Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 05/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 05/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • INEC
  • Atiku
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Shugaban Paraguay Santiago ya yi murabus bayan badaƙala a bankunan ƙasar

    Santiago Peña

    Shugaban Paraguay, Santiago Peña, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa bayan wata badakala da ta shafi ɗaya daga cikin manyan bankunan ƙasar.

    A cikin wani bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Mista Peña ya nemi afuwar ‘yan Paraguay, yana mai cewa ba manufarsa ba ce ya ci amanar da suka ba shi.

    Mista Peña na fuskantar shari’ar tsige shi daga mukami saboda alaƙarsa da Ueno Bank, wanda ya shiga wani hali na matsalar kuɗi da ya kai ga fara shirin rushewarsa.

    Wakiliyar BBC ta ce ana zarginsa da rufa-rufa da kuma badakala da kudaden fansho.

    Lamarin ya bar kusan abokan hulɗa miliyan uku ba tare da damar amfani da asusunsu ba. Jam’iyyarsa ma ta haɗa kai da ‘yan adawa wajen goyon bayan fara shari’ar tsige shi a majalisar dattawan ƙasar.

  2. Ina da niyyar ci gaba da riƙe Hegseth a matsayin sakataren tsaro - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana da cikakkiyar niyyar ci gaba da riƙe Pete Hegseth a matsayin Sakataren Tsaro, duk da cewa yaƙin da Amurka ta yi da Iran na daga cikin manyan dalilan da ake ganin suka taimaka wajen gagarumin kayen da Jam’iyyarsa ta Republican ta sha a zaɓen tsakiyar wa’adi na ranar Talata.

    Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na ABC News, yayin da ɗan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican, Thomas Massie, ya ce zai sake gabatar da ƙudirin tsige Mista Hegseth idan Majalisar Wakilai ta koma zama.

    Mista Massie ya ce yana ganin akwai isassun ‘yan majalisar Republican da za su karya sahu domin goyon bayan ƙudirin.

    Sai dai Shugaba Trump ya amince cewa watakila zai fi sauƙi a nemo wani mutum domin jagorantar Ma’aikatar Tsaro ta Amurka (Pentagon) kafin jam’iyyar Democrat ta karɓi iko da Majalisar a watan Janairu mai zuwa.

  3. Manyan jam’iyyun Larabawa na shirin kafa gwamnati a Isra'ila

    Manyan jam’iyyun siyasa na Larabawa a Isra’ila sun ba tsohon shugaban rundunar sojin ƙasar, Gadi Eisenkot, goyon baya domin ya kafa gwamnati ta gaba.

    A halin yanzu, shugaban Isra’ila na gudanar da tattaunawa da dukkan jam’iyyun siyasar ƙasar domin tantance wanda zai samu damar ƙoƙarin kafa gwamnatin haɗaka.

    Tun da babu wani daga cikin Gadi Eisenkot ko Firaminista Benjamin Netanyahu da ya samu rinjayen kujerun majalisa a zaɓen da aka gudanar a makon da ya gabata, jam’iyyun da Larabawa ke jagoranta na da muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai kafa gwamnati.

    Ƙungiyar Joint Arab List ta ce yana da matuƙar muhimmanci a hana Mista Netanyahu da gwamnatinsa komawa mulki.

    Wata babbar jam’iyyar Larabawa, Ra’am, ita ma ta bayyana goyon bayanta ga Mista Eisenkot a jiya Laraba.

    Sai dai duk da wannan goyon baya, Mista Eisenkot ya sha nanata cewa ba ya goyon bayan kafa gwamnatin haɗaka tare da jam’iyyun Larabawa.

  4. Lokutan da Shugaba Tinubu ya nemi rancen ƙasashen waje

    Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da buƙata a hukumance zuwa Majalisar dokoki domin neman amincewa ya karɓo rance daga ƙasashen waje da ya kai dala biliyan 7.7, kwatankwacin naira triliyan 10.79 don taimakawa wajen cike giɓin kasafin kuɗin 2026 na naira triliyan 31.4.

    An karanta buƙatar a zauren Majalisar Dattawa a zaman ranar Laraba, cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Oktoba, 2026, wadda aka aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

    Bayan gabatar da wasiƙar, Majalisar Dattawa ta miƙa saƙon daga ɓangaren zartarwa ga Kwamitinta kan Basussukan Cikin Gida da na Waje domin ƙarin nazari da gabatar da rahoto.

    A cewar wasiƙar shugaban ƙasar, an ƙididdige rancen da ake neman amincewa da shi ne bisa ƙimar canjin kuɗi da aka tanada a kasafin kuɗi na ₦1,400 kan dalar Amurka guda.

