Amurka ta samu mutum 5,000 da suka kamu da cutar kyanda
Asalin hoton, EPA
Amurka ta tabbatar da samun fiye da mutum 5,000 da suka kamu da cutar kyanda a wannan shekara, wanda shi ne mafi yawan adadin masu kamuwa da cutar cikin shekara guda a cikin shekaru 35 da suka gabata.
Sabbin alkaluman sun kuma nuna cewa mutane takwas sun mutu sakamakon cutar, ciki har da ƙananan yara.
Kyanda cuta ce mai saurin yaɗuwa, amma ana iya kare kai daga kamuwa da ita cikin sauƙi ta hanyar allurar rigakafi.
An ayyana cewa an kawar da cutar a Amurka a shekara ta 2000 sakamakon wani shirin rigakafi mai tasiri.
ADC ta tsaya ta warware matsalolinta, ta daina ɗora mana laifi - APC
Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta faɗa wa jam'iyyar adawa ta ADC da ta tsaya ta warware rikicinta na cikin gida maimakon ɗora wa APCn da kuma ɓangaren shari'a laifi, kan matsalolin da take ciki.
APC ta zargi jam’iyyar ta adawa kan yadda ta mayar da martani ga hukunce-hukuncen kotu, tana mai cewa idan hukunci ya yi mata daɗi sai ta yaba wa ɓangaren shari’a, amma idan hukuncin ya saba wa muradunta sai ta zargi jam’iyya mai mulki da haɗa baki da kotu.
A wata sanarwa ranar Juma'a, sakataren yaɗa labarai na jam'iyar APC, Felix Morka, ya ce hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wanda ya soke shugabancin ADC, ciki har da zaɓukan fitar da gwani, sun kasance ne a matsayin aika ta ba daidai ba da jam'iyyar ta yi.
Mai shari'a Peter Lifu ya yanke hukuncin soke shugabancin ADC ne bayan ƙorafe-korafe da wasu fusatattun mambobin jam'iyyar ADC suka shigar.
Morka ya ce APC ba ta hannu a laamrin, inda ya jaddada cewa batun rikicin cikin gida ne tsakanin shugabannin ADC.
Ya zargi David Mark da abokansa kan karɓe iko da shugabancin jam'iyyar wanda ya saɓa wa tsarin doka.
Kakakin na APC ya ce a yanzu jam'iyyar ta adawa ta ɓige da ɗora laifin matsalar da take ciki kan wasu, maimakon neman warware rikicin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Houthi ta zargi Saudiyya da kai harin da ya kashe mutum 20 a wata kasuwa
Asalin hoton, Reuters
Ƴan tawayen Houthi a Yemen sun ce aƙalla mutum 30 ne suka mutu sakamakon hari ta sama da aka kai kan wata kasuwa a yankin Taiz.
Houthi ta zargi Saudiyya da kai harin, yayin da dakarun gwamnatin Yemen suka ce ƴantawayen da Iran ke goyon bayan ne suka kai shi.
Taiz yanki ne mai matuƙar muhimmanci ta fuskar dabarun yaƙi a kudu maso yammacin Yemen, kuma ya daɗe yana fuskantar mummunan faɗa tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
Yankin na kusa da mashigar ruwa da ke tsakanin Yemen da yankin kusurwar Afurka, wadda ke ɗaya daga cikin manyan hanyoyin sufuri na jiragen ruwa a duniya.
Yankin na Taiz na ci gaba da kasancewa muhimmiyar cibiyar rikici a yaƙin Yemen.
Babu wata barazana da za ta hana mu yin takara - Atiku
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya tabbatar wa magoya bayansa cewa ba zai fasa takara ba a zaɓen 2027, inda ya ce babu wata barazana ko kuma zagon ƙasa da za ta sa ya karaya.
Atiku ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma'a, inda ya ce shugaba Bola Tinubu wanda ke neman wa'adin mulki na biyu, ba zai guje wa fushin ƴan Najeriya ba.
''Kada a yi kuskuren ɗaukar hukuncin kotu na baya-bayan nan a matsayin abin da al’ummar Najeriya suke so. Babu wata barazana da za ta sa mu dakatar da takaramagudi, ko kuma ya hana ‘yan Najeriya damar zaɓar makomarsu. Da mu za a yi takara, kuma dole ne a bai wa jama’a damar yanke hukunci,” in ji shi.
