Matsalar tsaro: Buƙatu biyu da ƴanmajalisar Najeriya suka miƙa wa Tinubu

Asalin hoton, AFP
Ɓangaren marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya buƙaci shugaba Tinubu ya kai ziyara jihohin Neja da Zamfara da Sokoto bayan sace mutane da dama a hare-haren yanbindiga.
Ƴan majalisar sun ce sun tsaya sun Nazari shin babu kudi ne da aka ki amfani da su don magance wannan matsala ta tsaro da ta addabi wadannan jihohi, ko kuma akwai kudin amfani da su ne yadda ya kamata ba'ayi.
Hon Abdussamad Dasuki, shi ne mataimakin shugaban marassa rinjaye a majalisar wakilan ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, sun riga sun sani cewa akwai kudaden da za a iya yakar 'yan ta'addan nan, idan babu to aje a dauko kudaden Najeriya da aka ajiye a a asusun ajiya na kasashen waje don ayi amfani da su wajen kawo karshen wannan matsala ta tsaro.
Ya ce,"Kamar yadda aka yi a jihar Oyo, lokacin da aka sace dalibai, to azo arewacin Najeriya ma a zagayeta da jami'an tsaro, ma'ana duk inda ake zaton akwai wadannan 'yan ta'adda to a zagaye wajen to cikin ikon Allah za a ga an samu nasara wajen kakkabe wadannan batagari."
" Mu muna ganin idan aka je asusun ajiyar Najeriya na kasashen waje aka ciro kamar dala biliyan biyar aka zo aka yi abin da ya dace, to cikin wata daya zuwa uku za a ga an shawo kan wannan matsala ta tsaro." In ji shi.
Hon Abdussamad, ya ce," A gaskiya mu ba mu gamsu da yadda ake tunkarar matsalar tsaro ba, domin abin da ya kamata ace an yi don magance matsalar ba a yi haka, tun yaushe ake cikin dokar ta baci akan batun tsaro to me aka yi babu."
Ya ce," Shi shugaban kasa a matsayinsa na askarawan Najeriya kamata ya yi ya ja gaba wajen yaki da wadannan 'yan ta'adda, domin idan za a tuna a kwankin baya ya je jihar Fulato ya yi jaje har ya ce ayi duk abin da za a yi domin kawo karshen kashe-kashen da ake a jihar, to amma me ya yi a jihohinmu shin ya je?.
" Yanzu a matsayinsa na shugaban kasa ya je garin Zamfara ya kwana biyu zuwa uku to ko shakka babu jami'an tsaro za su shiga dazukan nan, sanann daga nana ce ya zuwa Sokoto ya gane ma idanuwansa abubuwan da ke faruwa, sannan ya je Neja ma, to ko shakka babu idan har ya yi hakan dole za a ga sauyi." In ji shi.
Dan majalisar ya ce," Yanzu duk wani abu da za a yi don a datse dazukan da ke arewacin Najeriya, ya kamata ayi shi, ma'ana akai sojoji su mamaye dazukan sannan ayi amfani da na'urori wajen gano ainihin inda wadannan mutane suke, to ko shakka babu za a samu nasara, don mun ga abin da aka yi a Oyo, mu me yasa ba za a yi hakan ba a jihohi arewacin Najeriya?."
Najeriya dai ta jima tana fama da matsalolin tsaro, inda ƴanbindiga a sassan ƙasaer da dama ke kai hare-hare da kashe mutane tare da kama wasu domin neman kuɗin fansa.
Ƙungiyoyin ƴanbindiga irin su Boko Haram da ISWAP da ƴan fashin daji ne ke yawaitar kai hare-hare.
Ƴanbindiga kan sace mutane domin neman kuɗin fansa, wasu kuma sukan yi garkuwa da su kariya daga hare-haren jami'an tsaro.
''Yankin arewa maso yammacin Najeriya ne kan gaba a yawan mutane da aka yi garkuwa da su.