    BBC ta tattara lokutan da Shugaban na Najeriya ya nemi rance daga ƙasashen waje domin aiwatar da ayyuka a ƙasar.

  5. Atiku ya yi zargin ƙoƙarin hana shi takara a 2027 saboda kasancewarsa ɗan Arewa

    Atiku

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC Atiku Abubakar, ya yi Alla-wadai da hukuncin kotun da aka yanke ranar Alhamis, wanda ke ƙoƙarin ƙwace shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark, yana mai zargin cewa mataki ne na shirin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 saboda shi ɗan Arewa ne.

    A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labarai da Sadarwa na Yaƙin Neman Zaɓen ADC, ya fitar, Atiku ya ce lokacin da aka yanke hukuncin yana da abin lura.

    Ya ce an yanke hukuncin ne kwana ɗaya kacal bayan dimbin jama'a sun fito a Sakoto domin tarbarsa da halartar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ADC.

    "Al'ummar Sakoto sun fito dubbai saboda suna son sauyi, kuma sun yi imani da alƙawarinmu na dawo da sauƙin rayuwa. Abin da muka gani a can ba komai ba ne face farkon abin da ke tafe. Al'ummar Kebbi ma za su bayyana ra'ayinsu, kuma saƙonmu zai ci gaba da isa ga 'yan Najeriya a faɗin ƙasar,'' in ji Atiku.

    "Na yi imanin cewa waɗanda ke wannan zagon kasa sun saka Nafiu-Bala Gombe, wanda shi ma ɗan Arewa ne, ya yi musu wannan aiki ta hanyar amfani da kotu domin hana ni shiga takara. Amma ba za su yi nasara ba, domin goyon bayan da nake samu bai takaita ga Arewa kaɗai ba.

    Ya kuma ce ba su wani ɗar-dar sannan za su ɗaukaka ƙara.

    A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke takarar Atiku da kuma shugabancin ɓangaren Sanata David Mark.

    Kotun ta ce kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark, wanda ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya haifar da Atiku a matsayin ɗan takarar ADC haramtaccen kwamiti ne.

  6. Aƙalla jiragen fasinja 12 a Turai sun fuskanci tangarɗa

    Jirage

    Gwamnatin Birtaniya ta bayyana jerin barazanar bama-bamai da ke shafar jiragen fasinja a faɗin Turai a matsayin barazanar da ba ta gaske ba, amma ta jaddada cewa ana ɗaukar kowane lamari da muhimmanci.

    Aƙalla jirage fasinja goma sha biyu a Turai sun fuskanci tangarɗa sakamakon barazanar cewa an dasa bama-bamai a cikinsu, lamarin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu saukar gaggawa a filayen jiragen sama.

    Zuwa yanzu dai, ba a gano wani abin fashewa ba. Wata fasinja ke nan take cewa ana tsaka da tafiya lokacin da aka yi barazanar, ba mu san abin da ke faruwa ba.

    Jami'an tsaro sun yi saurin fitar da mu daga jirgin ba tare da ɓata lokaci ba.

    'Yan sanda a Jamhuriyar Czech sun ce jirage huɗu sun sauka lafiya a filin jirgin saman Prague. Tun da farko sun samu gargaɗi cewa an dasa abin fashewa a cikin jiragen.

  7. Demokrats na shirin kafa wani sabon tarihi a siyasar Amurka

    Siyasar Amurka

    Jam'iyyar Demokrats na shirin ƙwace kujerar gwamnan jihar Alaska da ke Amurka karon farko cikin shekara 20.

    Gwamnan Democrat na ƙarshe a jihar shi ne Tony Knowles, da ya bar ofis a shekarar 2002.

    A halin yanzu, Jonathan Kreiss-Tomkins, wanda aka fi sani da JKT, na gaba da ɗan takarar Republican, Bernadette Wilson, da ƴar ƙaramar tazara a ɗaya daga cikin fafatawar da ta fi zafi a zaɓen tsakiyar wa'adi na wannan karon.

    Ya zuwa yanzu da aka kusa kammala ƙirga ƙuri'un tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce ƙuri'a 20 ba.

    Idan ya yi nasara, ɗan siyasar mai shekara 37 kuma tsohon ɗan majalisar dokokin jihar zai zama gwamna mafi ƙarancin shekaru a tarihin Alaska.

    Kreiss-Tomkins ne kaɗai ɗan takarar Democrat a cikin ƴan takara huɗu da ke fafatawa a zaɓen.

    Yaƙin neman zaɓensa ya mayar da hankali kan rage kuɗin wutar lantarki, yana mai cewa za a iya cimma hakan ta hanyar bunƙasa iskar gas da makamashi mai sabuntawa.

