An miƙa ’yan Najeriya biyu ga Amurka kan zargin damfarar intanet da ta yi sanadin mutuwar matashi
Wasu ’yan Najeriya biyu sun isa Amurka domin fuskantar shari’a bayan an miƙa su daga Najeriya kan zargin hannu a damfarar intanet ta hanyar barazanar yaɗa hotunan tsiraici, lamarin da ake zargin yayi sanadin mutuwar wani matashi ɗan Amurka.
Hukumar EFCC ta bayyana sunayensu da Mudashiru Afeez Olawale da Adebola Festus Adekunle, tana mai cewa an miƙa su ne ga hukumomin Amurka bayan binciken da FBI ta gudanar kan zargin cin zarafin yara ta intanet.
A cewar EFCC, ana zargin mutanen biyu da yi wa yara maza masu shekaru tsakanin 13 zuwa 17 barazana da hotuna na batsa domin karɓar kuɗi.
Daraktan FBI, Kash Patel, ya ce ɗaya daga cikin waɗannan zarge-zargen ya yi sanadin mutuwar wani yaro.
Hukumar ta ƙara da cewa an kama mutanen biyu a Najeriya a shekara ta 2023.
EFCC ta ce miƙa waɗannan mutanen ga Amurka wani ɓangare ne na haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaƙi da laifukan intanet da kuma cin zarafin yara.
Sai dai har yanzu mutanen biyu ba su mayar da martani kan zarge-zargen ba, kuma ba a tabbatar da su a kotu ba.