Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 10 - 16 Agusta 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 10 - 16 Agusta 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. New Zealand ta janye goyon bayanta ga Infantino

    Ƙasar New Zealand ta kauce wa matsayar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta yankin Oceania, inda ta zama sabuwar ƙasa da ta janye goyon bayanta ga shugaban FIFA, Gianni Infantino.

    Infantino ya rasa goyon bayan manyan ƙungiyoyin yankuna uku, wato UEFA ta Turai, AFC ta Asiya da kuma Concacaf ta Arewacin Amurka, Tsakiyar Amurka da yankin Caribbean. Rashin goyon bayan ya samo asali ne daga shirin da bai cimma nasara ba na sayar da kashi 20 cikin ɗari na haƙƙoƙin kasuwanci na gasar cin kofin duniya ga masu zuba jari masu zaman kansu.

    Sai dai kuma, Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) da kuma hukumar ƙwallon ƙafa ta Kudancin Amurka, Conmebol, sun bayyana goyon bayansu ga shugaban mai shekaru 56 domin ya sake lashe wa'adi na huɗu a zaɓen da za a yi a taron FIFA (FIFA Congress) a watan Maris.

    New Zealand ta bi sahun wasu ƙasashe mambobi daban-daban, ciki har da Ingila, Wales, Norway, Jamhuriyar Ireland da Arewacin Ireland, wajen tabbatar da cewa ba za su mara wa Infantino baya a yunkurinsa na sake neman shugabancin FIFA ba.

    A cikin wata sanarwa, an ce:

    "Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta New Zealand tana kuma neman a gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan matakan da aka bi wajen ƙirƙiro da Tsarin Fifa Forward Enterprise Scheme (FFE)."

  2. Man City za ta sayar da Reijnders fan £52m ga Al-Qadsiah ta Saudi

    Dan wasan tsakiyar Manchester City, Tijjani Reijnders, na daf da komawa kungiyar Al-Qadsiah ta gasar Saudi Pro League kan kudi fam miliyan 52.

    Manchester City ta amince da kudin sayar da dan wasan na kasar Netherlands, wanda ta saya daga AC Milan a bara kan fam miliyan 46.5.

    Duk da cewa Reijnders ya fara rayuwarsa a City cikin nasara, bai samu damar taka rawar gani sosai ba a kakar da ta kasance ta karshe ga Pep Guardiola a kulob din. Ya zura kwallaye bakwai a wasanni 47 da ya buga.

    Dan wasan mai shekaru 28 ya yi atisaye ne daban da sauran 'yan wasan City ranar Alhamis, gabanin yiwuwar komawarsa kungiyar Al-Qadsiah wadda tsohon kocin Liverpool, Celtic da Leicester City, Brendan Rodgers, ke jagoranta yanzu.

    Ficewar Reijnders na nuna cewa Manchester City na shirin yin babban sauyi a tsakiyarta, yayin da har yanzu ake cikin rashin tabbas kan makomar Rodri, wanda ya kasance fitaccen dan wasa a gasar cin kofin duniya, sannan kuma kulob din na nuna sha'awar dan wasan Chelsea kuma dan kasar Argentina, Enzo Fernandez.

    Reijnders ya kasance cikin tawagar Netherlands da ta halarci gasar cin kofin duniya ta 2026, inda ya buga wasanni uku a gasar.

    Ya fara wasannin rukuni da Japan, Sweden da Tunisia, amma bai buga wasan zagaye na 32 da Morocco ba, wasan da Netherlands ta sha kashi a bugun fenariti.

  3. Arsenal na fatan fara kakar bana da gagarumar nasara

    Arsenal za ta fara sabuwar kakar wasa tana son ta nuna ƙarfi tun da wuri bayan wani yanayi na wasannin share fage da ya kasance cike da nasarori da koma baya, tare da fara kasuwar musayar 'yan wasa cikin natsuwa.

    Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jagoranta ta fara wasannin share fage da manyan nasarori a kan MK Dons da Girona, kafin daga baya ta sha kashi a hannun Real Betis da Borussia Dortmund, sannan ta kammala shirye-shiryenta da canjaras 1-1 da ƙungiyar Serie A ta Italiya, Como.

    A wajen fili kuwa, Arsenal ta samu kwanciyar hankali a lokacin bazara, kuma ta ƙara samun muhimmiyar ƙarfafawa bayan ɗaukar Bruno Guimaraes, domin ƙarfafa tsakiyar fili.

    Idan har Arsenal ta samu nasara a kan Manchester City, wadda ke fara sabon zamani bayan ficewar Pep Guardiola, hakan zai nuna cewa har yanzu ita ce ƙungiyar da sauran masu neman kambun gasar za su yi ƙoƙarin doke wa yayin da take neman kare kambunta a wannan kakar.

