Aƙalla fararen hula 10 aka kashe a hare-haren Pakistan a Afghanistan - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla fararen hula 10 ne aka kashe a hare-haren sama da aka kai a Afghanistan ranar Alhamis, inda ta tabbatar da adadin waɗanda gwamnatin Taliban ɗin ta sanar.
Ofishin taimakon Majalisar Ɗinkin Duniya a Afghanistan (UNAMA) ya ce a cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na AFP: “Aƙalla fararen hula 10, galibinsu yara aka kashe, yayin da wasu tara suka jikkata a hare-haren sama da aka kai a yau (Alhamis) a lardunan Kunar da Helmand na Afghanistan.”
Tun da farko, Pakistan ta ce ta kai hare-hare kan wasu wurare a Afghanistan.
Jami’an Pakistan sun kuma ce “akalla mutane 22” ne aka kashe a hare-haren, tare da lalata dimbin alburusai.
Taliban ta musanta ikirarin Pakistan na cewa tana bai wa mayakan da ke kai hare-haren ƙetare iyaka mafaka.
Najeriya ta samu ƙarin kujerun aikin Hajjin 2027
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta ce Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027 da 10,000 lamarin da ya kai adadin kujerun da ƙasar za ta samu zuwa 60,000.
NAHCON ta ce ƙarin kujerun sun haɗa da 7,500 da za a bai wa hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, da kuma 2,500 da za a raba wa kamfanonin shirya aikin Hajji guda bakwai da ke kan gaba.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya yaba wa gwamnatin Najeriya da gwamnatin Saudiyya kan ƙarin kujerun.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta raba kujerun cikin gaskiya da bin ƙa'idojin Najeriya da Saudiyya, tare da tabbatar da walwala da jin daɗin mahajjatan Najeriya.
NAHCON ta ce za ta ci gaba da aiki da hukumomin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin tsari.
Sojoji uku da mahara 16 sun mutu bayan gumurzu a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
An kashe sojojin Najeriya uku yayin da dakarun suka fatattaki hare-hare kan sansanonin sojoji biyu tare da kashe mahara 16 a wasu samame daban-daban tsakanin ranar 30 ga Satumba zuwa 1 ga Oktoba a jihar Adamawa, da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda shafin yanar gizon Channels TV mai zaman kansa ya ruwaito a ranar 1 ga Oktoba.
Mai magana da yawun rundunar sojojin da ke gudanar da ayyuka a arewa maso gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce mayaƙan sun ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan sansanonin sojoji a yankunan ƙananan hukumomin Garkida da Hong, inda suka kashe sojoji uku kafin dakarun suka mayar da martani tare da fatattakar su.
Goni ya ce: “A lokaci guda, dakarun sun nuna ƙwarewar kare kai a lokacin da maharan suka ƙaddamar da hare-hare masu haɗin gwiwa kan wuraren da sojoji suke a Bataliya ta 226 da ke Garkida da Bataliya ta 232 da ke Garaha a ƙaramar hukumar Hong.”
Ya ƙara da cewa: “jaruman sojoji uku sun rasa rayukansu a yayin gumurzu, yayin da aka yi gaggawar kwashe sojojin da suka samu raunuka, kuma a halin yanzu suna cikin kwanciyar hankali yayin da suke karɓar magani.”
Har yanzu, Islamic State West Africa Province (ISWAP) ba ta yi ikirarin kai wani hari a Adamawa ba, inda mayaƙan ke yawan kai hari kan ƙauyukan da ba su da kariya, musamman waɗanda galibinsu Kiristoci ne.
A ƙaramar hukumar Gombi, Goni ya ce dakarun sun yi kwanton ɓauna tare da kashe mayaƙa 16 da suka taru tare da babura 15 a ƙarƙashin bishiyoyi a yankin Boima.
Dakarun sun ƙwato bindigogin AK-47 guda uku, bindigogi manya biyu, bindigar baushe ɗaya, da sunduƙan alburusan AK-47 shida da sauran su.
