Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 22/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Shugaban Brazil ya zargi Majalisar Ɗinkin Duniya da kasa shawo kan rikici a duniya

    .
    Bayanan hoto, .

    A jawabin da ya gabatar a babban taron MDD Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na Brazul, ya yi allawadai da abin da ya kira rashin katabus din kwamitin tsaro na MDD. Ya ce kwamitin tsaron ya gaza gudanar da aikin shi yadda ya dace dan haka kusan kowa a tsorace ya ke. A jawabi na daban ya gargadi yadda ake tsoma baki a zabukan kasashe. Wannan na zuwa ne makonni biyu gabannin babban zaben shugaban kasa a Brazil da zai kara tsayawa takara. Tun da fari babban magatakardar MDD, Antonio Guterres, ya shaidawa zauren taron, cewa ana ƙara samun giɓi kan abubuwan da ba su dace ba a duniya. Ya kira a hada ƙarfi da ƙarfe domin magance sauyin yanayi da rage gibin da ke tsakanin jama'a.

  2. Sarki Abdullah na Jordan ya gargaɗi Isra'ila kan shirinta na mamaya

    .

    Sarki Abdullah na Jordan ya yi amfani da jawabin babban taron MDD don yin gargaɗi kan abin da ya kira yunwar mamayar da Isra'ila ke yi na neman zama babbar barazana ga yankin Gabas ta tsakiya. Sarki Abdallah ya ce ƙasashen duniya sun gaza musamman kan abin da ake ganin ƙoƙarin mamayar wani ɓangare na ƙasar Syria da Isra'ila ke yi. Sarki Abdallah ya gadarar da gwamnatin nan ke nunawa ta kai matakin ha'u'la'i, an kai matakin da ba ta shakkar duk abin da ka je ya zo. Dan haka kar wani a zauren na MDD ya yi tunanin aniyarsu za ta tsaya ne akan mallake ƙasar Falasdinu.

  3. An yanke wa wasu mutane hukuncin ɗaurin shekara 250 a Sri Lanka

    .
    Bayanan hoto, .

    Kotu a Sri Lanka ta yankewa mutanen nan 15 da aka samu da kai mummunar hari ranar Ista a shekarar 2029, hukuncin daurin shekaru 250 a gidan kaso.Harin da 'yan ƙunar bakin wake suka kai otal uku da Majami'u 3 da ke bikin ranar Ista a Colombo, ya yi ajalin 270, cikinsu akwai 'yan kasashen waje 45.Wakilin BBC ya ce cikin laifukan da aka same su da aikatawa akwai kisan kai da kitsa kai harin ta'addanci, da mallakar ababen fashewa da bindigogi.A watan da ya gabata an yankewa wasu manyan jami'an tsaro hukuncin kisa kan gaza dakile harin.Kotun ta kuma ba da umarnin kwace dukkan kadarori da abin da wadanda aka yankewa hukuncin suka mallaka.

  4. Harin jirgi maras matuƙi ya kashe mutum 14 a Tigris

    .
    Bayanan hoto, .

    Aƙalla mutum goma sha huɗu sun rasa rayukansu yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon wani harin jirgin sama marar matuƙi (drone) da rundunar sojin Habasha ta kai a Kudancin yankin Tigray, kamar yadda gidan talabijin na Dimtse-Woyane da ke yankin, ya ruwaito.

    Magajin garin Alamata, Moges Shiferaw, wanda kafar ta ambato, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Talata, 22 ga Satumba, 2026. Ya bayyana cewa an kai hare-hare guda 20 ta jiragen drone tare da hari guda ɗaya da jirgin yaƙin soja a garin da kewayensa.

    Ya ce hare-haren sun afkawa fararen hula da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwannin da ke kusa, sannan kuma sun lalata gine-ginen makarantu biyu.

    Kafafen yaɗa labarai na yankin sun kuma ba da rahoton wani harin drone daban a gundumar Tahitay Adiabo da ke Arewa maso Yammacin Tigray, sai dai ba a tabbatar da samun asarar rayuka ko jikkata a wannan harin ba.

    Sashen BBC na harshen Tigrigna na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da faruwar waɗannan hare-hare tare da hukumomin yankin da kuma majiyoyi na cikin gida.

    Wadannan hare-hare na baya-bayan nan sun zo ne a daidai lokacin da ake ƙara fargabar yiwuwar sake barkewar cikakken yaƙi tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da ƙungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF).

    A cikin makonnin baya-bayan nan, sojojin gwamnatin tarayya sun ƙara yawan hare-haren sama da suke kaiwa a sassa daban-daban na yankin Tigray.

