Fitattun ƴan takarar gwamnan jihar Osun

Wasu daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar Osun

Asalin hoton, FB/Multiple

Bayanan hoto, Wasu daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar Osun
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

A ranar Asabar 15 ga watan Agustan nan al'ummar jihar Osun da ke kudu maso yammacin najeriya za su fita rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamnan da zai jagorancin jihar tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

Ƴantakarar 15 ne ke takarar kujerar gwamnan jihar da zaɓenta ya kasance a koyaushe mai cike da taƙaddama.

BBC ta zaɓo wasu ƴan takara guda biyar da ake hasashen takarar tasu za ta fi zafi.

Ademola Adeleke - APP

Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar Osun

Asalin hoton, Senator Ademola Adeleke/Facebook

Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar Osun a halin yanzu kuma ɗaya daga cikin 'yan takarar zaɓen gwamna, an haife shi ne a ranar 13 ga Mayun 1960 a garin Ede, jihar Osun.

Ya fito daga cikin iyali mai tasiri a siyasa - Mahaifinsa shi ne Sanata Raji Ayoola Adeleke, yayin da mahaifiyarsa, Nnenna Esther Adeleke, ta fito daga yankin Akwete da ke ƙaramar hukumar Ukwa West a jihar Abia.

Ademola Adeleke ya shiga harkar siyasa a shekarar 2001 tare da ɗan'uwansa, Sanata Isiaka Adeleke, wanda ya rasu a watan Afrilun 2017.

Bayan rasuwar ɗan'uwansa, Ademola Adeleke ya tsaya takarar kujerar Sanatan Osun ta Yamma , inda ya samu nasara a zaɓen cike gurbi na shekarar 2017 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Kafin komawarsa PDP a watan Afrilun 2017, Adeleke ya kasance mamba a jam'iyyar APC.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga baya, ya shiga takarar gwamnan jihar Osun, inda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyarsa bayan ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Akin Ogunbiyi, da ƙuri'u bakwai kacal. Bayan haka ya tsaya takarar gwamna a zaɓen da aka gudanar a ranar 23 ga Yulin 2018.

A watan Disamban 2025, Adeleke ya koma jam'iyyar Accord, inda ya samu tikitin takarar gwamna domin neman wa'adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar Osun.

A ranar 22 ga Maris, 2019, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar zaɓe ta ƙasar ta ce bai kammala ba. Amma daga bisani, a ranar 5 ga Yulin 2019, Kotun Ƙolin Najeriya ta soke wannan hukunci tare da tabbatar da Gboyega Oyetola a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun na 2018.

A zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga Yulin 2022, Adeleke ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, inda ya samu nasara kan gwamna mai ci a wancan lokaci, Gboyega Oyetola.

Adeleke ya samu ƙuri'u 402,979, yayin da Oyetola ya samu 375,027, abin da ya ba shi damar lashe zaɓen.

Ademola ya yi karatun Kimiyyar Siyasa (Political Science) a Jami'ar Jacksonville State University da ke jihar Alabama, Amurka.

Ademola Adeleke fitaccen ɗan kasuwa ne kuma ƙwararren mai gudanarwa.

A cewar bayanan da aka bayar, ya riƙe mukamin Babban Darakta na kamfanin Guinness Nigeria Plc tsakanin shekarun 1992 zuwa 1999.

Haka kuma, ya kasance Babban Daraktan kamfanin Pacific Holdings Limited daga shekarar 2001 zuwa 2016. Kafin wannan, ya yi aiki da kamfanin Quicksilver Courier da ke Atlanta, jihar Georgia ta Amurka tsakanin 1985 zuwa 1989.

Adeleke ya kuma yi aiki da kamfanin Origin International LLC da ke Atlanta, Georgia, inda ya riƙe mukamin mataimakin shugaban kamfanin tsakanin 1990 zuwa 1994.

Folasayo Salaam - ADC

Folasayo Salaam

Asalin hoton, @Najeem Salam Fcbk

An haifi Najeem Folasayo Salaam a ranar 8 ga Agustan 1965 a garin Ejigbo da ke jihar Osun, inda ya taso.

Najeem Salaam Musulunci ne.

Najeem Salaam ya fara shiga harkar siyasa tun yana ɗalibi a jami'a, inda ya kasance cikin ƙungiyar ɗaliban na masu nazarin kimiyyar siyasa.