Sojoji uku da mahara 16 sun mutu bayan gumurzu a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
An kashe sojojin Najeriya uku yayin da dakarun suka fatattaki hare-hare kan sansanonin sojoji biyu tare da kashe mahara 16 a wasu samame daban-daban tsakanin ranar 30 ga Satumba zuwa 1 ga Oktoba a jihar Adamawa, da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda shafin yanar gizon Channels TV mai zaman kansa ya ruwaito a ranar 1 ga Oktoba.
Mai magana da yawun rundunar sojojin da ke gudanar da ayyuka a arewa maso gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce mayaƙan sun ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan sansanonin sojoji a yankunan ƙananan hukumomin Garkida da Hong, inda suka kashe sojoji uku kafin dakarun suka mayar da martani tare da fatattakar su.
Goni ya ce: “A lokaci guda, dakarun sun nuna ƙwarewar kare kai a lokacin da maharan suka ƙaddamar da hare-hare masu haɗin gwiwa kan wuraren da sojoji suke a Bataliya ta 226 da ke Garkida da Bataliya ta 232 da ke Garaha a ƙaramar hukumar Hong.”
Ya ƙara da cewa: “jaruman sojoji uku sun rasa rayukansu a yayin gumurzu, yayin da aka yi gaggawar kwashe sojojin da suka samu raunuka, kuma a halin yanzu suna cikin kwanciyar hankali yayin da suke karɓar magani.”
Har yanzu, Islamic State West Africa Province (ISWAP) ba ta yi ikirarin kai wani hari a Adamawa ba, inda mayaƙan ke yawan kai hari kan ƙauyukan da ba su da kariya, musamman waɗanda galibinsu Kiristoci ne.
A ƙaramar hukumar Gombi, Goni ya ce dakarun sun yi kwanton ɓauna tare da kashe mayaƙa 16 da suka taru tare da babura 15 a ƙarƙashin bishiyoyi a yankin Boima.
Dakarun sun ƙwato bindigogin AK-47 guda uku, bindigogi manya biyu, bindigar baushe ɗaya, da sunduƙan alburusan AK-47 shida da sauran su.
Ambaliyar ta kashe masu haƙar ma’adinai 9 A Najeriya
Masu aikin haƙar ma’adinai tara sun mutu bayan ambaliyar ruwa mai ƙarfi ta nutsar da wani ramin haƙar ma’adinai a jihar Bauchi, da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda shafin yanar gizon Channel TV mai zaman kansa ya ruwaito a ranar 1 ga Oktoba.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Nafiu Habib, ya ce waɗanda suka mutu duk ma’aikatan kwangila ne, kuma suna aiki a wani wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Nahuta, a ƙaramar hukumar Alƙaleri, lokacin da ruwa ya mamaye ramin a ranar 27 ga Satumba.
Ƙungiyoyin ceto sun yi nasarar fitar da wasu daga cikin masu aikin haƙar ma’adinan zuwa wuri mai tsaro.
Habib ya ce: “Jami’in ƴansanda mai kula da sashen na Alƙaleri ya jagoranci tawagar jami’an bincike zuwa wurin, inda aka ga janareto uku suna fitar da ruwa daga ramin domin ba da damar ceto sauran waɗanda abin ya shafa.”
Habib ya ce an miƙa gawarwakin ga ƴan uwa bayan an gudanar da binciken lafiya. Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Abu huɗu da suka sauƙaƙa rayuwar ƴan Najeriya bayan ƴancin kai
Asalin hoton, Getty Images
A ranar 1 ga Oktoba na shekarar 1960 ce Najeriya ta samu ƴancin kai daga hannun turawan Birtaniya bayan kwashe shekaru ƙasar da ƴan ƙasar suna ƙarƙashin mulkin mallaka.
A duk ranar ta 1 ga watan Oktoba, ana guganar da bukukuwa a faɗin ƙasar domin tunawa da ranar.
A lokuta da dama, a kan tattaunawa abubuwa da dama da suka shafi cigaban ƙasa ko ma akasin, duk da cewa ana yawan mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi komawa baya da ƴan ƙasar suke ganin tana fuskanta.
