'Batun takunkuman Amurka kan Iran ne zai mamaye taron G20'
Ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashen G20 za su gana a birnin Asheville da ke jihar North Carolina ta Amurka a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba, inda ake sa ran batun takunkuman da Washington ke ƙaƙaba wa Iran zai kasance cikin muhimman batutuwan taron.
Wani jami'in Ma'aikatar Kuɗi ta Amurka ya ce Washington za ta yi amfani da taron wajen jaddada muhimmancin bin takunkuman da ta sanya wa Iran.
Haka kuma ana sa ran Sakataren Kuɗi na Amurka, Scott Besant, zai tattauna kai tsaye da takwarorinsa kan yadda ake aiwatar da shirin matsin tattalin arziki kan Tehran, tare da yin gargaɗin cewa kamfanoni da ƙasashen da ke ci gaba da hulɗa da Iran na iya fuskantar hukunci, ciki har da hana su amfani da tsarin dalar Amurka.
Amurka ta ce tawagogi daga ma’aikatun kuɗi, harkokin wajen ƙasa da tsaro na ci gaba da tattaunawa da gwamnatoci a faɗin duniya domin ƙayyade lokacin kawo ƙarshen ayyukan da ke da alaƙa da Iran.
G20 dai ya ƙunshi ƙasashe 19 tare da Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka, kuma an kafa ƙungiyar ne domin ƙarfafa zaman lafiyar tattalin arziki da harkokin kuɗi a duniya.