Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 09/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin, 09/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • INEC
  • Atiku
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Mutum 16 sun mutu a wata fashewa a Turkiyya

    Masana'antar ƙarafa

    Aƙalla mutum 16 ne suka rasa rayukansu, sama da mutum goma sha biyu kuma suka jikkata sakamakon wata fashewa da ta auku a wata masana'antar sarrafa ƙarafa da ke lardin Izmir a yammacin Turkiyya.

    Gwamnan lardin ya ce fashewar ta faru ne bayan wata na'urar daga kaya ɗauke da tukunya ta kife, lamarin da ya sa wasu kayayyaki suka faɗa a inda ake narkar da ƙarafa.

    Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce an kaddamar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

    A halin yanzu, jami'an ceto da na agaji na ci gaba da gudanar da ayyukan neman waɗanda abin ya shafa da kuma ceto waɗanda ka iya kasancewa a karkashin baraguzan ginin.

  2. An ɗaure ɗan wasan barkwanci Russell Brand shekara 10 da wata shida

    Russell Brand

    An yanke wa fitaccen ɗan wasan barkwanci kuma jarumin Birtaniya, Russell Brand, hukuncin daurin shekaru goma da watanni shida a gidan yari bayan an same shi da laifin fyade da kuma laifukan cin zarafin mata ta hanyar lalata guda uku.

    Yayin da yake yanke hukuncin, alkalin kotun ya ce ɗan wasan mai shekaru 51 ya nuna "girman kai mai muni", yana tunanin cewa shahararsa za ta kare shi daga hukunci.

    Russell Brand bai nuna wata alamar damuwa ko nadama ba, yayin da aka karanta bayanan tasirin laifukan da wadanda abin ya shafa suka rubuta.

    Wata daga cikin matan ta bayyana shi a matsayin "mai farautar mata ta hanyar lalata wanda ba shi da nadama ko kaɗan.

  3. An kama ƴan Zimbabwe tara kan yunkurin zuwa Ukraine faɗa

    Ƴan Afrika

    An kama 'yan Zimbabwe tara a Afrika ta Kudu bayan zargin su da kokarin ficewa daga kasar domin shiga yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, a cewar 'yan sanda.

    Wata tawagar jami'an tsaro ne suka kama mutanen, waɗanda shekarunsu ke tsakanin 20 zuwa 26, a yankin Johannesburg da kewaye a yammacin ranar Lahadi.

    Mahukunta sun ce an kama su ne yayin da suke "shirye-shiryen shiga jiragen sama domin barin ƙasar", sai dai ba a bayyana takamaiman inda suka dosa ba.

    An tuhume su da karya dokar Afirka ta Kudu da ke hana bayar da taimakon soja ga ƙasashen waje ba tare da izinin gwamnati ba, wadda ta haramta ayyukan sojojin haya.

    Ƴa sanda sun ce an kama mutum biyar a filin jirgin sama mafi girma a Afirka ta Kudu, wato OR Tambo, sannan an kama wasu huɗu a wani otal da ke Bruma, gabashin Johannesburg.

    An gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na Interpol da sauran hukumomin tsaro.

    Daga baya, dukkan mutanen tara sun gurfana a gaban kotu, a cewar masu gabatar da kara.

    Sanarwar 'yansanda ta kuma ce shigar Interpol da sauran hukumomin tsaro na kasa da kasa cikin lamarin na nuna cewa waɗanda ake zargin sun kuma karya dokoki a ƙasashensu na asali, lamarin da ya sa aka samu haɗin kai tsakanin hukumomin Afirka ta Kudu da na waɗannan ƙasashe.

  4. Ƴansanda sun gargaɗi masu son tayar da tarzoma gabanin ziyarar Tinubu a Jigawa

    Yansanda

    Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa ta gargaɗi mutanen da ke son tayar da rikici da su guji hakan, gabani ziyarar da shugaba Bola Tinubu zai kai jihar ranar Talata don yaƙi neman zaɓe.

    Wannan ce ziyarar aiki ta farko da shugaba Tinubu zai kai jihar tun bayan hawansa mulki.