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi kira da a ƙara samun haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi domin magance matsalar ƴan bindiga da sauran nau’o’in laifuka da ke addabar wasu sassan Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a saƙonsa ga al’ummar jihar yayin da Najeriya ke bikin cika shekara 66 da samun ƴancin kai, inda ya yaba da tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bai wa jihar wajen yaƙi da rashin tsaro.
Gwamna Aliyu ya ce akwai kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Sokoto da Gwamnatin Tarayya wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen ganin an kawo ƙarshen rashin tsaro, tare da jaddada cewa tallafin da ake samu daga Gwamnatin Tarayya ya kamata ya ci gaba.
Ya ce gwamnatin jihar ta samar da kayan aiki da dama domin tallafa wa hukumomin tsaro, ciki har da motocin sintiri sama da 200, motocin sulke 100, babura 200, kayan aikin tsaro 3,200, rigunan kariya daga harsasai 2,000 da na’urorin hangen nesa da daddare guda 200. Haka kuma, ya ce an samar da na’urorin hangen zafin jiki 100 tare da taimakawa wajen ƙarfafa ayyukan tsaro da kafa rundunar Sokoto State Community Guard Corps.
Gwamnan ya ƙara da cewa an sayi motocin Hilux 40 da babura 700 domin Community Guard Corps, sannan gwamnatin jihar ta taimaka wajen kafa sansanin soji a Illela da sansanin ‘yan sandan Mobile a Tara, Sabon Birni. Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga, tare da neman haɗin kan jama’a wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
An yi jana'izar Falasɗinawa 100 da hare-haren Isra'ila suka kashe a Gaza a 2023
Asalin hoton, Reuters
A Gaza, an gudanar da jana’izar Falasɗinawa 100 da hare-haren Isra’ila suka kashe a watan Oktoban 2023 a ƙabari ɗaya.
Sun rasa rayukansu a makonnin farko na yaƙin, bayan wani hari da Hamas ta jagoranta kan Isra’ila.
An ciro gawarwakin daga ɓaraguzan wani rukunin gidaje na mazauna a tsakiyar birnin Gaza. Aikin nema da kwashe gawarwakin ya ɗauki fiye da mako biyu.
An lulluɓe kowane akwatin gawa da tutar Falasɗinawa, sannan aka jera su a cikin baraguzan gine-ginen da aka kashe mutanen a cikinsu.
A cikin ‘yan watannin nan, an gudanar da jana’izar gama-gari da dama a Gaza, yayin da tsagaita wutar yaƙi ya ba da damar ci gaba da nema da kuma kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu.
Matar da aka yi wa allurar kisa sau biyu amma ba ta mutu ba
An garzaya da wata fursuna da ke jiran hukuncin kisa a jihar Tennessee ta Amurka, Christa Pike, zuwa asibiti bayan yunkurin zartar mata da hukuncin kisa ta hanyar allura ya ci tura, lamarin da ya haifar da sabon ce-ce-ku-ce kan yadda ake aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar.
Lauyoyinta sun yi gaggawar neman kotu ta dakatar da hukuncin a daidai lokacin da jami'ai ke ƙoƙarin aiwatar da shi, bayan da Pike ta suma amma zuciyarta ta ci gaba da bugawa.
An kai ta asibiti domin kula da lafiyarta bayan an yi mata allurai biyu na sinadarin pentobarbital, maganin da ake amfani da shi wajen aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar allura.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027, yana mai cewa har yanzu ‘yan Najeriya da dama na cikin ƙunci duk da ikirarin Shugaba Bola Tinubu cewa ƙasar ta shiga zamanin wadata.
Atiku ya bayyana hakan ne a jawabinsa na “Yanayin da ƙasa ke ciki" da ya gabatar ranar Alhamis domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Ya ce duk wani cigaban tattalin arziki ba shi da wani amfani idan iyalai ba za su iya biyan buƙatun rayuwa na yau da kullum ba.
Ya ce raguwar hauhawar farashi kaɗai ba za ta mayar wa ‘yan Najeriya ƙarfin sayen kayayyakin da suka rasa ba, musamman ganin yadda farashin muhimman kayayyaki da ayyuka ke ci gaba da tashi.
Domin nuna irin matsin tattalin arzikin da ma’aikata ke fuskanta, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kwatanta ƙarfin sayen albashin mafi ƙaranci kafin da bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da aka yi.