  4. Ta yaya za ka iya maye gurbin koci kamar Guardiola?

    Wannan ita ce tambayar da ke gaban tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca, bayan an naɗa shi domin ya gaji Pep Guardiola a matsayin kocin Manchester City.

    Ɗan ƙasar Italiya ɗin na iya lashe kofinsa na farko a wasansa na farko na hukuma a matsayin kocin City, yayin da ƙungiyarsa ke shirin fafatawa da Arsenal a filin wasa na Principality da ke Cardiff a gasar Community Shield.

    Manchester City ta samu damar shiga wannan wasa ne a matsayin wadda ta lashe Kofin FA na bara, wanda ya zama kofi na 20 da ƙungiyar ta lashe a cikin shekaru 10 ƙarƙashin jagorancin Guardiola.

  5. Arsenal na son Konsa

    Arsenal ta sake gudanar da sabuwar tattaunawa kan ɗaukar ɗan wasan bayan Aston Villa, Ezri Konsa.

    An fahimci cewa a cikin 'yan kwanakin nan, Gunners ɗin ta nuna aniyarta ta ƙara tayin da suka fara yi na kusan fam miliyan 30 domin ɗan wasan na Ingila.

    Sai dai har yanzu ƙimar da Arsenal ke yi wa ɗan wasan ta yi nisa da fam miliyan 60 da Aston Villa ke nema domin sayar da Konsa.

    A halin yanzu, Villa ba ta nuna wata alamar cewa za ta amince da duk wani tayi da ta gaza kai wa farashin da take nema ba.

    Konsa mai shekaru 28, wanda har yanzu yake hutu bayan kammala gasar cin Kofin Duniya, shi ne babban ɗan wasan baya da kocin Arsenal Mikel Arteta ya fi son ɗaukowa don ƙarfafa tsaron ƙungiyarsa.

  6. Carrick na son ƙarin 'yan wasa

    Michael Carrick ya ce yana matuƙar farin ciki da cinikin 'yan wasan da Manchester United ta yi zuwa yanzu. Kulob din ya kashe fam miliyan 83 wajen sayen Andrey Santos daga Chelsea da kuma Youri Tielemans daga Aston Villa, yayin da Karl Darlow, wanda kwantiraginsa ya ƙare, ya shiga a matsayin gola na biyu.

    Sai dai duk da haka, tare da matsalolin da har yanzu suke akwai a bangaren mai tsaron baya na hagu da kuma tsakiya, yayin da kungiyar ke shirin komawa gasar Zakarun Turai bayan shekaru biyu da rashin halarta, Carrick ya san cewa akwai buƙatar ƙarin sayen 'yan wasa.

    Domin a wannan kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara, United ta rasa wasu manyan 'yan wasa da ta yi burin ɗauka irin su Elliot Anderson da Matheus Fernandes, saboda ta ƙi daidaita tayin da sauran kungiyoyi suka gabatar. Haka kuma, tana kashe kuɗi ƙasa da sabbin kungiyoyin da suke sabbin hawowa gasar, Ipswich da Coventry. Saboda haka, Carrick ya san cewa akwai buƙatar ƙarin saye duk da ƙoƙarin kauce wa kurakuran tsadar kuɗi da aka yi a baya.

    Ya ce "Muna son ƙari, muna buƙatar ƙari, kuma muna ci gaba da neman hanyoyin da za mu cimma hakan."

    "Kuɗi dai kuɗi ne, na fahimci hakan. Muna ganin ya kamata mu kasance muna fafatawa kan duk abin da muke da hannu a kai, amma kuma cikin fahimtar yadda abubuwa suka kasance a tarihin baya-bayan nan."

    "A yanzu, dole ne mu yi amfani da abin da muke da shi yadda ya kamata, amma kuma dole ne mu tura iyakokinmu gwargwadon iko domin mu sake fara lashe kofuna. Wannan shi ne ƙalubalen da ke gabanmu."

  7. Carrick ya ƙi ƙarin haske kan makomar Rashford

    An bai wa kocin Manchester United Michael Carrick damar da dama ya bayyana cewa Marcus Rashford zai ci gaba da kasancewa ɗan wasan Manchester United lokacin da kasuwar saye da sayar da 'yan wasa za ta rufe a ranar 1 ga Satumba, amma ya ƙi ya yi ƙarin haske kan haka.

    "Dan wasanmu ne," haka yake faɗa a koda yaushe.

    Haka kuma an lura cewa lokacin da yake magana kan ɗan wasan gaban na Ingila, ya yi ƙoƙarin jaddada cewa Rashford ba shi ne kaɗai ɗan wasan da ke cikin tawagarsa da ya taɓa horaswa, jagoranta ko kuma ya kasance abokin wasansa ba, duk da cewa ana ganin wannan dangantaka a matsayin wani ƙarfin da zai taimaka wajen dawo da ɗan wasan cikin tawagar.

    "Ba wani yanayi ne na musamman ba ko kaɗan, kuma muna mu'amala da shi kamar yadda muke yi wa kowane ɗan wasa," in ji Carrick.

