Yadda mutum-mutumi ke aiki a gidan abinci da 'yarjarida mai sukar gwamnati

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Zaɓɓaɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

Miss universe Kenya

Ƴan takarar sarauniyar kyau ta Kenya a lokacin da suke shiryawa a bayan fage a ranar Juma'a.

Miss Kenyan audience

Ƴan kallo a wajen taron fitar da sarauniyar kyau ta Kenya ke kirari ga gwanayensu.

Fashion Show in UK

A lokacin da mai tallar kayan ƙawa ke tallata kayan ɗan Najeriya Adebayo Oke-lawal a wajen bikin nuna kayan ƙawa a Birtaniya.

Malian basketballer Maimouna Haidara

Yadda shahararriyar ƴar wasan kwandon Mali, Maimouna Haidara ta ƙawata gashinta a wajen wasan da suka buga da Venezuela a Mexico.

Forty-two-year-old retired circus elephant

Giwa mai shekara 42 da aka mayar a wani gidan kayan tarihi na lardin Limpopo da ke Afirka ta Kudu a ranar Laraba.

A customer thanks a robot

Wata Kwastoma kenan a lokacin da take godiya ga butun-butumin da ya kai mata abinci a gidan abincin butun-butumi a Nairobi a ranar Alhamis.

Dricus Du Plessis na Afirka ta Kudu tare da Israel Adesanya na Najeriya

Dricus Du Plessis na Afirka ta Kudu tare da Israel Adesanya na Najeriya, rungume da juna bayan kammala fafatawa a wasan dambe na ajin matsakaita ranar Lahadi, bayan Dricus ya lashe fafatawar.

Ƴan ƙasar Gabon kenan a lokacin d asuke ɗaga tutar ƙasar

Ƴan ƙasar Gabon kenan a lokacin d asuke ɗaga tutar ƙasar a yayin faratin tunawa da samun ƴancin kai a babban birnin ƙasar Libreville a ranar Asabar.

Yar jarida kuma mai sukar gwamnatin Burundi, Floriane Irangabiye

Yar jarida kuma mai sukar gwamnatin Burundi, Floriane Irangabiye a lokacin da take godewa tawagar lauyoyin da suka roƙi shugaban ƙasar ya sako ta daga gidan yari, bayan sakinta a ranar Juma'a.

Wasu mutane

Wasu kenan da suke amfani da kwale-kwale domin zagayawa a babban birnin ƙasar Chadi, N'Djamena inda aka samu ambaliyar da ta yi sanadiyar rushewar gidaje sama da 16,000.

Wata uwa a gabashin Kongo, Justine Munguiko

Wata uwa a gabashin Kongo, Justine Munguiko riƙe da yarinyarta da aka yi wa maganin cutar ƙyandar biri.

mawaƙiya

An karrama tauraruwar fina-finai kuma mawaƙiyar Afirka ta Kudu a Johannesburg, Abigail Kubeka a matsayin wadda ta cika shekara 67 cikin msana'antar.

Mawaƙan zamani masu salon rap Wadagliz a Kenya

Mawaƙan zamani masu salon rap Wadagliz da aka yi amfani da sautinsu a yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Kenya.