A cewarsa, albashin mafi ƙaranci na yanzu, wato naira 70,000, na iya sayen kusan lita 50 na man fetur ne kawai, yayin da tsohon albashin naira 30,000 zai iya sayen lita 118 a watan Afrilun 2023.
Ya kuma yi nuni da tashin farashin burodi da ƙwai, yana mai cewa tsadar kayan masarufi na yau da kullum na ci gaba da yi wa gidaje nauyi.
A wani ɓangare na shirinsa na rage farashin man fetur, Atiku ya gabatar da shawarar bayar da tallafin gwamnati ga man fetur da aka tace a Najeriya kaɗai, yayin da za a cire man da aka shigo da shi daga ƙasashen waje daga shirin.
Ɗan takarar na ADC ya kuma yi tambaya kan kuɗaɗen tallafin kai tsaye da gwamnati ta ce tana bai wa marasa galihu, inda ya nemi a bayyana yadda aka gano mutum miliyan 10 da aka ce an bai wa kowannensu naira 75,000.
“Idan har za ku iya gano mutum miliyan 10 da za ku biya kuɗi, to ya kamata ku iya yin bayanin yadda aka biya su.”
Har ila yau, ya yi kira da a wallafa bayanan lamuni da kwangilolin gwamnati, yayin da ya nuna damuwa kan yawaitar kasafin kuɗi iri ɗaya da kuma rashin biyan wasu ‘yan kwangila haƙƙoƙinsu.
Atiku ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati ta yadda ‘yan Najeriya za su iya biyan buƙatun rayuwarsu da kuma rayuwa cikin tsaro, ba wai kawai ta hanyar alkaluman tattalin arziki da gwamnati ke fitarwa ba.
Dangane da zaɓen shekarar 2027, ya yi alƙawarin mutunta ‘yancin kan hukumomin zaɓe tare da goyon bayan fitar da sakamakon zaɓe daga kowace rumfar kaɗa ƙuri’a cikin gaggawa.
Iran ta musanta cewa Amurka ta kori tawagarta daga New York
Iran ta musanta rahoton Amurka da ke cewa an nemi tawagarta ta gaggauta ficewa daga New York
Jakadancin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce tawagar ƙasar ta bar birnin New York tun ranar Litinin kamar yadda aka tsara tun da farko.
Tun da farko, shafin labarai na Axios ya ruwaito cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya buƙaci tawagar Iran da ta gaggauta barin ƙasar Amurka bayan tattaunawar da ake yi ta shiga tsaka mai wuya.
Rahoton na Axios ya ce ya samo bayanansa ne daga wani jami'in Amurka da kuma wani mutum na biyu da ke da masaniya kan lamarin.
Sai dai jakadancin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙaryata rahoton a wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X.
"Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, wadda ta kasa cimma wata nasara, ta koma yada labaran ƙarya marasa tushe kuma marasa amfani," a cewar jakadancin.
Muhimman abubuwa 10 da ke cikin jawabin Tinubu na ranar ƴancin kai
Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi ikirarin cewa ƙasar ta kai wani muhimmin mataki a tafiyar farfaɗo da tattalin arzikinta, yayin da yake jawabi ga al'umma a ranar bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai.
Tinubu ya ce yanzu an wuce matakin ɗaukar matakan gaggawa, inda ya ce matakan gaggawa na gyaran tattalin arziki sun yi tasiri, kuma an kafa tubalin farfaɗowar tattalin arziki.
Tinubun ya ce abin da gwamnatinsaza ta mayar da hankali daga gyare-gyaren tattalin arziki zuwa tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun amfana da ci gaban.
Wannan shi ne karo na huɗu da Bola Tinubu ke gabatar da jawabin ranar ƴancin kan Najeriya tun bayan da ya zama shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayun 2023.
Benjamin Netanyahu ya yaba wa matuƙin jirgin FlyDubai
Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin Isra’ila da Indiya sun jinjinawa matukin jirgin saman ɗan kasar Indiya, da ya taka muhimmiyar rawa wajen hana wani yunƙurin haddasa hatsarin jirgin saman Flydubai da ke kan hanyarsa ta zuwa Tel Aviv.
