Gwamnonin APC
sun gana da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba, ƙarƙashin
jagorancin shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
Gwamnonin sun
ce sun tattauna da Bahari kan batutuwa da dama musamman game da babban taron
Jam’iyyar na ranar Asabar inda za a zaɓi shugabannin jam’iyyar.
Ganawar na zuwa a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai
mulkin Najeriya ke ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin
jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shugabanninta.
Tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai
daban-daban – inda misali aka kebe wa yankin arewa ta tsakiya kujerar shugaban
jam’iyya na kasa.
Shugaban Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a
wajen zaben shugabanni, a maimakon haka yake neman a sasanta tsakanin ‘yan
takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba
Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.
Sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su
yarda da wannan tsari ba, kamar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari,
wanda ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa
ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganinsa bai wa wani yanki ko wani
mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.
Gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya yi wa Ishaq
Khalid karin bayani kan ganawarsu da shugaba Buhari.