Masu goyon bayan gwamnati sun ƙwace wani muhimmin gari daga ƴan tawayen Tigray

Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiyar ’yan tawaye mai goyon bayan gwamnatin Habasha ta ce dakarunta tare da sojojin gwamnati sun ƙwace iko da garin Alamata mai matuƙar muhimmanci a yankin Tigray.
Hotunan bidiyo da ƙungiyar ta wallafa a shafinta sun nuna dakarun suna yin fareti a kan titunan garin, yayin da suke ɗaga tutar ƙasar.
Ƙwace ikon garin Alamata, wanda ke kan wata babbar hanyar safarar kayayyaki da man fetur, na iya zama babbar nasara ga gwamnatin Addis Ababa.
Garin na kusa da iyakar kudancin Tigray da yankin Amhara.
Hakan zai bai wa sojojin gwamnati damar matsawa zuwa babban birnin yankin, Mekelle, wanda ke da tazarar kusan kilomita 120 daga garin.
Sabon tashin hankalin da ya ɓarke tsakanin sojojin gwamnati da ’yan tawayen Tigray ya haifar da fargabar sake ɓarkewar yakin basasa.
A lokacin yakin da aka gwabza tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022, an kiyasta cewa sama da mutane dubu 600 ne suka rasa rayukansu.