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya ce Kyaftin Smit Machchhar ya nuna matuƙar jarumta, kuma ya taimaka wajen ceto rayukan ɗaruruwan fasinjoji.
Fasinjojin Isra’ila da ke cikin jirgin sun ce duk da raunin da ya samu bayan da mataimakin matukin jirgin ya daɓa masa wuka, Kyaftin Machchhar ya samu damar buɗe ƙofar shiga wajen da matuka jirgin suke.
Hakan ya ba su damar kai ɗauki cikin wajen.
Daga nan ne jirgin ya yi saukar gaggawa a ƙasar Saudiyya.
Da yake zantawa da kafafen yaɗa labarai na Amurka, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce matukin jirgin FlyDubai ɗan ƙasar Indiya, tare da fasinjojin Isra’ila da ke cikin jirgin, sun yi nasarar hana aukuwar mummunan hatsari da ya yi kama da harin 11 gawatan Satumba (9/11)
Abubuwa biyar da suka faru a ranakun tunawa da ƴancin kan Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Daren ranar 30 ga watan Satumban 1960, wayewar garin 1 ga watan Oktoban shekarar rana ce da Najeriya ba za ta manta da ita ba a tarihi.
Duk da cewa tarihin ya samo asali ne tun daga shekaru gabanin wannan ranar, amma dai ranar da aka ayyana ƴancin kan ta musamman ce.
An ƙawata dandanlin Tafawa Balewa wanda a nan ne aka gudanar da wannan biki na bayar da ƴancin kai.
Dubban ƴan Najeriya ne suka taru a wajen bikin, kama daga ma'aikatan gwamnati, yara ƴan makaranta, ƴan kasuwa, mata da maza sannan kuma aka gudanar da raye-raye da al'adu daga ƙabilun Najeriya daban-daban.
Gimbiyar Alexandra ta Kent ce ta wakilici Sarauniya Elizabeth II a yayin bikin, kuma ta isa Legas ne tun ranar 26 da watan Satumban shekarar.
Shugaba Tinubu ya lissafa nasarorin da ya samu a ƙasa da shekaru huɗu
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya lissafo abubuwan da ya bayyana a matsayin nasarorin tattalin arzikin Najeriya tun lokacin da ya karɓi ragamar mulki shekaru uku da rabi da suka gabata.
A jawabin da ya yi na ranar cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai, shugaban ya ce ƙasar ta fara ganin alamun ingantuwa a fannin tattalin arziki.
Ya ce tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da sama da kashi huɗu cikin ɗari a shekarar 2026, tare da gudunmawar da bangaren man fetur da kuma waɗanda ba na man fetur ba suka bayar.
Haka kuma ya ce an rage satar danyen mai, yayin da hauhawar farashi ta ragu sosai daga kololuwar matsayin da ta kai a baya.
Bugu da ƙari, Tinubu ya bayyana cewa an sake gina asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasar na waje, kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare ta samu daidaito, sannan Najeriya ta samu sama da dala biliyan shida daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba a shekarar 2025, wanda ya bayyana a matsayin mafi girma da ƙasar ta taɓa samu a tarihinta.
“Wadannan ba maganganu marasa tushe ba ne,” in ji Tinubu, yana mai jaddada cewa masu sa ido na kasa da kasa, ‘yan jarida, kungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin kasa da kasa masu bayar da tallafi da lamuni sun amince cewa an samu ci gaba wajen tabbatar da daidaito da kuma karfin tattalin arzikin Najeriya wajen jurewa kalubale.
Buɗewa
Asalin hoton, Getty Images
Masu bibiyarmu barka da safiya. Da fatan mun wayi gari lafiya. Yau Alhamis 1 ga watan Oktoban 2026. Muna taya ɗaukacin al'ummar Najeriya murnar cikar ƙasar tasu shekara 66 da samun ƴancin kai. Da fatan Allah ya maimamata mana.
Kamar kullum mun dawo da shafinmu na kai tsaye da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriyar da sauran sassan duniya. Da fatan za ku kasance da mu.