Yadda aka ɗaura auren wasu Falasɗinawa a sansanin ƴan gudun hijira

Amarya da ango
Bayanan hoto, Nan wasu Falasɗinawa ne Mahmud Akhiziq da Shaima' Qazeat ke murnar aurensu da aka ɗaura
An wallafa
Gaza
Bayanan hoto, An ɗaura auren ne a ranar Juma'a 16 ga watan Febrairu, a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke Deir Al-Balah a tsakiyar Zirin Gaza.
Gaza
Bayanan hoto, An kuma raba abinci inda mutane da dama suka halarci bikin domin taya ango da amaryarsa murna.
Aure
Bayanan hoto, An ɗaura auren ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa
Aure
Bayanan hoto, Ba kasafai ake ganin irin waɗannan bukukuwa na ɗaura aure ba yayin da ake gwabza yaƙi