Iran ta ce ta harbo jirgin Amurka mara matuƙi a mashigar Hormuz
Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin yaƙi maras matuƙi na Amurka ƙirar MQ-1 a gabashin mashigar Hormuz.
A cewar rundunar, "wannan shi ne jirgin leƙen asiri da na yaƙi maras matuƙi na huɗu mallakin sojojin Amurka da aka harbo cikin sa'o'i 24 da suka gabata."
A kwanakin baya-bayan nan, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci da kuma sojojin Iran sun sha bayyana cewa sun yi nasarar harbo jiragen marasa matuƙi na sojojin Amurka.
Sai dai har yanzu Babban Hedikwatar Sojojin Amurka ta Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ba ta tabbatar ko ta musanta waɗannan ikirari ba.