A shekarar 2002, ya tsaya takarar kujera a ƙaramar hukumarsa amma bai yi nasara ba. Daga bisani, a 2007, ya tsaya takarar kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Osun, inda ya samu nasara.

A shekarar 2009, rikicin siyasa ya haifar da rufe majalisar bayan an yi korafi cewa tambarin jam'iyyarsa bai bayyana a takardar zaɓe ba, tare da zargin samun wasu kura-kurai a tsarin zaɓen.

A 2011, ya sake tsayawa takara domin wa'adi na biyu a Majalisar Dokokin Jihar Osun, inda ya sake samun nasara.

A zaɓen 2015, ya sake lashe kujerarsa, sannan ya ci gaba da zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun har zuwa shekarar 2018, lamarin da ya sanya ya kasance cikin 'yan majalisa masu dadewa a majalisar jihar.

A shekarar 2012, an naɗa shi shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na Ƙungiyar Kakakin Majalisun Dokokin Jihohi ta Najeriya.

Daga baya ya yi aiki a kamfanin sadarwar tauraron ɗan adam mallakin gwamnatin tarayya, Nigerian Communications Satellite Limited (NIGCOMSAT), inda ya riƙe muƙaman gudanarwa da suka haɗa da shugaban sashen kasuwanci da bunƙasa harkokin kasuwanci.

Mutane da dama daga cikin magoya bayansa sun fi sanin sa da laƙabin "Iwaloye."

Najeem Folasayo Salaam

Asalin hoton, @Najeem Salam Fcbk

Alƙawurra:

Daga cikin muhimman abubuwan da ya yi alƙawarin mayar da hankali a kansu idan ya zama gwamna akwai:

  • Gyara da inganta tsarin ilimi
  • Ƙarfafa tsaro a faɗin jihar
  • Bunƙasa tattalin arzikin jihar Osun
  • Haɓaka harkokin noma
  • Inganta walwala da jin daɗin al'umma
  • Ƙarfafa ayyukan ci gaba da samar da damammaki ga mazauna jihar

Olufemi Adesuyi - ZLP

Olufemi Adesuyi

Asalin hoton, Adesuyi John Olufemi/Facebook

An haifi Olufemi Adesuyi a ranar 7 ga Yulin shekara ta 1976, kuma ya yi karatun Kimiyyar Kwamfuta da Injiniyan Kwamfuta a Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, a jihar Osun.

Adesuyi kuma shi ne shugaban kwalejin ƙirƙira da fasaha ta Living Spring College of Technology and Innovation da ke Osogbo, a jihar Osun.

Baya ga haka, Adesuyi mutum ne mai kishin addini, wanda ya jajirce wajen bautar ubangiji kuma sananne ne da tsayuwa kan abin da ya yi imani da shi.

Adesuyi ya shiga harkar siyasa a shekarar 2015 da nufin yi wa al'ummarsa hidima. Sai dai ya fara fitowa takara ne a shekarar 2019 a ƙarƙashin jam'iyyar ZLP.

A zaɓen 2019, Adesuyi ya tsaya takarar kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Ife ta tsakiya, Ife ta Arewa, Ife ta Kudu da Ife ta Gabas. Sai dai bai yi nasara ba, inda ya samu ƙuri'u 96 kacal, lamarin da ya sa ya kasance a baya sosai a jerin 'yan takarar da suka fafata.

Ba wannan kaɗai ba, Adesuyi ya sake tsayawa takarar gwamnan jihar Osun a shekarar 2022 ƙarƙashin jam'iyyar siyasa ɗaya, inda ya samu ƙuri'u 364.

Daga cikin dukkan 'yan takarar da suka fafata a waccan shekara, Adesuyi ne ya zo na ƙarshe a sakamakon zaɓen.

Burin Adesuyi da ƙudirinsa na jagorantar gwamnatin jihar Osun ne suka sa ya sake tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2026.

Alƙawari:

Adesuyi ya yi alkawura da dama ga al'ummar da mazauna jihar Osun, idan suka zaɓe shi a matsayin gwamna a ranar 15 ga Agustan 2026.

Daga cikin alkawuran da ya ɗauka sun haɗa da:

  • Samar da ayyukan yi ga matasa
  • Gyara da sake fasalin fannin kiwon lafiya
  • Bunƙasa tsarin ilimi
  • Inganta hanyoyi
  • Tabbatar da jin daɗin jama'a da ma'aikatan gwamnati.

Olajide Esan - AAC

Olajide Esan

Asalin hoton, Olajide Esan/X

An haifi Olajide Esan a garin Ejigbo da ke jihar Osun a shekarar 1986.