    Ana sa ran zai kaddamar da ayyuka da kuma yin kamfe gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    Kwamishinan ƴansanda a jihar, Tijjani Murtala, shi ya bayyana haka ranar Litinin a Dutse, inda ya ce an tanadi jami'an tsaro da suka kamata zuwa muhimman wurare a faɗin babban birnin jihar.

    A cewarsa, rundunar ta fara shirye-shirye kan ziyarar, da suka haɗa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don sanin matakai da za a ɗauka.

    Kwamishinan ƴansanda ya kara nanata cewa za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da ziyarar Tinubu ta gudana cikin tsanaki.

    Ya kuma buƙaci ƴan jihar da su bai wa jami'a tsaro haɗin kai da kuma kai rahoton duk abin da ba su yarda da shi ba.

  5. Akwai yiwuwar zan tattauna da shugaban China da Rasha kan batun Iran - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana tunanin zai yi wata ganawa ta ƙasashe uku da takwarorinsa na China da Rasha, wato Xi Jinping da Vladimir Putin, gabanin taron ƙungiyar Hadin Kan Tattalin Arzikin Kasashen Asiya da Tekun Pasifik (APEC) da za a yi a China mako mai zuwa.

    Shugaban na Amurka ya shaida wa manema labarai cewa za a tattauna batutuwa da dama a ganawar, ciki har da kawo ƙarshen yaƙin Iran da kuma batun kawar da makaman nukiliya.

    Tun da farko, jaridar Wall Street ta ruwaito cewa Vladimir Putin na da sha'awar gudanar da ganawar ƙasashe uku tare da Xi Jinping da Donald Trump domin tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya a Ukraine.

    A ɗaya gefe, wakili na musamman na gwamnatin China mai kula da harkokin Gabas ta Tsakiya, Zhai Jun, ya kai ziyara Tehran inda ya gana da Ali Bagheri, mataimakin sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa ta Iran.

    A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ziyarar wakilin na China wani ɓangare ne na ci gaba da kusantar tuntuɓa tsakanin Tehran da Beijing kan batutuwan da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu, tsaron yankin da kuma cigaban al'amuran duniya.

  6. Madatsar ruwa ta ɓalle sakamakon ƙaryewar wata katanga a Pakistan

    Madatsar ruwa

    Hukumomi a arewa maso yammacin Pakistan sun ce wani katanga da ake ginawa domin kare madatsar ruwa ta Tarbela ya karye, lamarin da ya janyo kwararar ruwa daga madatsar.

    An ayyana dokar ta-ɓaci a lardin Khyber Pakhtunkhwa bayan aukuwar lamarin.

    Har yanzu ba a tabbatar da abin da ya haddasa karyewar katangar ba, wadda ke cikin aikin faɗaɗa madatsar ruwa ta Tarbela.

    Sai dai hukumomi sun ce an kwashe duka ma'aikatan ginin, 'yan Pakistan da na ƙasashen waje, cikin koshin lafiya.

    Ana gudanar da aikin faɗaɗa madatsar mai darajar dala miliyan 800 domin samar da wutar lantarki daga ruwa, tare da taimakon ƙasar China.

  7. Faransa ta zargi Iran da yi mata kutse ta intanet

    Kantuna

    Faransa ta zargi Iran da yi mata kutse ta intanet wanda ya shafi manyan kantuna.

    Da yake magana a wani taron manema labariai, ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot ya ce: "Ina tabbatar muku cewa dakarun juyin juya-hali na Iran ne suka kai wannan hari."

    Ya ce harin ya yi munin gaske kuma ƙasar za ta saka takunkumai a matakain Turai kan duk masu hannu a lamarin.

    An kai harin ne a watan da ya gabata, inda firiji-firiji na adana abubuwa a manyan kantuna suka lalace da kuma ɗaukar zafi, abin da ya janyo lalacewar kayan abinci da kuɗinsa ya kai miliyoyin yuro.

    A farkon watan Nuwambar da muke ciki, dubban kantuna a faɗin ƙasashen Turai bakwai suka fuskanci matsala bayan harin intanet. Ba a dai san cewa ko hare-haren na da alaƙa da juna ba.

    Iran dai ba ta ce uffan kan zarge-zargen ba kawo yanzu.