Atiku ya ce za su jajirce wajen tabbatar da cewa ba a mayar da Najeriya mai tsarin jam'iyya ɗaya ba.
Ya ce Najeriya ta kowace ba ga mutum ɗaya ba, dole ne a bai wa kowa ƴancin dimokuraɗiyya da kuma samar da jam'iyya fiye da ɗaya.
"Idan waɗanda ke kan mulki sun amince da irin ayyukan da suka yi wa ƴan ƙasa, to mu haɗu a rumfar zaɓe. A kuma tabbata an yi zaɓe cikin gaskiya da adalci," in ji Atiku.
Kalaman Atiku na zuwa ne bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke takararsa da kuma shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin David Mark.
Hannayen jarin kamfanonin fasaha sun yi mummunar faɗuwa
Asalin hoton, Michael Nagle/Bloomberg via Getty Images
Hannayen jarin kamfanonin fasaha sun yi mummunar faɗuwa sakamakon fargabar cewa ci gaban fasahar kirkirarriyar basirar AI na iya raguwa.
Masu zuba jari na ta sayar da hannayen jarinsu a kamfanonin fasaha, bayan gagarumar nasarar da Jam’iyyar adawa ta Democrat ta samu a zaɓukan rabin wa’adin mulki da aka gudanar a Amurka.
Wakiliyar BBC ta ce abu mai daukar hankali shi ne faduwar darajar kamfanonin adana bayanai, wanda shi ne ruhin kirkirarriyar basirar ta AI, dole sai da shi sannan zai yi aiki.
Hannayen jarin ta kamfanin Nikkei 225 na Japan, da Kospi na Koriya ta Kudu, sun fadi da kashi 6 cikin 100.
A Taiwan kuwa, kasuwar hannayen jari ta yi faduwar da aka jima ba a gani ba cikin shekaru 25.
Rashin yin takarar Atiku Abubakar ba zai sanya sama ta faɗo ba - Keyamo
Asalin hoton, Festus Keyamo/X
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya ba za ta ruguje ba idan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya kasa yin takara a zaɓen 2027.
Keyamo ya bayyana haka ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke takarar Atiku da kuma rutsa shugabancin ADC karkashin jagorancin David Mark.
Wata sanarwa da Keyamo ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma'a, ya ce "sama ba za ta faɗo ba idan Atiku Abubakar ya gaza yin takara a 2027."
Ministan ya ce jam'iyyarsu ta APC ta amince da hukuncin kotu da ya soke nasarar da suka samu a zaɓen gwamnan Bayelsa, kwana guda kafin rantsar da David Lyon.
Ya ƙara da cewa jam'iyyar ta kuma amince da hukuncin kotun koli kan zaɓen jihar Zamfara a 2019, wanda ya soke dukkan ƴan takarar APC tare da maye gurbinsu da na PDP.
Keyamo ya kuma yi gargaɗi kan mutanen da ke sukar lauyoyi da ɓata sunan ɓangaren shari'a idan abubuwa ba su tafi yanda suke so ba.
Kiristoci a Indiya sun koka kan far musu da ake yi
Shugabannin tsirarun Kiristocin da ke zaune a Indiya sun ce suna fuskantar hare-hare kan addininsu bayan wasu jerin hare-haren da aka kai musu da lalata kadarori da kuma cin zarafi a jihar West Bengal.
Sun ce ana kai musu harin ne kan zargin suna jan ra'ayi jama'a da sauya wa mutane addini ba bisa ka’ida ba.
Rahotanni sun ce an lalata wasu coci-coci tare da kai hari ga fastoci a wannan jiha tun bayan jam'iyyar BJP mai kishin addinin Hindu ta firai minista Narendra Modi ta lashe zabe a watan Mayu a jihar.
West Bengal dai na da mutane akalla miliyan 100, da kusan kashi 90 mabiya addinin Hindu ne.
Jam’iyyar BJP mai mulki ta musanta waɗannan zarge-zargen.