    Sai dai kuma, magoya baya da dama ba su yafe wa Rashford ba saboda yadda ya nuna halin ko in kula ga Manchester United a lokacin da yake zaman aro a Aston Villa da Barcelona, inda kusan kowa ya yi tsammanin zai ci gaba da taka leda a wannan kakar.

    Har ma waɗanda suka san shi sosai sun yarda cewa akwai babban bambanci tsakanin Rashford ɗin da ya zama mai nuna rashin sha'awa a ƙarƙashin Ruben Amorim da kuma Rashford mai cike da ƙwazo da jajircewa, wanda mutane da dama ke ganin shi ne mafi kyawun ɗan wasan da ya fito daga makarantar koyon ƙwallon ƙafar Manchester United tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson a shekarar 2013.

  8. Maresca na tsaka mai wuya

    Enzo Maresca ya shafe makonni shida kacal a sabon aikinsa na kocin Manchester City, amma tuni ya fada tsaka mai wuya.

    Yayin da ake ci gaba da danganta Rodri da komawa ƙasarsa ta Spain, babban ƙalubalen farko na Maresca na iya zama nemo wanda zai maye gurbin kyaftin ɗin da ya lashe Kofin Duniya da kuma gwarzon Ballon d'Or.

    Rodri, mai shekaru 30, yana cikin shekararsa ta ƙarshe a kwantiraginsa da City, kuma kulob ɗin ya riga ya ƙi amincewa da tayin fam miliyan 38.5 daga Barcelona, bayan da Real Madrid ma ta nuna sha'awar ɗaukarsa.

    Bayan ya taimaka wa Manchester City ta lashe kofuna uku a shekarar 2023, sannan ya jagoranci Spain zuwa lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai a shekarar da ta gabata, raunin gwiwa da ya ji ya dakile kwazonsa na wani lokaci.

    Sai dai duk da haka, Rodri ya nuna wasu bajintarsa a kakar wasan da ta gabata tare da Manchester City, kafin daga baya ya koma irin fitaccen matakin da aka saba gani daga gare shi, inda ya jagoranci Spain a matsayin kyaftin zuwa lashe Kofin Duniya a wannan bazarar.

    Darajarsa a kasuwar kwallon kafa tana da matuƙar girma a yanzu, kuma idan ya bar Manchester bayan shekaru bakwai da ya yi a kulob din, zai bar babban gibi wanda Maresca zai yi wahala wajen cikewa.

  9. Waye zai maye gurbin Rodri?

    Ayyoub Bouaddi

    Shekara: 18Ƙasa: MoroccoKulob: Lille

    Ana ta rade-radin cewa Manchester City na son ɗaukar Ayyoub Bouaddi tun farkon wannan bazarar, kuma rahotanni sun ce kulob ɗin ya riga ya yi tattaunawa da ɗan wasan na Morocco, wanda ake hasashen zai kai darajar kimanin fam miliyan 85.

    An ce Bouaddi yana da matuƙar son komawa Manchester City.

    Matashin ɗan wasan ya burge mutane sosai a Gasar Kofin Duniya ta wannan da aka yi a Amurka Canada da Mexico, bayan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da Lille ta samu kan Real Madrid a Gasar Zakarun Turai Champions League a shekarar 2024, abin da ya sa ya yi suna a babban matakin ƙwallon ƙafa na duniya.

  10. Najeriya ta rasa damar zuwa Kofin Duniya na 2027

    Najeriya ta kasa samun gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta FIFA karo na farko a tarihinta bayan da Afirka ta Kudu ta doke ta da ci 2-1 a wasan neman tikitin shiga gasar a Gasar Kofin Afirka ta Mata ta 2026 WAFCON.

    Tawagar Najeriya, wadda ita ce mafi girman matsayi a Afirka, ta shiga gasar da ke gudana a Morocco a matsayin wadda ake ganin za ta kare kambunta, amma Kamaru ta fitar da ita a wasan daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da ta sha kashi a hannun Malawi a matakin rukuni.

    Da yake dukkan ƙungiyoyin da suka kai wasan kusa da na ƙarshe sun riga sun samu gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta bana, tawagar Justin Madugu ta samu wata dama ta ƙarshe don ci kar burinta na zuwa Brazil. Wanda ya yi nasara a wannan wasa da aka buga sau ɗaya a Casablanca zai samu damar shiga wasan neman gurbi tsakanin nahiyoyi.

    Sai dai ƙwallayen da Thembi Kgatlana da Refiloe Jane suka ci a mintina 45 na biyu na wasan ne ne suka bai wa Banyana Banyana nasara, duk da cewa an samu ɗan ruɗani a ƙarshen wasa lokacin da aka bai wa Jane jan kati bayan ta samu katin gargadi na biyu saboda taɓa ƙwallo da hannunta cikin yankin bugun fanareti.