  8. Kotu ta wanke mutumin da ake zargi da kashe matarsa a Kano

    Kotu

    Wata babbar kotun jihar Kano mai lamba 11 da ke zama a yankin Bompai, ta wanke tare da sallamar wani mutum mai suna Yusuf Nadabo Kawule, daga zargin kashe matarsa.

    Kotun, wadda Mai Shari’a Nasir Saminu ke jagoranta, ta yanke hukuncin ne bayan masu gabatar da ƙara sun kasa gabatar da gamsassun hujjoji da za su tabbatar da zargin kisan da ake yi wa wanda ake tuhuma.

    An gurfanar da Yusuf kan laifin kisan kai, amma ya musanta aikata laifin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    A yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidunsu, yayin da wanda ake tuhuma shi ma ya gabatar da hujjoji domin kare kansa.

    Lamarin ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo da ke karamar hukumar Takai a Jihar Kano.

    Ana zargin cewa ya ɗauki matarsa a kan babur domin nema mata gida a wani ƙauye, inda suka yi hatsari wanda ya yi sanadin mutuwarta.

    Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

  9. Masana taurari sun gano wata na biyu a sararin samaniya

    Taurari

    Masana ilimin taurari sun ce sun gano wani ƙarin wata na biyu a sararin samaniya.

    Da farko masana kimiyya sun yi tunanin abin wasu ɓaraguzan da suka rage a sararin samaniya ne, mai yiwuwa daga roka ko tauraron ɗan'adam.

    Amma yanzu an tabbatar cewa wata halitta ce a sararin samaniya da ta samo asali ta hanyar ɗabi'a.

    Sabon watan, wanda girmansa ya kai kusan mita guda, ya shiga kewayar Duniya a watan Afrilu, kuma ana sa ran zai ɓace daga duniyarmu a wata mai zuwa.

    Sai dai wannan ba lallai ne ya zama karo na ƙarshe da za mu gan shi ba.

    Ana hasashen zai sake kusantar Duniya a shekara ta 2058.

  10. Mutanen da doka ta haramta wa zaɓe a Najeriya

    Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓe a shekarar 2027 da ke tafe, ƴan ƙasar da dama sun fara mayar da hankali kan wanda za su zaɓa.

    To sai dai bisa dokokin ƙasar, akwai wasu jerin mutane da aka dokar ƙasar ta haramta wa zaɓen.

    Kalli bidiyon nan domin ganin jerin mutanen.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  11. China ta yi watsi da zargin amfani da wata mata don leƙen asiri a Amurka

    Ƙasar China ta yi watsi da abin da ta kira zarge-zarge marasa tushe, kan cewa ta yi amfani da wata mata wajen leƙen asiri kan babban jami'in kamfanin fasaha na Amurka, ENvidia, Jensen Huang.

    Ana zargin Mista Huang da yin wata mu'amala ta soyayya da wata mata da ake zargin tana yi wa Beijing aikin leƙen asiri.

    Kamfanin ENvidia, wanda ke daga cikin manyan masu ƙera na’urorin kwamfuta na zamani da ake amfani da su da fasahar AI, ya ce ya fara bincike kan zarge-zargen.

    Mista Huang ya amince cewa ya taɓa cin amanar matarsa, amma bai yi magana kan zargin alaƙa da leƙen asiri ba.

    Bayan bayyana zarge-zargen, farashin hannayen jarin Nvidia ya ragu a kasuwa.

  12. Tinubu zai ƙaddamar da titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Kano a watan gobe

    Layin dogo

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai ƙaddamar da fara sabon titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Kano a wata mai zuwa.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya ce shugaban Tinubu zai ƙaddamar da sabin titin a ranar 3 ga watan Disamba mai zuwa.

    Aikin layin dogo mai tsawon kilomita 203 daga Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano, wanda yana ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin, ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammaluwa, yayin da aikin layin dogo mai tsawon kilomita 400 daga Kano zuwa Katsina da Maradi ya kai kashi 70 cikin 100 na kammaluwa.

    Layin dogon Kaduna zuwa Kano, wanda ƙari ne ga layin dogon da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, zai samar da ci gaba da haɗin layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna da Zaria da Kano da tare da ƙarfafa hanyoyin sufuri tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci a Arewacin Najeriya.