    Ya yi alƙawarin haɗa membobin jam’iyyar Republican da kuma ’yan siyasa masu zaman kansu a gwamnatinsa.

    A makon ƙarshe na yaƙin neman zaɓe, ya samu goyon bayan Lisa Murkowski, Sanata ta jam’iyyar Republican daga Alaska.

  8. Mun yi maraba da hukuncin kotu da ya soke takarar Atiku - Nafi'u Bala

    Nafi'u Gombe

    Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Hon Nafiu Bala Gombe ya ce ya yi maraba da hukuncin babbar kotun tarayya da ya soke shugabancin David Mark na jam'iyyar.

    A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayyar ta yanke hukuncin soke duk matakan da ɓangaren na David Mark ya ɗauka a madadin jam'iyyar.

    Matakan sun haɗa da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

    Nafi'u Gombe, wanda ya shigar da ƙarar ya ce ya yi maraba da hukuncin kotun.

    ''Dama na jima ina magana a kan gaskiya, gaskiya, to ga shi yau gaskiyar ta yi halinta'', in ji shi.

    Dama dai Nafi'u Gombe ya tsayar da ƴantakara a ɓangarensa.

    ''To yanzu za mu mayar da hankali wajen ci gaba da tallata ƴantakararmu domin tunkarar zaɓen 2027 da ke tafe'', in ji shi.

  9. Kotu ta soke takarar Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC

    Atiku Abubakar

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta rushe shugabancin ADC tsagin Sanata David Mark.

    Yayin yanke hukuncin alƙalin kotun Mai shari’a Peter Lifu ya kuma soke duk matakan da ɓangaren na David Mark ya ɗauka a madadin jam’iyyar.

    Waɗannan matakan sun haɗa da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

    Atiku, wanda hukumar zaɓen ƙasar INEC ta riga ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, daga baya ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.

    Sai dai a hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar Alhamis, kotun ta ce kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark, wanda ya shirya zaɓen fidda gwani da ya haifar da Atiku a matsayin ɗan takara ADC, a matsayin haramtaccen kwamiti ne.

    Hon Nafiu Bala Gombe ne dai ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar hanyar da David Marka ya zama shugaban riƙo na jam'iyyar.

    Kotun ta ce ƙarar, Nafiu Bala Gombe na da tushe don haka ta yanke wannan hukunci.

    Nafiu Gombe ya jaddada wa kotun cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, shi (Gombe) ne mutum na gaba da dokar jam'iyyar ta tadani ya zama shugabanta.

    Saboda haka, daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotun akwai soke duk wasu matakai da aka ɗauka a madadin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark.

  10. Dole ne mu riƙa ɗora wa Trump alhaki idan muka fara jagorantar majalisa

    Babban Sanatan Amurka, Bernie Sanders, ya ce bayan jam’iyyar Democrat ta karɓe ikon majalisar dokokin ƙasar, dole ne a “riƙa ɗaukar mataki kan” shugaban Amurka, Donald Trump.

    Da aka tambaye shi a shirin BBC Newsnight ko yanzu Democrats za su gurfanar da Trump da kuma ’yan uwansa a gaban kuliya tare da tsige shi, Sanders ya ce: “Tabbas.”

    Sanatan mai ra’ayin kawo sauyi, wanda ke da tasiri kuma mai zaman kansa ne, ya soki halin da jam’iyyar ke ciki duk da nasarar da ta samu a zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki.

  11. 'Nasarar Demokrats koma-baya ce ga Trump da Isra'ila'

    Kafar yaɗa labarai

    Wasu kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun bayyana sakamakon zaɓen tsaiyar wa'adin Amurka a matsayin “babbar koma baya” ga Donald Trump da Isra’ila, kamar yadda Sashen Fasha na BBC ya ruwaito.

    Yayin da suke tattauna nasarar Democrats a jihohin da Republican ke da ƙarfi, waɗannan kafafen yaɗa labaran sun bayar da misali ga nasarar Abdulrahman Abdul-Sayed a matsayin sanata Musulmi na farko a Amurka, da kuma matsayinsa na suka ga Isra’ila.

    A lokaci guda, wasu manazarta Isra’ila sun ɗora alhakin sanarwar da Trump ya yi kan yiwuwar kawo ƙarshen tallafin soji da Amurka ke bai wa Isra’ila a shekarar 2027 a kan Benjamin Netanyahu, tare da gargadin illolin siyasa da na kuɗi da hakan ka iya haifarwa.