  5. Idan ba a cimma yarjejeniya ba zan ruguza Iran - Trump

    Donald Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ware babban ɓangare na jawabinsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) wajen magana kan Iran, kafin daga bisani ya karkata zuwa wasu batutuwan duniya da suka haɗa da yaƙe-yaƙen Gaza da Ukraine, da kuma halin da ake ciki a Venezuela da Cuba da Greenland, da sauya fasalin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma basirar ɗan'adam ta wucin gadi (AI).

    A farkon jawabinsa, Trump ya ce Amurka tana cikin cikin ƙarfi fiye da kowane lokaci, yana mai cewa tattalin arzikinta da ƙarfinta na soja da kuma fasaha sun kai wani mataki da ba a taɓa gani ba.

    Ya kuma yi magana kan ƙoƙarin gwamnatinsa na rage laifuffuka da ƙarfafa tsaron kan iyaka da kuma jawo ƙarin masu saka hannun jari zuwa Amurka.

    Trump ya bayyana Iran a matsayin "ƙasar da ta fi kowacce tallafa wa ta'addanci a duniya", tare da nanata cewa ba zai taɓa bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

    Ya ce bayan fara wani sabon zagaye na tattaunawa, Washington ta miƙa wa Tehran tayin cikakken haɗin gwiwar tattalin arziki idan za ta kawo ƙarshen shirinta na nukiliya tare da dakatar da abin da ya kira tallafa wa ta'addanci, sai dai ya ce Iran ta yi watsi da tayin.

    Daga nan Trump ya ce Iran na da zaɓi guda biyu a gabanta: ko dai ta cimma yarjejeniya da Washington tare da sake gina tattalin arzikinta, ko kuma ta fuskanci abin da ya kira "rushewar Jamhuriyar Musulunci cikin sauri".

    Ya ƙara da cewa yana ganin akwai yiwuwar ɓangarorin biyu su cimma yarjejeniya bayan zaɓen Amurka.

  6. Birtaniya za ta taimaka wa Saudiyya don daƙile harin Houthi

    ..

    Birtaniya na shirin tura wani jirgin soji don taimakawa wajen ƙarawa jiragen yaƙin Saudiyya mai a sararin samaniya a rikicin da ƙasar ke yi da ƴan Houthi masu samun goyon bayan Iran.

    Jirgin ƙirar RAF Voyager wanda zai riƙa aiki daga sansanin Birtaniya da ke Cyprus, zai soma aikin ƙarawa jiragen yaƙin mai a sararin samaniya a ƴan kwanaki masu zuwa bayan da Birtaniyar ta amince da buƙatar Saudiyya, kamar yadda ministan tsaro Luke Pollard ya bayyana.

    Ya ƙara da cewa Birtaniya ta bayar da tallafin ne kawai domin ayyukan Saudiyya na kare kai kuma zai kasance na ɗan lokaci "ƴan makonni maimakon kwanaki."

    Mayaƙan Houthi na gwabza rikici da gwamnatin Yemen wadda duniya ta amince da ita kuma take samun goyon bayan Saudiyya.

    A baya-bayan nan, mayaƙan Houthi a Yemen sun ce sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa da a Riyadh, babban birnin Saudiyya, har ma da wasu cibiyoyin makamashi da ke gaɓar Tekun Maliya.

  7. Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da shirin ƙara kuɗin lantarki

    ..

    Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin lantarki a ƙasar.

    Ministan lantarki, Joseph Tegbe ne ya bayyana haka a Abuja a wani taron manema labarai don cikarsa kwanaki 100 a matsayin minista.

    Tegbe ya ce a arshen makon nan, ya samu kiraye-kiraye da dama sakamakon rahotannin da ke cewa gwamnatin tarayya tana oarin ara kuin wuta.

    Ya bayyana cewa gwamnati ta mayar da hankali kan iganta lantarki ga an Najeriya.

    A cewar shi, gwamnati na oarin samar da hanyyin makamashi tare da gudanar da bincike kan angare lantarki a fain asar don gano matsaloli tare da magance su.

  8. Babban Bankin Najeriya ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23

    .

    Kwamitin Manufofin Kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya rage wani adadin na kuɗin ruwa daga kashi 26.5 zuwa kashi 23 cikin ɗari.

    Gwamnan Babban Banin Najeriya, Olayemi Cardoso, ne ya sanar da matakin a ranar Talata, bayan kammala taron kwamitin karo na 307 da aka gudanar a Abuja.

    Cardoso ya ce: “Kwamitin ya yanke shawarar rage adadi mai yawa na kuɗin ruwa zuwa kashi 23 cikin 100.”