    Christy Ucheibe ta zura bugun fanaretin a minti na 93 domin rage tazarar kwallaye, lamarin da ya sa wasan ya ɗauki sabon armashi. Har ma mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Kaylin Swart, ta sake ceton tawagarta da ƙwarewa ta hanyar tare ƙwallon Michelle Alozie da ƙafafunta a mintuna na ƙarshe.

    Zakarun WAFCON na 2022, Afirka ta Kudu, ta bi Ghana zuwa matakin neman gurbin shiga gasar duniya tsakanin nahiyoyi bayan da Black Queens ta doke Cote d’Ivoire da ci 2-1 a wani wasa da aka buga a ranar Alhamis.

    Najeriya ta halarci dukkan gasannin Cin Kofin Duniya ta Mata guda tara tun daga farkon gasar da aka gudanar a kasar Sin a shekarar 1991.

    Rashin samun gurbin shiga gasar ba zai yi wa magoya bayan ƙwallon ƙafar kasar dadi ba, kasancewar sun saba da ganin Super Falcons na mamaye gasar Afirka, inda suka lashe kofin WAFCON sau 10, mafi yawan da kowace ƙasa ta taba yi.

    Sai dai doke ƙungiyar Desiree Ellis ta Banyana Banyana, wadda ke da tsari mai kyau, ba abu ne mai sauƙi ba.

    Bayan rabin farko da bai cika daukar hankali ba a Casablanca, rabin na biyu ya kasance cike da dama da ake samu a raga.

    Asisat Oshoala ta samu wata babbar dama bayan da ta kutsa cikin kariya ta hanyar karfin hali, amma bugun da ta yi daga kusa da raga bai samu ƙarfin da zai dami Swart ba.

    Ba da jimawa ba aka cire Oshoala daga wasa, kuma babu shakka za a fara tambayar ko wannan ne WAFCON na ƙarshe ga gwarzuwa mai shekaru 31 da ta lashe kyautar Gwarzon Ɗan wasan Afrika sau shida.

    Afirka ta Kudu ta fara cin kwallo a minti na 56 bayan wani kyakkyawan harin ramuwar gayya. Ronnel Donnelly ta turo wata doguwar ƙwallo mai kyau daga tsakiyar filin wasanta zuwa ga Hildah Magaia.

    Magaia ta daga ƙwallo daga gefen hagu, inda Kgatlana ta karasa da ita cikin raga duk da cewa mai tsaron Najeriya Chiamaka Nnadozie ta samu hannunta a kanta.

    Nnadozie ta sake hana Kgatlana cin wata kwallo bayan mintuna biyar, yayin da Swart ta yi wani gagarumin ceto bayan ta tare bugun kai na Uchenna Kanu da hannu guda.

    Kwallon ta biyu da Jane ta ci a minti na 77 ta samu ne bayan ƙwallon ta karkata daga kafar Ucheibe.

    Da alama Najeriya ta rasa hanyar dawowa wasan har sai da VAR ta gano taɓa ƙwallo da hannu da Jane ta yi ba tare da wata bukata ba.

    Kyaftin ɗin ba ta da wani dalilin miƙa hannunta saboda Swart na cikin kyakkyawan matsayi domin tare ƙwallon a layin raga.

    Da suka samu rinjayen yawan 'yan wasa, Najeriya ta matsa lamba sosai kuma ta kusa daidaita wasan a minti na 97 lokacin da Michelle Alozie ta bugi ƙwallo mai hatsari zuwa gaban raga, amma Swart ta sake ceto tawagarta da ƙafarta ta hagu.

    Afirka ta Kudu ta yi murnar nasararta, amma har yanzu samun gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya bai tabbata ba.

  11. Lukaku ya koma Fenerbahce daga Napoli

    Dan wasan mai shekaru 33 ya sha fama da raunuka a kakar wasan da ta gabata, inda ya buga wasanni bakwai kacal a dukkan gasa tare da kungiyar Serie A ta Napoli.

    Lukaku, wanda shi ne dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihin tawagar kasar Belgium, ya koma Turkiyya ne bayan ya taba rayuwa a can a kakar 1996-1997 lokacin da mahaifinsa, Roger Lukaku, ke buga kwallo a matsayin kwararre ga kungiyar Genclerbirligi a gasar Super Lig.

    A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta domin magoya bayan Fenerbahce, Lukaku ya ce:

    "Babban abin alfahari ne kuma gata a gare ni in shiga kungiyar ku.

    Ina cikin koshin lafiya, dari bisa dari, kuma a shirye nake domin fara aiki.

    Wannan lokaci ne mai cike da motsin zuciya a gare ni bayan shekaru masu yawa, domin zan koma Turkiyya inda na rayu tun ina karamin yaro, inda na fara fahimtar duniyar kwallon kafa ta kwararru tare da mahaifina tun ina yaro."