    Kwanan nan wata tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Funso Adebiyi, ta duba waɗannan ayyukan layin dogo guda biyu bisa umarnin Shugaba Tinubu, inda ya bayyana gamsuwarsa da ingancin aikin ginin, musamman dangane da shimfiɗar layin dogo, ababen zubar da ruwa da kariyar ginin tudu da shimfiɗar duwatsu da kuma daidaita ƙasa.

    Binciken ya haɗa da gwajin tafiyar jirgin ƙasa daga Jaji a Jihar Kaduna zuwa Kano, wanda ya bai wa jami’ai damar tantance kayayyakin ingancin layin dogon da aka kammala haɗe da abubuwan more rayuwa da aka tanada.

  13. 'Za mu yi duk mai yiwuwa don hana Amurka kai wa Iran sabbin hare-hare'

    Erdogan

    Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce ƙasarsa ba ta son ganin sabbin hare-hare kan Iran.

    Ya ƙara da cewa ya bayyana damuwarsa ga Shugaban Amurka, Donald Trump, a wata tattaunawar waya da suka yi kwanan nan.

    “Mukan jaddada a duk lokacin da muka samu dama cewa warware matsaloli ta hanyar diflomasiyya da tattaunawa abu ne mai yiwuwa. Abin takaici, muna sake ganin wani yanayi mara kyau,” in ji Erdogan ga manema labarai yayin jirgin dawowarsa daga Azerbaijan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa: “Za mu yi duk abin da za mu iya domin hana wannan yanayi faruwa.”

  14. Da ba don ni ba da yanzu an shafe Isra'ila - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kare hare-haren sojin Amurka kan Iran a wata hira da gidan talabijin na CBS, yana mai cewa sai a nan gaba ne za a gane amfanin yaƙin.

    Trump ya ƙara da cewa idan Iran ta mallaki makaman nukiliya a lokacin da yake kan mulki, hakan zai kasance baƙin tarihi a gare shi.

    Shugaban ya kuma ce ba ya son ƙara tsanantar rikicin yaƙi da Iran.

    A cikin hirar, an kuma tambayi Trump game da kuɗaɗen da Amurka ke kashewa wajen ɗaukar nauyin ayyukan sojinta a yankin.

    Sai dai ya amsa da cewa ƙasashen da Amurka ke karewa ne ya kamata su biya duka kuɗaɗen yaƙin da Amurka ta kashe, yana mai cewa ƙasar ba za ta wanzu ba da Amurka ba ta taimaka mata ba.

    Ya ce, "In da ba don mu ba, da tuni an jima da shafe Isra'ila. Ina so in gaya muku cewa da ba don Donald Trump ba, da an gama da Isra'ila, domin fiye da shekara guda da ta gabata muka tura jiragen saman yaƙi na zamani ƙirar B-2, waɗanda suka kai hari kan dukkan cibiyoyin nukiliyar Iran uku."

  15. Tawagar matan Najeriya da suka lashe Gasar Kofin Duniya sun koma ƙasar

    ƴanwasa

    Tawagar ƴanƙwallon Najeriya da suka lashe Gasar Kofin Duniya ta mata ƴanƙasa da shekara 17 ta koma ƙasar.

    Ƴan wasan sun sauka a filin jirgin sama na Abuja, babban birnin ƙasar da asubahin ranar Litinin.

    A ranar Asabar ne tawagar ta lashe Kofin Duniyar bayan doka Japan da ci 2-1 a gasar da aka buga a ƙasar Moroko.

    Magoya baya

    Tawadar ta samu tarba daga ɗimbin magoya baya a lokacin da ƴan wasan suka sauka a filin jirgi.

    Ana sa ran ƴan wasan za su zarce kai-tsaye zuwa fadar shugaban ƙasa, inda aka shirya musu tarba ta musamman.

    Wannan ne karo na farko da Najeriya ta kafa tarihin lashe wannan gasa.