    Wannan mataki ya zo ne bayan kwamitin ya bar kuɗin ruwa yadda yake a tarurrukansa biyu da suka gabata, sannan ya rage shi da maki 50 kawai a watan Fabrairun 2026.

    Matakin rage kuɗin ruwan dai ya zo ne a daidai lokacin da ake samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a jere.

    A cewar sabon rahoton Ma’aunin Farashin Kayayyaki da Hukumar Kididdiga ta Ƙasar (NBS) ta fitar, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta ragu kaɗan zuwa kashi 15.39 cikin 100 a watan Agustan 2026, daga kashi 15.43 cikin 100 da aka da shi a watan Yulin da ya gabata.

  9. Najeriya ta bayar da wa'adin mako biyu a binciki mutuwar mutum 37 a Neja

    Olubunmi Tunji-Ojo

    Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce kwamitin da aka kafa domin binciken mutuwar wasu mutane 37 da ke tsare a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Sibil Defens a Najeriya NSCDC) a Jihar Neja, zai binciki yadda aka kama su da kuma yadda aka tsare su.

    Kwamitin zai binciki ko an azabtar da mutanen ko kuma an hana su samun kulawar lafiya, da kuma ko wasu jami’an tsaro sun yi sakaci wajen kula da su.

    Haka kuma, kwamitin zai duba bayanan jinya da na gwaje-gwajen gawawwaki, da bayanan tsare mutanen. Zai kuma yi hira da waɗanda suka tsira da ’yan uwansu da shaidu da ma’aikatan lafiya.

    Kwamitin zai sake duba dokoki da ƙa’idojin da ke jagorantar ayyukan Hukumar ta NSCDC na yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, tare da tantance ko akwai wasu mutane ko hukumomi da ya kamata a ɗora wa alhakin abin da ya faru.

    Ministan ya ce kwamitin zai ba da shawarar ɗaukar matakin shari’a kan duk wanda aka samu da laifi, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka mutu. Haka kuma, zai ba da shawarwari kan matakan da za a ɗauka domin hana sake faruwar irin wannan lamari.

    Ya yi gargaɗin cewa ba za a kare wani jami’i ba, ko da kuwa yana da babban matsayi, sannan duk wani ƙoƙari na hana binciken zai fuskanci mataki mai tsauri.

    Ya ce: “Mu ’yan Najeriya, muna bin ku gaskiya, kuma za mu faɗa muku gaskiyar.”

    Kwamitin na da makonni biyu da zai gabatar da rahotonsa da sakamakon bincikensa.

    An kama mutanen ne a lokacin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar kan mutanen da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jihar Neja.

  10. Iran ta ce ta ƙarfafa sabon shirinta na yaƙi

    Makaman Iran

    Mataimakin kwamandan rundunar rundunar juyin juya halin Iran, Mustafa Ezadi, ya ce dakarun ƙasar na ci gaba da ƙarfafa sojinsu da inganta makaman yaƙi.

    Sashen Fasha na BBC ya ruwaito wasu kafafen yaɗa labaran Iran nma ambato Ezadi na maraba da masu goyon bayan gwamnati da ke ci gaba da fitowa kan tituna da dare.

    “Idan ƴan ƙasa suka ci gaba da kasancewa a kan tituna, da yawa daga cikin makircin abokan gaba za su ci tura.”

    Mataimakin kwamandan ya kuma ce Iran na ci gaba da bunƙasa ƙarfinta a fannonin makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da makamai masu linzami da tsaron intanet ɗinta (cyber) da kuma kariyar sararin samaniya.

  11. An ƙaddamar da kwamitin binciken mutuwar masu haƙar ma'adanai 37

    ..

    Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da kwamitin mutum 10 don gudanar da bincike game a kisan matasa 37 a hannun hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Neja bisa zarginsu da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

    Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya ƙaddamar da kwamitin yau a Abuja bayan sakamakon umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da a gudanar a bincike kan lamarin.

    Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Jonathan Kure yayin da wani tsohon babban daraktan makarantar horas da aikin lauya, Farfesa Isa Hayatu, zai kasance a matsayin sakatare.

    Sauran mambobin sune AIG Hosea Hassan Karma mai ritaya; Farfesa Olayinka Buhari, tsohon babban likitan asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin, wakili aga masarautar Minna sai kuma wani wakilin daga gwamnatin Neja.

    Kwamitin ya kuma haɗa da Alhaji Liman Sulaiman, Sakataren ƙungiyar masu haƙar ma'adanai ta ƙasa sai lauya kuma ɗan fafutuka Deji Adeyanju.

