun ƙoli ta gwamnatin Taliban ta tabbatar da wannan a cikin wata sanarwa. An kuma zartar da hukunci a kan wasu maza biyu a kudu maso yammacin Farah da kuma Gabashin Laghman.
Shaima - (ba asalin sunan ta ba ne), wata mata daga gabashin Afghanistan ta zanta da wakilan BBC, inda ta bayar da labarin yadda jami'an Taliban suka zane ta a lokuta da dama, har suka tsinke mata gashi kafin a fara zaman shari'ar ta.
Ta ce "Sun gabatar mani da wata takarda kuma suka nemi in amsa cewa: 'Eh, ni mace ce da ta fita daga addini, ina da alaƙa da maƙiya addini kuma na yi magana a keɓe da wani mutum da ba muharrami na ba.''
Ta ƙara dace: ''A ranar Juma'a da misalin ƙarfe 8:30 na dare aka yi mata bulala 39. Tana ihu tana kabbara a duk lokacin da aka zabga mata bulala. An zane ne sosai ta yadda har kaina ba bugi ƙasa. Bayan hutun minti 10 zuwa 15 sai suka tattauna a tsakanin su sannan suka ƙara yi mani bulala 21.''
Ta shaidawa BBC cewa mutane aƙalla 200, ciki harda mata da matasa da kuma ƙananan yara ne suka taru domin kallon yadda aka zane ta.
Ta ce, ''Bayan an kammala zane ne sai dattawa dadama suka matso kusa suna gargaɗin kada in sake, sannan suka bani shawarar in bar wajen.''
Manizha, wadda a yanzu take zaune a ƙauyensu, ta ce yadda jama'a ke alaƙa da ita ya sauya sosai bayan bulalar da aka yi mata. Ta bayyana yadda aka fara tsangwamar ta hatta a tsakanin ƴan uwanta da kuma sauran jama'ar gari.
Manizha ta ce: "Na shiga mummunan yanayi a gidan yari, ta yadda har na kasa bai wa mahaifiyata labarin halin da na shiga. An muzguna mani, kuma bayan an sake mu sai aka sanya muka yi alƙawarin ba za mu taɓa bayyana cewa mun yi zaman gidan yari ba.''
Ta ci gaba da bayar da labarin cikin takaici da hawaye: "Rayuwa ta fita raina. Na sha alwashin da zarar na fita daga gidan yari, abu na farko da zan yi shi ne in kashe kaina. Abokaina sun juya mani baya, aure kuwa, ko tunanin shi bana yi.''
"Da dare suna ɗaure mana hannaye, kuma ban san ko su wane ne ba, ko matasa ne ko kuma tsaffi, amma suna shiga har cikin ɗakinmu,'' in ji Manizha.
Ta ɗan yi shiru sannan ta ci gaba cikin rawar murya: "Ku yi haƙuri, akwai abubuwan da ba zan iya bayyanawa ba."
Ta bayyana yadda zaman ta a gidan yarin ya sa ta manta duk wani abu da ya shafe ta a rayuwa kafin wannan lokaci, kama daga makaranta da yadda ta zamo ba ta iya bacci da yadda ta daina jin daɗin abinci da kuma yadda rayuwa ta fitar mata a rai saboda kowa ya juya mata baya, sai mahaifiyar ta kaɗai ke tare da ita.
Ita ma Sheema ta ce har yanzu matsalar ƙwaƙwalwa da ta samu bayan zaman gidan yarin na ci gaba da bibiyar ta. ''Bayan abin da ya faru, duk lokacin da na ga mutane biyu suna magana sai in fara zargin suna tattaunawa ne a kai na,'' in ji ta.
Ta ce: ''Har yanzu ina da tabbai a kafaɗata. Bana iya bacci a kan ɓangaren. Na ɗauka an karya mani ƙashi ne.
Ta ƙara da cewa abin ya shafi hatta rayuwar ƴaƴanta: ''Babbar ɗiyata, har yanzu tana farkawa tsakar dare cikin firgici tana mafarkin ana zane ta ko kuma an kashe ta. Raɗaɗin da nake ji a duk lokacin da na ga ƴaƴana a cikin tsoro da firgici iri ɗaya ne da wanda nake ji a lokacin zaman gidan yari.''
Yana da kyau a sani cewa gwamnatin Taliban ta musamnta zargin muzgunawa fursunoni mata da kakkausar murya, inda ta dage cewa ana bin dokar shari'ar musulumci wajen tsare su.
A wata hira da BBC a baya, kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce mata ne ke kula da fursunoni mata a Afghanistanwomen.
Ya ce: "Muna ba ku tabbacin cewa ba a duka ko muzgunawa fursunoni a gidajn yarin Afghanistan, kuma ana kula da fursunoni ne a bisa tanadin dokar musulumci.''
Binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa daga watan Nuwamban 2022 zuwa 15 ga watan Ogustan 2023, bayan gwamnatinTaliban ta sanar da komawa zartar da hukuncin kisa a hukumance, mutane 346 aka zartawa hukuncin.
Yawan mutanen da ake zartarwa hukuncin ya ƙaru bayan 13 ga watan Nuwamban 2022. A lokacin ne jagoran Taliban, Haibatullah Akhundzada, ya umarcin ɓangaren shari'a ya zartar da hukuncin shari'ar musulumci a kan wadanda aka samu da laifuka.
An zartar da hukuncin kisa a kan wasu yayin da aka tura wasu gidan yari.
Alƙaluman kotun ƙoli ta Taliban sun nuna cewa mutane aƙalla 241, maza 210 da kuma mata 31 aka zartarwa hukuncin kisa a 2024.
A 2025, adadin ya ƙaru zuwa 395, da suka haɗa da maza 317 da kuma mata 78.
A 2026, kotun ƙolin Taliban ta ci gaba da wallafa rahoton zartar da hukuncin shari'a har zuwa ranar 22 ga watan Afirelu, amma daga nan sai aka daina wallafa rahoton. Alƙaluman da aka tattara a wancan lokacin sun nuna an zartar da hukuncin kisa kan mutane 214 da suka haɗa da maza 184 da kuma mata 30.
Amma ba kowanne zartar da hukunci bane ake wallafawa a shafukan kotun ƙolin Taliban, kuma hakan na nuni da cewa yawan mutanen da aka yi wa bulala da waɗanda aka muzgunawa ya zarce alƙaluman da mahukunta suka fitar.