Za mu iya tafiya da Netanyahu a gwamnatinmu - Gadi Eisenkot

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Gadi Eisenkot, wanda a hukumance aka ɗora wa alhakin kafa sabuwar gwamnatin Isra’ila a yau, ya bayyana cewa yana maraba da shiga Firaminista mai ci Benjamin Netanyahu da kuma ɗaya daga cikin abokan siyasarsa masu tsattsauran ra’ayi cikin gwamnati, muddin za a kafa gwamnatin ƙarƙashin jagorancinsa.
Eisenkot ya ce: “Idan mambobin jam’iyyun Likud da Religious Zionist da gaske sun yi imanin cewa yanzu ne lokacin haɗin kai, kamar yadda shugaban ƙasa ya bayyana, ban ga dalilin da zai hana su goyon bayan kafa gwamnati ƙarƙashin jagorancina ba, bisa ƙa’idojin da na shimfiɗa.”
Ya bayyana cewa dimokuraɗiyyar Isra’ila na fuskantar ɗaya daga cikin mafi mawuyacin lokuta a tarihinta, yana mai jaddada muhimmancin samar da gwamnati mai ɗorewa.
A yau ne shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya ɗora wa Eisenkot alhakin kafa sabuwar gwamnati bayan da aka gaza samun wata jam’iyya ko ƙawance da ta samu rinjayen kujerun da ake buƙata a zaɓen majalisar dokoki. Herzog ya yi gargadin cewa Isra’ila na fuskantar yanayi mara tabbas da kuma sauye-sauyen al’amura da ba za a iya hasashensu ba, don haka tana buƙatar gwamnatin da za ta samu kwanciyar hankali fiye da kowane lokaci.
Tun da farko kuma, Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi kira ga ‘yan siyasar ƙasar da su haɗa kai wajen fuskantar abin da ya kira “barazanar nukiliyar Iran”, yana mai cewa: “Aikinmu dangane da Iran bai ƙare ba.” Iran dai ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kuma ba domin ƙera makamai ba.






