    Ba a bayyana adadin kudin cinikin ko tsawon kwantiragin da ya sanya hannu ba.

    Duk da matsalolin raunuka da ya fuskanta a kakar wasan da ta gabata, tsohon dan wasan Chelsea, Everton da Manchester United ya zura kwallaye uku a gasar Kofin Duniya ta wannan bazarar.

    Lukaku ya taba lashe gasar Belgium tare da Anderlecht, FIFA Club World Cup tare da Chelsea, Gasar Serie A tare da Inter Milan da kuma Napoli.

    Ya zama tsohon dan wasan Manchester United na biyu da ya koma Fenerbahce a wannan bazarar bayan Mason Greenwood, wanda aka dauko daga Marseille.

    Fenerbahce ta gama a matsayi na biyu bayan Galatasaray a gasar lig din Turkiyya a kakar wasa hudu a jere, kuma ba ta lashe kofin gasar lig tun shekarar 2014 ba.

  12. Tielemans ya nemi ahuwar magoya bayan Aston Villa

    Youri Tielemans ya nemi afuwar magoya bayan Aston Villa bayan ya bayyana cewa ya koma wata ƙungiya mafi girma, wato Manchester United, wadda ke ɗaya daga cikin abokan hamayyar Villa a Gasar Firimiya.

    Ɗan wasan tsakiya na Belgium mai shekaru 29, ya koma Old Trafford a wannan bazarar kan kwantiragin shekaru biyar bayan Manchester United ta biya fam miliyan £35m, kuɗin da ke cikin sharadin sallamarsa daga Aston Villa.

    Tielemans ya shafe shekaru uku a Villa Park bayan ya koma kungiyar daga Leicester City a shekarar 2023, inda ya buga wasanni 134 tare da zura ƙwallaye 10.

    Da yake magana yayin rangadin shirye-shiryen kakar wasa na Manchester United, Tielemans ya yaba wa Aston Villa saboda taimaka masa wajen dawo da kan ganinyarsa, sannan ya ƙara da cewa: "Amma akwai ƙungiyoyin da suka fi Aston Villa girma, kuma Manchester United na ɗaya daga cikinsu."

    Wasu daga cikin magoya bayan Aston Villa ba su ji daɗin wannan kalami ba, lamarin da ya sa Tielemans ya yi amfani da shafinsa na Instagram domin fayyace abin da yake nufi.

    A ranar Alhamis ya rubuta cewa: "Ban yi nufin kalamaina su bata ran kowa ba ko kuma su raina martabar Aston Villa Football Club ba. Ina girmama ƙungiyar sosai kuma ina matuƙar godiya da shekaru uku da na shafe a can."

    Ya ƙara da cewa: "Duk da haka, dole ne in amince cewa na yi kuskure a zaɓin kalamaina, kuma ina neman afuwa. Zan fi kula da irin kalaman da zan yi a gaba."

    "Ina yi wa ƙungiyar fatan alheri a nan gaba."

  13. Chelsea ta ba da zuwa Juma'a ga duk mai son sayan Fernandez £120

    Chelsea ta sanya wa'adin ranar Juma'a ga duk wata ƙungiya da ke son sayen ɗan wasanta na tsakiya, Enzo Fernandez, inda ta ce dole ne tayin ya kai akalla fam miliyan £120 kafin wa'adin ya cika.

    Ɗan wasan na ƙasar Argentina mai shekaru 25 ya kasance cikin rashin tabbas game da makomarsa a Stamford Bridge tun daga watan Maris, lokacin da ya fara bayyana yiwuwar komawarsa zuwa Real Madrid.

    A daidai wannan lokaci, wakilinsa Javier Pastore ya bayyana a bainar jama'a cewa abokin huldarsa ba ya samun albashin da ya dace da matsayinsa, kuma yana son barin Chelsea bayan kakar wasa mai wahala.

    Chelsea ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na 10 a Gasar Firimiya, sannan ta kasa lashe kowanne kofi bayan da ta sha kashi a hannun Manchester City a wasan ƙarshe na FA Cup.

    Rahotanni sun nuna cewa Chelsea ba za ta yi tunanin sayar da Fernandez ba sai idan ta samu tayi mai tsoka da ya kai ko ya haura fam miliyan £120, lamarin da ya sa kungiyar ta sanya wa'adin ranar Juma'a domin kawo ƙarshen rade-radin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa.

    Fernandez ya koma Chelsea ne daga Benfica a shekarar 2023 kan kuɗi mai yawa, kuma ya kasance ɗaya daga cikin muhimman 'yan wasan tsakiyar fili na ƙungiyar duk da matsalolin da Chelsea ta fuskanta a kakar wasan da ta gabata.