    Masu haƙar ma'adanan su 37 sun rasu ne ranar Alhamis a hannun hukumar NSCDC inda ake tsare da su.

    Zuwa yanzu ba a tantance abin da ya janyo mutuwar tasu ba, inda hukumomi suka nemi a gudanar da bincike a kai.

  12. Mutum 11 sun ji rauni bayan buɗe wuta a Turkiyya

    ..

    Aƙalla mutum 11 sun ji rauni sakamakon buɗe wuta da wani mahari ya yi a wajen wata makarantar sakandare da ke Turkiyya.

    Daga bisani kuma ɗan bindigar ya tsere. Lamarin ai ya faru ne a makarantar da ke Lardin Manisa a yammacin ƙasar.

    Tuni dai aka kama ɗan bindigar, kamar yadda ofishin gwamnan yankin ya sanar.

    Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa biyu daga cikin mutanen da aka kai asibiti suna cikin mawuyacin hali.

    Bidiyon da aka wallafa a intanet ya nuna wani mutum a kusa da makarantar ɗauke da bindiga, sai kuma bidiyon ya nuna shi yana tserewa amma da makamin a hannunsa.

    Zuwa yanzu ba a san dalilinsa na kai harin ba.

    Bayanai daga kakafen yaɗa labaran Turkiyya na cewa maharin ɗalibi ne ɗan shekara 15 sai dai hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ilimi ta Turkiyya ta ce lamarin ya jefa ƙasar, musamman ɓangaren ilimi cikin yanayi na alhini.

    Ma'aikatar ta kuma ce ta tura jami'ai zuwa Manisa domin gudanar da bincike.

    ...
  13. Iran ta yi tayin buɗe Mashigar Hormuz

    ..

    Kamfanin dillancin labarai na Japan, Kyodo ya ruwaito wani babban jami’i a Iran da ba a bayyana sunansa ba yana cewa ƙasar tana tayin buɗe Mashigar Hormuz nan da mako ɗaya don a sassauta mata takunkumin da aka ƙaƙaba mata.

    Matakin wani ɓangare ne na yunƙurin da Tehran ke yi na komawa kan teburin tattaunawa da Amurka don kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, kamar yadda dillancin labaran ya bayyana.

    Kyodo ya ruwaito jami’in na cewa Majalisar tsaron ƙasar da Jagoran addini Mojtaba Khamenei sun amince da shawarar.

    A cewar rahoton, tuni masu shiga Tsakani suka gabatar da shawarar ga Amurka.

    Jami’in ya ce Iran na son ganin alamu da za su tabbatar da cewa Amurka a shirye take ta koma teburin sulhu, a dakatar da ayyukan soji a Mashigar Hormuz tare kuma da ƙarshen ci gaba da rufe tashoshin jiragen Ruwan Iran.

  14. Mutum biyar sun mutu sakamakon ƙaƙƙarfar guguwa a Japan

    ...

    Aƙalla mutum biyar sun mutu, wasu da dama kuma sun ɓace sakamakon wata ƙaƙƙarfar guguwa da ta afkawa gaɓar tekun gabashin Japan.

    Guguwar ta kuma haddasa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka jima ba a samu irinsa ba a yankunan da ke kewaye da babban birnin ƙasar, Tokyo, tare da jefa dubban gidaje cikin duhu bayan da wutar lantarki ta ɗauke.

    Jami'an hukumar kula da yanayi a ƙasar sun buƙaci jama'a su ci gaba da kasancewa cikin shiri da taka-tsantsan.

    Tun kafin guguwar ta fice daga ƙasar, ta tilasta rufe ɗaya daga cikin manyan bukukuwan baje kolin wasannin bidiyo mafi girma a duniya da ake gudanarwa a Tokyo.

    Haka kuma, an soke tashi da saukar ɗaruruwan jiragen sama, yayin da aka dakatar da wasu ayyukan sufurin jiragen ƙasa saboda mummunan yanayin da guguwar ta haifar.

  15. Ya kamata Isra'ila ta sassauta matakan shigar da kayan agaji Gaza - MDD

    Wani tanti na Falasɗinawan da yaƙi ya ɗaiɗaita
    Bayanan hoto, Wani tanti na Falasɗinawan da yaƙi ya ɗaiɗaita

    Shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa, ya yi kira ga Isra’ila da ta sassauta matakan da take ɗauka wajen ba da damar shigar da kayayyaki da kayan aiki zuwa Gaza.

    Christian Saunders ya shaida wa BBC cewa kusan dukkan mutanen da ke yankin na zaune ne a cikin tantuna, ko ƙarƙashin buhun roba ko kuma a cikin gine-ginen da aka ruguza wani ɓangare.