Ya kammala karatun digiri na farko (BSc) a fannin fannin nazarin duniya da gudanarwa wato Geography and Resource Management a Jami'ar Jihar Osun (UNIOSUN).

Bello Muideen Yekeen ne aka zaɓa a matsayin mataimakinsa a takarar gwamnan jihar Osun. Olajide Esan ɗan kasuwa ne mai harkar sayar da motoci.

A cewarsa, ya fi sauran 'yan takara cancanta, abin da kawai ba ya da shi shi ne kuɗi.

Ya ce abin da ya fi bai wa muhimmanci shi ne mayar da gwamnati hannun jama'a, ta yadda za su riƙa bayyana abin da suke so kuma a saurare su.

Ya ce wani shiri da ya kira Rumbun bayanan al'ummar jihar Osu" wato "Osun Residence Data Base" zai taimaka masa wajen sanin yawan manya da yara a jihar Osun da kuma buƙatunsu, domin gwamnati ta tsara ayyuka da manufofi bisa ga waɗannan bayanai.

Haka kuma ya ce yana da wani tsarin kula da harkokin kuɗi da ya kira "Financial Dashboard".

"Wannan zai bai wa al'ummar jihar Osun damar sanin yawan kuɗin da ke shiga asusun gwamnati, nawa ake kashewa, da kuma abin da ya rage. Ta haka idan aka rasa ko naira ɗaya, za su iya tambayar gwamnati inda kuɗin ya shiga," in ji Olajide.

Ya kuma ce gwamnatocin baya sun ɗora wa jihar Osun bashin da zai kai kusan naira miliyan ɗaya kan kowane ɗan jihar, don haka ya kamata al'umma su riƙa tambayar yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati.

Bugu da ƙari, ya ce zai samar da wani tsari na kare haƙƙin jama'a, inda za a riƙa sauraron koke-koken mazauna Osun tare da tabbatar da adalci tsakanin waɗanda ba su da laifi da waɗanda aka samu da laifi.

Munirudeen Bola Oyebamiji - APC

Daya daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar Osun shi ne Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, wanda aka fi sani da AMBO.

Asalin hoton, Bola Oyebamiji/Facebook

Daya daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar Osun shi ne Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, wanda aka fi sani da AMBO.

Laƙabin AMBO ya samo asali ne daga haruffan farkon sunayensa, kuma sunan ne da ya shahara da shi a tsakanin mutane.

AMBO, wanda ke takara a ƙarƙashin jam'iyyar APC, na ɗaya daga cikin manyan 'yan adawar da ke ƙalubalantar gwamna mai ci, Ademola Adeleke, a zaɓen gwamnan jihar Osun.

A matsayinsa na ɗan takarar APC, AMBO na neman karɓar ragamar jagorancin jihar daga hannun gwamnatin da ke kan mulki a halin yanzu.

An haifi Munirudeen Bola Oyebamiji a ranar 17 ga Nuwamban 1965 a garin Ikire, da ke ƙaramar hukumar Irewole a jihar Osun.

A matsayinsa na ɗan takarar jam'iyyar APC, AMBO ya fara aikinsa ne a fannin banki da harkokin kuɗi.

Ya yi aiki a bankuna daban-daban da suka haɗa da:

  • Wema Bank
  • Trans International Bank
  • Spring Bank
  • Enterprise Bank

Baya ga haka, AMBO ya riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Osun sau biyu, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara da gudanar da manufofin kuɗaɗen gwamnati da tattalin arzikin jihar.

Oyebamiji ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Osun a zamanin gwamnatocin Rauf Aregbesola da Gboyega Oyetola, lokacin da suke shugabantar jihar.

Haka kuma, AMBO ya kasance Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Ruwa da Sufuri a zamanin tsohon gwamna Gboyega Oyetola.

Daga baya ya jagoranci Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Cikin Gida ta Ƙasa, National Inland Waterways Authority (NIWA). Sai dai ya yi murabus daga muƙaminsa a watan Oktoban 2025 domin mayar da hankali kan takararsa ta gwamnan jihar Osun a zaɓen shekarar 2026.

Daya daga cikin manyan alƙawuran da AMBO yake yi wa al'ummar jihar Osun shi ne amfani da iliminsa da gogewarsa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Ya ce idan aka zaɓe shi gwamna, zai samar da ayyukan yi ga matasa tare da aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa tattalin arzikin jihar Osun da bunƙasa harkokin kasuwanci.