Ana kyautata zaton an gano abin da zai magance kansar da ke da wuyar warkewa

    • Marubuci, Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Tifaftiraha caafimaadka dhijitaalka ah
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Masana sun bayyana wannan a matsayin babban cigaba mafi muhimmanci da aka samu cikin shekaru da dama wajen magance cutar kansar ƙoda wato pancreatic cancer.

Wannan maganin ƙwaya ce da ake sha kullum, wanda ya nuna alamun rage girman ƙwayoyin cutar dajin, kuma a wasu marasa lafiya yana iya ma kawar da su gaba ɗaya.

Wannan na da muhimmanci musamman saboda cutar tana daga cikin mafi haɗari kuma mafi wahalar magani.

A gwaje-gwajen farko na asibiti, ba a sake gano alamun cutar daji ba a jikin ɗaya daga cikin marasa lafiya 12 da suka karɓi maganin da ake kira daraxonrasib, tare da haɗa shi da maganin chemotherapy.

Haka kuma, ƙwayoyin cutar daji sun daina ƙaruwa a kusan dukkanin mutane 61 da suka shiga gwajin, waɗanda aka gano suna da cutar dajin pancreas mai tsanani wadda ta bazu zuwa wasu sassan jiki.

Sai dai likitoci sun jaddada cewa har yanzu ba a san tsawon lokacin da wannan magani zai iya ci gaba da dakile cutar ba. Saboda haka, ba za a iya ɗaukarsa a matsayin maganin da ke kawar da cutar daji gaba ɗaya ba a halin yanzu.

Wannan babban cigaba ne kuma abin farin ciki sosai

Hukumar bincike kan cutar kansa ta Ingila ta bayyana wannan a matsayin "babban ci gaban da aka samu cikin shekaru da dama wajen magance cutar dajin ƙoda."

Dakta Sam Godfrey, wanda ke aiki a wannan hukuma, ya shaida wa BBC cewa sakamakon gwajin yana da matuƙar ƙarfafa gwiwa.

"Abin da wannan sabon maganin ya samar shi ne hanyar magance wani abu da a baya ake ganin ba za a iya magancewa ba," in ji shi.

"A ƙarshe dai muna ganin ci gaba a fannin magance kansar ƙoda, ci gaban da aka daɗe ana jira."

An daɗe ana kallon cutar kansar ƙoda a matsayin ɗaya daga cikin cututtukan daji mafi wahalar magani, kuma tana da mafi ƙarancin yawan mutanen da ke rayuwa bayan kamuwa da ita idan aka kwatanta da sauran nau'ukan cutar daji a Birtaniya.

Ko da yake maganin chemotherapy kan rage girman ƙwayoyin cutar na ɗan lokaci, galibi cutar kan sake dawowa bayan wani lokaci.

Yawancin masu fama da kansar ƙoda mai tsanani kan rayu ne na watanni kaɗan, ba shekaru ba.

Sai dai likitoci na fatan cewa wannan sabon magani zai iya taimaka wa marasa lafiya su yi rayuwa na tsawon lokaci, ko da kuwa ba zai iya magance da cutar gaba ɗaya ba.

An bibiyi marasa lafiyar da suka shiga gwajin na tsawon kusan shekara ɗaya da rabi a matsakaici, kuma a wasu daga cikinsu cutar ba ta sake bayyana ba a wannan lokacin.

Sai dai ana buƙatar ƙarin bincike na dogon lokaci domin gano ko za a iya kai wasu daga cikin waɗannan cututtukan zuwa matakin da za su lafa sosai ko ma a yaƙe su gaba ɗaya, da kuma tsawon lokacin da wannan yanayi zai iya dorewa.

Sakamakon gwajin asibiti na mataki na farko da na biyu

- Kashi 90% na marasa lafiyar da suka shiga gwajin, ƙwayoyin cutar dajin da ke jikinsu sun daina ƙaruwa.

- Fiye da kashi 60% na marasa lafiyar, ƙwayoyin cutar dajin sun ragu ko kuma sun ɓace gaba ɗaya.

- A kusan kashi 8% na marasa lafiyar, wato mutum ɗaya cikin mutane 12, hoton CT bai nuna wata alamar cutar daji ba.

Ƙara tsawon lokacin rayuwa

Dsakta Wungki Park, daga Cibiyar Cutar Kansa ta Memorial Sloan Kettering a Amurka, kuma ɗaya daga cikin masu gudanar da wannan gwaji, ya ce sakamakon da aka samu zuwa yanzu yana matuƙar ƙarfafa gwiwa.

Ya ce: "Yanzu muna fara ganin cewa ba wai kawai yawan marasa lafiyar da ke samun sauƙi daga maganin ke ƙaruwa ba, har ma tasirin maganin yana ƙara ƙarfi, yayin da tsawon lokacin da ake iya shawo kan cutar ya kusan ninka sau biyu. Wannan kuma a ƙarshe na iya taimakawa marasa lafiya su rayu na tsawon lokaci."

Daraxonrasib magani ne da ke hana aikin sinadarin KRAS, wanda tuni aka amince da amfani da shi a Amurka. Yana aiki ne ta hanyar kama wasu ƙwayoyin halitta da ake kira RAS, sannan ya daƙile aikinsu. Ana samun waɗannan sauye-sauyen a yawancin masu fama da kansar ƙoda, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen girma da yaɗuwar ƙwayoyin cutar daji.

Sauran nau'ukan cutar daji, ciki har da kansar huhu da na ƙwai na mata (ovarian cancer), na iya kasancewa da irin waɗannan sauye-sauyen ƙwayoyin halitta. Wannan na nufin maganin na iya amfani ga marasa lafiya masu fama da wasu nau'ukan cututtukan daji daban-daban.

Dakta Sam Godfrey ya ce: "Ina fatan nasarar farko da muke gani a kansar ƙoda za ta ba da damar amfani da wannan magani wajen magance wasu nau'ukan cutar daji."

Sai dai ya jaddada cewa ana buƙatar ƙarin gwaje-gwaje na dogon lokaci da ƙarin sakamakon bincike.

Ya ce: "Cutar daji na iya dawowa ko da bayan gwaje-gwaje sun nuna babu wata alama da ta rage. Ba za a iya tabbatar da cewa mutum ya warke gaba ɗaya daga cutar ba sai bayan wani dogon lokaci ya wuce."

Farfesa Elena Garralda, shugabar cibiyar masu bincike kan cutar daji na Turai , inda aka gabatar da waɗannan sakamakon ga sauran masana, ta ce:

"Waɗannan sakamakon suna ba da kyakkyawar alama, domin suna nuna cewa haɗa magunguna tare na iya ƙara tsawon rayuwar marasa lafiya sosai, tare da tsawaita lokacin da ƙwayoyin cutar daji za su ɗauka kafin su sake fara girma."

A cewar Cancer Research UK, ana gano kusan mutum 11,500 da cutar dajin ƙoda a Birtaniya a kowace shekara, yayin da kusan mutum 10,200 ke mutuwa sakamakon cutar.

Fitaccen jarumin fina-finan Birtaniya Alan Rickman ya rasu sakamakon wannan cuta a shekarar 2016, watanni biyar bayan an gano yana fama da ita.

Alamomin cutar dajin ƙoda na iya haɗawa da:

- Sauyawar launin ido daga fari zuwa ruwan ƙwai.

- Ƙaiƙayin fata.

- Fitsari mai wani launi.

- Bahaya mai launi fiye ba yadda aka saba.

- Rage nauyi ba tare da bayyanannen dalili ba.

- Tsananin gajiya.

- Zazzabi.