Daruruwan Kiristoci ne suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin jihar, Kolkata, a ranar Alhamis.
An yanke wa jagoran adawar Tanzaniya hukuncin ɗaurin shekara huɗu
Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa babban jagoran jam’iyyar adawa a Tanzania hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari bayan an same shi da laifin tunzura jama'a.
Sai dai kotu ta wanke Tundu Lissu daga mafi girman tuhuma da ake masa ta cin amanar ƙasa.
An kama shugaban jam’iyyar Chadema a watan Afrilun bara, kan zargin kira ga mutane su kaurace wa zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a watan Oktoba.
Shari'ar da ake yi wa Tundu Lissu ta dauke hankalin mutane kan laifukan take hakkin ɗan'adam da ake zargin gwamnati tun bayan zaɓen shugaban ƙasa a bara.
Lissu ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa a shari’ar da ta janyo suka daga Tarayyar Turai da kuma Birtaniya.
An yanke wa matasan da suka kashe mata da ƴaƴanta shida a Kano hukuncin kisa
Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya babbar kotun jihar Kano ta yanke wasu matasa biyu hukuncin ɗaurin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin kashe matar da yaranta shida da aka kashe a farkon shekarar nan a unguwar Dorayi da ke birnin Kano.
A watan Janairu ne dai aka yi wa matar kisan gilla a tare da yaranta shida da rana tsaka a cikin gidanta a wani lamari mai sosai rai.
Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya ce mutum uku aka gurfanar a gaban kotun bisa zargin aikata laifin, to amma kotun ta wanke ɗaya daga ciki saboda ba ta same shi da hannu a aikata laifin ba.
''Amma su biyun da aka samu da lairin kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin rairai da rai har da shida saboda laifin fashi da makami'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa kotun ta kuma yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya har sau shida kan samunsu da laifin kisan matar da ƴaƴanta shida.
Baba jibo ya ce a yanzu matasan na da wata uku domin su ɗaukaka ƙara idan ba su gamsu da hukuncin ba.
Kan ƴan Demokrats ya rabu a yunƙurin tsige Trump
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan jam'iyyar hamayya ta Demokrats a Amurka sun samu saɓanin ra'ayi kan yunƙurin tsige Shugaba Donald Trump daga muƙaminsa.
Wasu, kamar Alexandria Ocasio-Cortez, sun goyi bayan batun, suna masu kafa hujjoji da rashin halascin yaƙin Iran da kuma wasu batutuwa da za a iya amfani da su wajen tsige shi daga shugabancin.
A ɗaya ɓangaren kuma, wasu na ganin ya kamata a yi taka-tsantsan, suna cewa akwai yiwuwar wannan yunƙuri ba zai yi nasara ba.
Har yanzu ba a tabbatar ko ƴan jam'iyyar Democrat za su cimma matsaya guda wajen ci gaba da yunƙurinsu na tsige Trump ba.
Haka kuma babu tabbas ko yunƙurin zai haifar da wani mataki mai tasiri a kansa ba.
A nasa ɓangare Shugaba Trump ya bayyana yunƙurin tsige shi da aka yi a wa'adinsa na farko a matsayin "abin da ya saba wa doka."
'Jiragen ruwa biyu sun kama da wuta bayan taka nakiya a mashigar Hormuz'
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar juyin juya halin Iran, IRGC taa ce wasu jiragen ruwa na dakon mai biyu da ke kokarin wucewa ta mashigar Hormuz sun kama da wuta bayan sun taka wata nakiya.
Sashen rundunar sojin ruwa ta IRGC ya ce tankokin biyu sun kashe "dukkan na'urorinsu na bibiyarsu da tantancewa", kuma suna shirin bi ta mashigar ne ta wata hanyar da suka bayyana a matsayin "wadda ba a amince da ita ba".
Sanarwar da IRGC ta fitar ba ta bayar da ƙarin bayani game da ƙasashen da suka mallaki jiragen ba.
Iran ta ce wajibi ne jiragen su ratsa ta mashigar Hormuz ta hanyar da ƙasar ta tsara ta kuma amince da ita.
Rahotanni sun ce wasu jiragen ruwa da na dakon mai na amfani da wata hanya da aka ƙirƙiro a 'yan makonnin nan domin kauce wa takunkuman da Iran ta sanar.