  14. Hukumar Kwallon Kafa ta Ireland ta janye goyon bayanta ga Infantino

    Hukumar Kwallon Kafa ta Jamhuriyar Ireland FAI ta janye goyon bayanta ga shugaban FIFA, Gianni Infantino, wanda ke fuskantar suka, yayin da Hukumar Kwallon Kafa ta Arewacin Ireland ta tabbatar da cewa tana mara wa UEFA baya kan wannan batu.

    A ranar Litinin, UEFA, tare da Concacaf da kuma Asian Football Confederation AFC, sun sanya hannu kan wata buɗaɗɗiyar wasiƙa inda suka zargi Infantino da cin amana ta hanyar abin da suka kira "yaudara".

    Wannan rikici ya biyo bayan yunƙurin da Infantino ya yi na sayar da wani kaso na harkokin kasuwancin FIFA ga wani kamfanin saka hannun jari mai zaman kansa.

    Daga baya an yi watsi da wannan shiri, amma lamarin ya jefa ƙudurinsa na neman wa'adi na huɗu a shugabancin FIFA cikin mawuyacin hali.

    A makon da ya gabata, Hukumar Kwallon Kafa ta Wales FAW ta zama ta farko daga cikin ƙasashen gida na Birtaniya da ta janye goyon bayanta ga Infantino, sannan Hukumar Kwallon Kafa ta England FA ta biyo bayanta bayan wasu kwanaki.

    FAI, wadda ke kula da harkokin ƙwallon ƙafa a Jamhuriyar Ireland, ta tabbatar da cewa ita ma ta janye goyon bayanta ga Infantino ta hanyar wata wasiƙa da ta aika wa FIFA, duk da cewa a baya ta nuna tana mara masa baya kafin wannan rikicin da ya biyo bayan Kofin Duniya.

    FAI ta ce “Bayan taron kwamitin gudanarwa na FAI, an yanke shawarar soke wasiƙar goyon bayan da ƙungiyar ta aika a farkon wannan shekara.”

    Ta ƙara da cewa, “Tun daga lokacin, mun rubuta wa FIFA domin bayyana dalilanmu.”

    Har ila yau, FAI ta bayyana cewa tana godiya ga tallafin da FIFA ke bai wa ƙwallon ƙafar Ireland, amma ta ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun haifar da damuwa mai tsanani game da:

    FAI ta kuma ce: “Saboda ƙalubalen shugabanci da muka fuskanta kuma muka shawo kansu a cikin shekarun baya-bayan nan, muna ganin muna da nauyi na musamman na kariya da kuma tabbatar da bin kyawawan ƙa'idojin gudanarwa.”

    Wannan mataki na FAI na nuna ƙara tsananta matsin lamba ga Gianni Infantino yayin da manyan hukumomin ƙwallon ƙafa ke ƙara nuna rashin amincewa da salon tafiyar da harkokin FIFA.

  15. Messi ya buga wa Inter Miami wasa bayan mutuwar mahaifinsa

    Lionel Messi ya buga wa Inter Miami a matsayin wanda aka sauya a ranar Laraba bayan rasuwar mahaifinsa da kuma nuna cewa yana iya yin ritaya daga buga ƙwallo.

    Mahaifin Messi, Jorge Messi, ya rasu a garinsu na haihuwa, Rosario da ke Argentina, a makon da ya gabata yana da shekaru 68, bayan ya shafe dogon lokaci yana fama da rashin lafiya.

    A cikin wani saƙo mai cike da tausayawa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ɗan wasan gaban Argentina mai shekaru 39 ya bayyana cewa yana tunanin makomarsa a harkar ƙwallon ƙafa: "Gaskiya ban tabbatar ba ko zan ci gaba da yin wannan na dogon lokaci."

    Bayan halartar jana'izar sirri da aka yi wa mahaifinsa a Argentina a ranar Lahadi, Messi ya koma Amurka, inda ya shiga wasa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

    Magoya baya sun tarbe shi da sowa da tafi yayin da Inter Miami ta sha kashi 3-2 a hannun Leon a wasan ƙarshe na rukuni na gasar Leagues Cup.

  16. Atlético Madrid ta amince ta sayi Remero £34.2 daga Tottenham

    Romero mai shekaru 28 zai zama ɗan wasa na huɗu da Atlético Madrid ta saya a wannan bazarar, yayin da Tottenham za ta ci gaba da mallakar kashi 15% na kuɗin da za a samu idan aka sake sayar da ɗan wasan a nan gaba.

    An kuma ce ƙungiyar Arsenal, wadda ta lashe gasar Firimiya a kakar da ta gabata, tana son ɗaukar Romero, amma Tottenham ba ta son sayar da kyaftin ɗin nata ga abokiyar hamayyarta ta Arewacin Landan.

    Romero ya bar Tottenham bayan ya shafe shekaru biyar a ƙungiyar, inda ya buga wasanni 156 tare da zura ƙwallaye 13. Ya fara zuwa Spurs ne a matsayin aro daga Atalanta a shekarar 2021.

