NAHCON da Saudiyya sun cimma yarjejeniyar inganta aikin Hajjin 2027

Asalin hoton, NAHCON
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya da Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta aikin Hajjin 2027.
Wata sanarwa da NAHCON ta fitar ranar Talata, ta ce an cimma yarjejeniyar ce a birnin Jeddah, yayin wani taro.
Shugaban NAHCON, Ambasada Isma'il Abba Yusuf, wanda ya sanya hannu a madadin gwamnatin Najeriya, ya ce yarjejeniyar ta tanadi tsarin da za a bi wajen ganin Najeriya ta yi aikin mai inganci, ciki har da ƙara ware wa ƙasar kujerun Hajji, bin dokoki da ƙa'idojin aikin Hajji na Saudiyya da kuma haɗin gwiwa wajen samar da masauki, sufuri da kula da lafiya cikin lokaci.
Sanarwar ta kuma ce ana fatan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu wajen magance ƙalubale da ake fuskanta yayin aikin Hajji.
Da yake jawabi a wajen taron, Ambasada Isma'il Abba Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudiyya da Ministan Hajji da Umrah kan ci gaba da zuba jari a ababen more rayuwa na aikin Hajji, da kuma sauye-sauyen da aka samu wajen inganta ayyukan hajji.
Ya kuma jaddada aniyar NAHCON ta ci gaba da daidaita ayyukanta da waɗannan nasarori ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi da samar da ingantaccen masauki ga maniyyatan Najeriya.
A nasa jawabin, Dr. Mashat ya bayyana cewa Saudiyya ta gamsu da yadda alhazan Najeriya suka kasance a aikin Hajjin 2026, yana mai yaba wa Najeriya kan gudunmawar da ta bayar wajen cimma wannan nasara.































