Tinubu ya yaba da ceto 'yan bautar ƙasa da aka sace a Kogi

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jinjinawa jami'an tsaro bayan ceto mutum 21 da aka sace a jihar Kogi, ciki har da mambobin bautar ƙasa 15.
Shugaban ya ce haɗin gwiwar sojoji, 'yansanda, jami'an DSS da kuma masu sa-kai ne suka gudanar da aikin ceton, inda aka kuɓutar da waɗanda aka sacen daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Ofu.
Tinubu ya ce jami'an tsaro na ci gaba da farautar masu garkuwar, yana mai jaddada cewa duk wanda ke da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa doka.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.



