    Dan wasan dai ya buga wa Argentina wasan gasar Kofin Duniya na wannan shekara, inda ya yi rashin wasa guda ɗaya kacal a duka gasar.

    Ana sa ran Romero ya koma atisayen Tottenham nan da kwanaki masu zuwa bayan an ba shi ƙarin lokacin hutu sakamakon halartar gasar da aka gudanar a Arewacin Amurka.

    Ya kasance kyaftin ɗin Tottenham a kakar da ta gabata lokacin da ƙungiyar ta tsallake rijiya da baya wajen faɗuwa daga gasar Firimiya.

    Bayan Tottenham ta saya shi daga Atalanta kan kuɗi kusan £42.5m, Romero ya zama muhimmin jigo a tsaron bayan ƙungiyar. An naɗa shi kyaftin a shekarar 2025 bayan tafiyar Son Heung-min.

  17. PSG ta lashe UEFA Super Cup karo na biyu a jere

    Ƙwallon da Desire Doue ya ci a minti na 62, bayan an duba ta ta na'urar VAR domin tabbatar da cewa ba a yi satar gida ba, ita ce ta ba zakarun gasar Champions League nasara a wasan da aka buga a Salzburg.

    Khvicha Kvaratskhelia ne ya fara zura ƙwallo mai kyau a minti na 20 PSG, kafin Brian Madjo na Aston Villa ya farke a minti na 45 cikin kayatarwa.

    Matashin ɗan wasan gaba mai shekaru 17 ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa cin ƙwallo a gasar Super Cup, bayan ya zura ƙwallon a wasansa na farko a filin wasa na Red Bull Arena.

    Madjo, wanda ke taka leda a tawagar Ingila ta 'yan ƙasa da shekara 17, sai da ya fara zubar da damar cin ƙwallo sau biyu a farkon wasan, inda ya harba ɗaya waje sannan ya buga ɗaya tai sama. Sai dai ya farke kwallon da John McGinn ya kawo daga gefe cikin salon watsiya dab da za a tafi hutun rabin lokaci.

    Wannan ya kawo ƙarshen takaddamar watanni takwas aka hana Aston villa ta yi masa rijista, bayan komawarsa kungiyar daga Metz a watan Janairu kan kuɗin fam miliyan 10.

    A farkon watan Agusta, Aston Villa ta yi nasarar daukaka ƙara a Kotun Sulhu ta Wasanni, wadda ta ba da damar Madjo ya buga wasannin gasa.

    Madjo ya kasance barazana ga 'yan bayan PSG a tsawon wasan, amma ƙwallonsa ba ta isa ta hana ƙungiyar Faransa kare kofin da ta lashe a karon farko a bara bayan ta doke Tottenham a bugun fanareti.

    Aston Villa, wadda ta samu damar buga Super Cup bayan lashe gasar Europa League a watan Mayu, ta samu damammaki da dama, sai dai ba ta samu ta ci kwallaye da yawa ba.

    Sai dai wannan rashin nasara ya sa kocin Villa, Unai Emery, ya yi rashin nasara a dukkanin wasanni huɗu na ƙarshe da ya jagoranta a wannan gasa, bayan ya taɓa rasa kofin tare da tsoffin ƙungiyoyinsa Sevilla da Villarreal.

    Alƙalin wasa ɗan Somalia, Omar Artan, ya kafa tarihi a matsayin alkalin wasa na farko daga wajen Turai da ya jagoranci wannan wasa, bayan an hana shi shiga Amurka yayin gasar Kofin Duniya da aka gudanar a lokacin bazarar wannan shekara.

  18. Arsenal ta sake nuna sha'awarta kan Ezri Konsa na Aston Villa

    Arsenal ta sake komawa neman ɗan wasan bayan Aston Villa, Ezri Konsa, yayin da take ƙoƙarin ƙarfafa ɓangaren tsaronta kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa.

    Konsa mai shekaru 28 na ci gaba da hutunsa bayan kammala gasar Kofin Duniya, kuma ba ya tare da tawagar Aston Villa da za ta kara da Paris St-Germain (PSG) a wasan Super Cup na ranar Laraba.

    Tun farko Arsenal ta yi ƙoƙarin sayen ɗan wasan a wannan bazarar, amma cinikin bai samu nasara ba saboda Gunners ta shirya biyan kusan fam miliyan 30 (£30m) ne kawai, yayin da Aston Villa ke ƙimanta ɗan wasan da kusan £60m.

    A kakar wasan da ta gabata, Konsa ya buga wasanni 48 a dukkan gasa, inda ya taimaka wa Aston Villa wajen lashe gasar Europa League.

    Bayan nasarar ɗauko Bruno Guimaraes daga Newcastle United, zakarun Premier League Arsenal sun mayar da hankali kan ƙarfafa tsaro, kuma sha'awarsu ga Konsa na ƙaruwa cikin sauri.

