Iran ta koma hada makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa karƙashin kasa
Mai magana da yawun rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ya bayyana cewa an mayar da layukan kera makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa zuwa cibiyoyi da ke ƙarƙashin ƙasa domin tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da su ko da a lokutan rikici.
Brigediya Janar Hossein Mohebi ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai, inda ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa ƙarfin samar da makamai a ƙarƙashin yanayi daban-daban. Ya ce, "Mun mayar da layukan samar da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa zuwa biranen ƙarƙashin ƙasa domin samarwa ya ci gaba ba tare da tangarda ba."
Mohebi ya kuma ce maƙiyan Iran ba su taɓa samun nasarar dakatar da ƙasar daga ƙera makamai masu linzami ba, yana mai bayyana cewa tsarin samar da makaman Iran yana da sassauci kuma zai iya ci gaba da aiki duk da matsin lamba ko hare-hare.
A cewarsa, dukkan makaman da rundunar Aerospace Force ta IRGC ke amfani da su ana ƙera su ne da ilimi da ƙwarewar cikin gida. Ya ce ba su dogara da shigo da makamai daga ƙasashen waje ba, domin fasahar ƙera makaman tana hannun masana na cikin Iran.
Amurka da Isra’ila sun sha bayyana cewa daya daga cikin manyan manufofin hare-haren da suka fara tun ƙarshen watan Fabrairu shi ne lalata shirin makamai masu linzami na Iran. Shugaban Amurka Donald Trump ma ya yi iƙirarin sau da dama cewa an yi wa ƙarfin makaman Iran mummunar illa. Sai dai Iran ta ƙaryata wannan ikirari, tana mai cewa ta ƙara yawan samar da makamai, ciki har da makamai masu linzami, a cikin watannin baya-bayan nan.


























