Diflomasiyya na neman yin tsami tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Takaddamar diplomasiya ta ɓarke tsakanin Najeriya da Afirka Ta Kudu bayan Babban Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya zargi fadar shugaban ƙasar Afirka Ta Kudu da katse watsa jawabinsa kai tsaye yayin bikin gabatar da takardun shaidarsa ga Shugaba Cyril Ramaphosa a Pretoria.
Fani-Kayode ya bayyana a shafinsa na X cewa daga cikin jawabai da gabatarwa 15 da aka yi a wajen taron, na Najeriya ne kaɗai aka cire daga watsa shirye-shiryen kai tsaye. Ya ce hakan ya nuna rashin mutuntawa ga Najeriya da kuma wakilcinta.
Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Afirka Ta Kudu shi ma ya nuna rashin jin daɗinsa kan lamarin, yana mai cewa an yi wa jakadan da ƙasar Najeriya raini da rashin kima.
Sai dai mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar Afirka Ta Kudu, Vincent Magwenya, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa Shugaba Ramaphosa bai sa baki a lamarin ba.
Ya bayyana cewa gidan talabijin na SABC wuri ne mai cin gashin kansa, kuma shugaban ƙasa ba shi da hurumin tsoma baki cikin harkokin editoci ko shirye-shiryensu.
Magwenya ya kuma soki yadda jakadan Najeriya ya tafiyar da lamarin, yana mai cewa abin da ya kira ƙaramar matsalar aiki bai kamata ya jawo irin wannan martani ba.
Daga bisani kuma, fadar shugaban ƙasar Afirka Ta Kudu ta wallafa wani bidiyo na daban da ke ɗauke da cikakken jawabin Fani-Kayode.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin naɗin Fani-Kayode a matsayin cikakken Babban Jakadan Najeriya na farko a Afirka Ta Kudu cikin shekara huɗu alama ce ta inganta dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, bayan shekaru na saɓani sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi da suka shafi ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka.
Duk da haka, farkon aikinsa ya zo ne cikin yanayi mai cike da ce-ce-ku-ce.