    Abin da ya sa Arsenal ke son Konsa shi ne yadda yake iya taka leda a wurare daban-daban a bayan gida, abin da ke burge masu yanke shawara a filin Emirates.

    Sai dai Arsenal ta fahimci cewa za ta buƙaci ƙara yawan kuɗin tayinta sosai idan tana son samun nasarar ɗaukar ɗan wasan. Duk da haka, har yanzu ba a san ko Aston Villa za ta amince ta sayar da shi a kan kuɗin da bai kai ƙimarta ba.

    Har ila yau, Arsenal na bibiyar Cristian Romero

    Majiyoyi da dama sun shaida wa BBC Sport cewa Arsenal ta kuma yi tattaunawa ta farko da Tottenham Hotspur kan yiwuwar ɗaukar kyaftin ɗin ƙungiyar, Cristian Romero.

    Sai dai ana ganin Tottenham ba ta da niyyar sayar wa Arsenal ɗan wasan mai shekaru 28, musamman saboda tsananin hamayyar da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu na arewacin Landan.

    Duk da haka, hakan bai hana Arsenal yin bincike da tattara bayanai game da yiwuwar cinikin ba, wanda idan ya tabbata zai kasance ɗaya daga cikin mafi ban mamaki a kasuwar musayar 'yan wasa ta bana.

  19. Aston Villa na dab da ɗaukar Matteo Ruggeri daga Atletico Madrid

    Aston Villa na gab da kammala cinikin ɗan wasan baya na Atletico Madrid, Matteo Ruggeri.

    Ana ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar ɗan wasan mai shekaru 24, kuma ana sa ran zai koma Villa Park bayan ya shafe kakar wasa ɗaya kacal a ƙungiyar Atletico Madrid.

    Ruggeri, wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya na hagu, zai maye gurbin Lucas Digne, wanda ya koma Paris Saint-Germain (PSG) a ranar Lahadi kan kuɗin da aka ruwaito sun kai fam miliyan 8.5 (£8.5m).

    Digne na iya fuskantar tsohuwar ƙungiyarsa ta Aston Villa a wasan Super Cup da za a buga a birnin Salzburg na Austria a ranar Laraba.

    Kocin Villa, Unai Emery, na neman lashe kofin Super Cup na farko a tarihinsa, bayan ya sha kashi a dukkan wasannin ƙarshe uku da ya buga a wannan gasa.

    A wannan bazarar, Villa ta himmatu wajen sake fasalin zaɓuɓɓukan da take da su a gefen hagu na tsaro, inda take neman ɗan wasan da zai ƙara ƙarfi da kuzari a wannan matsayi.

    Haka kuma, ƙungiyar ta nuna sha'awa ga mai tsaron baya na AC Milan, Pervis Estupiñán, wanda ya taɓa aiki tare da Emery a Villarreal.

    A halin yanzu, Ian Maatsen ne ake sa ran zai fara wasa a gefen hagu na Villa a karawar da za ta haɗa su da PSG a filin wasa na Red Bull Arena da ke Austria.

  20. Depay ya zargi Corinthians da karya alkawari bayan kin sabunta kwantiraginsa

    Memphis Depay ya zargi ƙungiyar Corinthians ta Brazil da nuna "halayen da ba za a amince da su ba" tare da karya yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu bayan kulob ɗin ya yanke shawarar kada ya sabunta kwantiraginsa.

    Tsohon ɗan wasan Manchester United da Barcelona ya koma Corinthians ne a shekarar 2024 kan kwantiragin shekaru biyu. Sai dai yanzu ya zama ɗan wasa mai zaman kansa bayan ya ce kulob ɗin ya janye aniyarsa ta tsawaita kwantiragin da tuni aka amince da ita.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Depay ya ce:

    "An amince da wannan sabuwar yarjejeniya kai tsaye daga shugaban kulob ɗin tare da sashen wasanni, shari'a da kuma kuɗi. Amma wasu mutane sun yanke shawarar karya wannan alkawarin."

    Ya ƙara da cewa:"Ban so wannan yanayin ya faru ba, kuma a tsawon wannan lokaci na girmama kulob ɗin. Amma yanzu an tilasta mini in mayar da martani mai ƙarfi domin kare muraduna."

    "A cikin kwanaki masu zuwa zan yi magana a bainar jama'a, amma ku sani cewa ba zan bar wannan hali da ba za a amince da shi ba ya wuce ba tare da ɗaukar mataki ba."

    Depay ya zura ƙwallaye 20 a wasanni 79 da ya buga wa Corinthians, sannan ya taimaka wa ƙungiyar ta lashe Copa do Brasil a shekarar 2025 da kuma Supercopa do Brasil a wannan shekara.

    Ƙungiyar Corinthians, wadda ke matsayi na bakwai a gasar Serie A ta Brazil, ta bayyana cewa dalilin rashin tsawaita kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 32 shi ne matsalolin kuɗi.