    Kafafen yaɗa labarai na Isra’ila sun mayar da hankali kan sakamakon zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka, inda jam’iyyar Democrat ta karɓe ikon duka Majalisar Wakilai ta Amurka da kuma Majalisar Dattawan Amurka.

    Jaridar Haaretz mai ra’ayin sassaucin ta riƙa bayar da rahotonni zaɓukan na Amurka kai tsaye tare da ci gaba da sabunta sakamakon zaɓen.

  12. Demokrats na shirin ɗaukar matakan kawo ƙarshen yaƙin Iran

    Chuck Schumer

    Jam'iyyar hamayya ta Demokrats a Amurka, wadda ta samu gagarumar rinjaye zaɓukan tsakiyar wa'adi da aka gudanar a ƙasar ta jaddada ƙudurin kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Chuck Schumer, wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan ƙasar kafin gagagarumar nasarar da jamiyyarsa ta samu, wanda kuma a yanzu ake sa ran zai zama shugaban masu rinjaye, ya jaddada muhimmancin kawo ƙarshen yaƙin na Iran.

    ''Dole ne mu ɗauki matakan kawo ƙarshen yaƙin idan har muna son cika alƙawuran da muka ɗaukar wa Amurkawa kafin wannan zaɓe'', in ji shi.

    A jawabin da ya yi bayan jam'iyyarsa ta Republican ta sha kaye a zaɓukan, Shugaba Trump ya amince cewa yaƙin Iran ne ya haddasawa jam'iyyarsa faɗuwa zaɓen.

    Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan ƙasar, Hakeem Jeffries ya ce jam’iyyar Democrats za ta mayar da hankali wajen fafutukar samar da rayuwa mai sauƙi ga Amurkawa, da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a ayyukan hukumomin gwamnati.

    Sai dai a bayanne take cewa Jeffries da Schumer za su fuskanci ƙalubale wajan aiki tare da Shugaba Donald Trump, a dan haka sai sun nemi hanyar da za ta tabbatar cewa Mista Trump bai yi amfani da ikon shugaban ƙasa wajan ƙin amincewa da manufofinsu ba.

  13. Ilhan Omar ta gode wa magoya bayanta kan sake zaɓenta

    Ilhan Omar

    Ƴar majalisar wakilan Amurka mai wakiltar gundumar Minnesota ta biyar, Ilhan Abdullahi Omar ta gode wa ɗimbin magiya bayanta kan sake zaɓenta a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta bayan samun nasararta, ƴar majalisar ta ce ''ina godiya a gare ku al'ummar Minnisota, ba zan taɓa mantawa da karimcin da kuke nuna min ba''.

    Ilhan ƴar asalin Somaliya, kuma ƴar jam'iyyar hamayya ta Demokrats na wakiltar gundumar tun 2019.

    Ƴarmajalisar ta yi suna wajen sukar manufofin shugaban Amurka Donald Trump, wanda shi ma ya sukarta a bainar jamar.

    A baya-bayan nan ma wasu jami'an tsaro suka kai samame gidanta da ke birnin Washington da nufin gudanar da bincike.

  14. Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala Umarah a Saudiyya

    Shugaban Najeriya

    Shugabna Najeriya, Bola Tinubu ya koma ƙasar bayan kammala ziyarar Umara zuwa Saudiyya.

    Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da daddare.

    A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya ya tafi ziyarar ibadar zuwa Saudiyya.

    A lokacin ziyarar shugaban ya samu damar shiga ɗakin Ka'abar.

  15. Wasu ƴan Republican sun fara nesanta kansu da Trump

    Trump

    Jamiyyar Republicans mai mulki a Amurka, ta fara nazari kan dalilan da suka sa jam'iyyar ta sha mummunan kaye a zaɓen tsaiyar wa'adi.

    Sakamakon zaɓen ya sa jam'iyyar Demokrats mai hamayya ta ƙwace rinjayen majalisun dokokin kasar biyu.

    Faɗuwar da Repbulican ta yi a zaɓen, na ɗaya daga cikin munanan shan kayen da ta taɓa fuskanta a tarihi.

    Ƴan jam'iyyar sun fara nazari kan makomar jamiyyar bayan shugabancin Donald Trump.

    Wasu daga cikin aminansa sun fara nesanta kansu da shugaban Amurkan, musamman mataimakinsa, JD Vance.

    Mista Vance ya ɗora alhakin shan kayen kan yakin da Amurka ke yi da Iran, kodaya ke ra’ayinsa ya zo ɗaya da na Shugaba Trump wanda da kansa ya ce yaƙin Iran ne ya sa suka faɗi a zaɓen.

  16. Maraba lale

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Yau ma dai kamar jiya Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.