    Shugaban hukumar ya ce matuƙar ba a samu ci gaba wajen sake gina yankin ba, to akwai yiwuwar mawuyacin yanayi da rashin tsafta su zame wa mutanen yankin jiki.

    Mista Saunders ya bayyana cewa ana matuƙar buƙatar kayayyaki irin su sandunan kafa tanti da man injina, amma Isra’ila ta hana shigar da su.

    A baya dai Isra’ila ta ce takunkumin da take sanya wa wasu kayayyaki ko kuma binciken da take yi a kan su na nufin hana ƙungiyar Hamas amfani da su.

  16. White House ta buɗe gidan talabijin na Trump TV

    Trump

    Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ƙaddamar da tashar talbijin ta yanar gizo mai suna Trump TV.

    Matakin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan manyan gidajen talabijin na Amurka sun dakatar da rahotannin da suke ɗauka daga fadar ta White House, domin nuna rashin amincewarsu da matakin da Shugaba Trump ya ɗauka na haramta wa tashoshin CNN, MS Now da kuma Politico shiga fadar.

    Trump ya zargi kafafen yaɗa labaran da wallafa labaran ƙarya.

    Shafin intanet na White House ya bayyana Trump TV a matsayin tashar da ta fi dacewa domin samun muhimman bayanai.

    A cikin wata sanarwa da gwamnatin Trump ta fitar, ta ce samun damar shiga White House alfarma ce, ba wai haƙƙi ba ne.

    Sanarwar ta kuma ce babu wani shugaban ƙasa da doka ta tilasta masa karɓar abin da ta bayyana a matsayin wata kafar yaɗa labarai mai adawa da gwamnatinsa.

  17. Shugaba Tinubu ya tsawaita hutunsa

    Shugaba Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tsawaita hutunsa da ƴan kwanaki kuma zai koma ƙasar a ƙarshen mako.

    Shugaba Tinubu dai ya bar Najeriya ne a ranar 30 ga Agusta inda ya tafi birnin London domin fara hutunsa.

    Bayan shafe mako ɗaya a London kuma, sai Tinubu ya je birnin Paris a Faransa inda ya gana da takwaransa Emmanuel Macron da ɗan kasuwa Mr Vincent Bollore.

    Shugaba Tinubu dai ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki daga inda yake a yayin hutun nasa.

    A cewar sanarwar da Fadar Shugaban Najeriya ta fitar, tun bayan soma hutun nasa, Shugaba Tinubu ya ci gaba da tuntuɓar gida inda kuma yake tafiyar da harkokin ƙasar ciki har da bayar da umarnin kafa kwamitin bincike kan mutuwar matasa 37 da ake zargin masu haƙar ma'adanai ne ba bisa ƙa'ida ba a Minna, babban birnin jihar Neja.

    Sannan sanarwar ta ƙara da cewa a yayin hutun, Tinubu ya wakilta mataimakinsa Kashim Shettima don halartar wasu taruka a ƙasar.

    Sanarwar ta ce duk da cewa Shettima ya tafi Amurka don halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka, Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume,wanda yake wakiltar shugaban a taruka, zai ci gaba da yin hakan.

  18. G7 ta buƙaci Houthi ta dakatar da hare-hare kan Yemen da Saudiyya

    Mayaƙa Houthi

    Kungiyar ƙasashen nan bakwai da ke da ƙarfin tattalin arziki a duniya wato G7, ta yi kira ga mayaƙan Houthi da ke samun goyon bayan Iran da su gaggauta dakatar da hare-haren da suke kai wa Yemen da kuma Saudiyya.

    Ministocin harkokin wajen Amurka da Birtaniya tare da na sauran ƙasashen biyar, sun kuma buƙaci a kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa na farar hula a Tekun Bahar Maliya, waɗanda suke haifar da cikas ga harkokin kasuwanci a duniya.

    Sanarwar haɗin gwiwar ta zo ne bayan da Birtaniya ta ce za ta bai wa Saudiyya taimakon soji a yaƙin da take yi da mayaƙan Houthi.

    Wakilin BBC ya ce jami’an gwamnati sun ce wannan tayin na da iyakacin lokaci, kuma a matakin farko ana sa ran zai ci gaba ne na tsawon wasu makwanni.

    A kwanakin baya bayan nan, mayaƙan Houthi sun kai hare-hare kan babban birnin Saudiyya, Riyadh, da kuma wasu wuraren samar da makamashi da ke gaɓar Tekun Bahar Maliya a ƙasar.

  19. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa Najeriya da ma sassan duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da kuma yin muhawara.

    Ku kasance tare da mu.