  16. Mutumin da ake zargi da kashe-kashen Krakow ya mutu

    Ƴansanda

    Ƴan sanda a Poland sun ce mutumin nan da ake zargi da harbe-harben da suka kashe mutum shida a tsakiyar Krakow, na ƙasar ya mutu a asibiti.

    Jami'ai sun ce mutumin mai shekara 24 a duniya na da tasiri daga "aƙidun matsanancin ra'ayin mazan jiya", kuma ya samu raunuka bayan ya buɗe wuta a tsakiyar Krakow, birni na biyu mafi girma a Poland, a ranar Asabar.

    Jami'an ƴan sanda ɗauke da makamai sun garzaya wajen da lamarin ya faru kuma suka yi musayar wuta da wanda ake zargin.

    Jami'ai sun ce an harbe shi cikin minti uku da fara harin, lamarin da ya hana aukuwar wani ƙarin kisan gilla.

    Ƴan sandan Krakow sun ce wanda ake zargin da harin ya mutu da sanyin safiyar ranar Litinin.

    An tabbatar da cewa mutum shida, mata huɗu da maza biyu, sun mutu a harin.

  17. Aƙalla ƴan ci-rani 21 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Senegal

    Jirgin ruwa

    Aƙalla mutum 21 ne suka mutu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da ci rani masu ƙoƙarin isa Turai ya kife a gaɓar tekun Kébémer da ke arewacin Senegal, a cewar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar.

    Ma’aikatar ta ce an gano gawawwaki 21 sannan an ceto mutum ɗaya bayan jirgin ya nutse a ranar 7 ga Nuwamba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

    Sai dai wasu kafofin yaɗa labarai sun ce adadin ya zarta hakan.

    Kamfanin Dillancin Labarai na Senegal mallakin gwamnati (SPA) ya ruwaito cewa an gano gawawwaki 35. Sai dai BBC ba ta iya tantance wannan adadi da kanta ba.

    SPA ya ce jirgin ya yi ƙoƙarin isa Tsibiran Canary na Sifaniya yayin bi ta cikin ƙasar Mauritania.

    Ana sa ran Ministan Harkokin Cikin Gida na Senegal, Mouhamadou Makhtar Cissé, zai kai ziyara wurin da lamarin ya faru a ranar Litinin domin jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma al’ummomin da lamarin ya shafa.

    Tuni shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.

  18. Tsohuwar Firaministar Bangladesh na shirin komawa ƙasar

    hh

    Tsohuwar Firaministar Bangladesh, Sheikh Hasina, ta nemi a ba ta sabon fasfo da katin shaida domin samun damar komawa ƙasarta daga gudun hijirar da take yi a Indiya.

    An cire Mis Hasina daga kan mulki tare da tserewa daga Bangladesh shekaru biyu da suka gabata bayan wata zanga-zangar juyin juya hali da ta yi sanadiyyar asarar rayuka masu yawa.

    A cikin wata wasiƙa da ta aike wa ofishin jakadancin Bangladesh da ke birnin Delhi, ta ce gwamnatin riƙon ƙwarya ta soke tsofaffin takardunta na tafiye-tafiye da shaidar zama 'yar ƙasa.

    Sai dai hukumomin Bangladesh a baya sun ce Misis Hasina ba ta buƙatar sabbin takardu, kuma suna ci gaba da neman a mayar da ita gida domin fuskantar shari'a.

  19. Sabuwar rundunar killace Iran ta ƙasa ta fara aiki - Trump

    Najeriya

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wata sabuwar runduna ta musamman da aka kafa domin killace iyakokin ƙasar Iran ta ƙasa ta fara aiki gaba ɗaya.

    An ƙirƙiri rundunar ne domin datse hanyoyin shiga Iran da sojojin Amurka ke zargin ana amfani da su wajen safarar makamai da sauran haramtattun kayayyaki.

    Tun da farko, Amurka ta riga ta ƙaƙaba wa Iran wani shamakin ruwa, wanda ta ce ya taƙaita yawan kuɗin da Tehran ke samu daga fitar da ɗanyen man fetur zuwa dala biliyan 25.

    Sai dai Iran ta ce sabon matakin ba zai yi nasara ba, kuma ba zai haifar da durƙushewar tattalin arzikin ƙasar ba.

  20. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.