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufurin makamashi a duniya.
Kafin fara yakin Amurka da Isra'ila da Iran a watan Fabrairun wannan shekara, kusan kashi ɗaya cikin biyar na cinikin ɗanyen mai da iskar gas na duniya na bi ta mashigar.
Dilolin wayoyin hannu a Najeriya na son NCC ta dakatar da dokar tantance wayoyi
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar masu sayar da wayoyin hannu ta jihar Kano ta bayyana damuwa kan matakin hukumar NCC na aiwatar da wani sabon shirin tantance wayoyin hannu da sauran na’urorin sadarwa a ƙasar.
Yayin da ya rage ƴan kwanaki hukumar ta NCC ta fara aiwatar da tsarin, ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin abin da zai kawo matsalolin da za su ta yi gagarumar asara da haifa da matsalar rashin aikin yi ga matasa.
Tun da farko dai NCC ta saka wa'adin 7 ga watan Nuwamba a matsayin ranar ƙarshe da za ta rufe duka wayoyin da ba ta tantance ba a faɗin ƙasar.
To amma ƙungiyar masu sayar da wayar ta ce ba duka nau'o'in wayoyin da take sayarwa ne hukumar ke tantancewa ba.
''Duka nau'o'in wayoyin da ba sabbi ba d ake kira London yus ba sa cikin waɗanda hukumar ke tantancewa, mu kuma da dama su ne muke sayarwa'', a cewar Abubakar Ibrahim Ma'aji ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar.
Ma'aji ya ƙara da cewa matakin NCC na zuwa ne bayan sun narka kuɗaɗensu masu yawa wajen sayo wayoyin, wani abu da ya ce zai sa su tafka muguwar asara idan dokar ta tabbata.
Ya ƙara da cewa kaso mai yawa na wayoyin da suke sayarwa, a ƙasashe maƙwabta suke sayar da su ba Najeriya, wani abu d aya ce bai kamata dokar NCC ta shafe su ba.
A nata ɓangare hukumar NCC ta ce ta ɓullo da tsarin tantance wayoyin ne da nufin magance matsalolin barazanar tsaro da kakkaɓe ayyukan masu damfarar intanet.
Sojojin Najeriya sun musanta yin sulhu da Boko Haram
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce babu batun tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi na Boko Haram da ISWAP.
Wannan na zuwa ne bayan da wata kafar yaɗa labari ta ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniyar sulhu da Boko Haram ɓangaren Bakura Doro, matakin da kafar ta ce ya taimaka wajen samun zaman lafiya a wasu sassan yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Da yake jawabi a wani taro kan harkokin leƙen asiri a babban birnin tarayya Abuja, kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce nasarorin da aka samu a baya-bayan nan, ciki har da kashe masu tayar da ƙayar baya da kama waɗanda ake zargi da kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su sun isa ƙaryata iƙirarin.
Sojojin sun ce jami'an tsaro na ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai lamba.
"Ina so na bayyana ƙarara cewa babu maganar tsagaita wuta ko kaɗan... idan aka yi la'akari da nasarorin da aka samu a dukkan ayyukanmu, a bayyane yake cewa ba mu sassautawa," in ji Uba.
Ya kuma ce Najeriya na tattaunawa da ƙasashen makwabta na yankin Sahel da suka fice daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS kan haɗin gwiwar tsaro da harkokin diflomasiyya
Gwamnatin Amurka ta musanta ajiye aikin sakataren tsaro na waje
Asalin hoton, Getty Images
Fadar White House ta musanta jita-jitar da ke cewa Sakataren Tsaro Pete Hegseth da Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio na iya yin murabus yayin da ake hasashen za a samu sauye-sauye a gwamnatin Donald Trump bayan zaɓe.
Kafofin watsa labarai na Amurka sun ruwaito cewa an yi kira da a cire Pete Hegseth daga muƙaminsa, musamman saboda yadda ya tafiyar da yakin da Iran, wanda wasu ke ganin yana daga cikin abubuwan da suka jawo wa jam'iyyar Republican gagarumar shan kaye a zabukan.
Wani ɗan majalisar dokokin Republican da ke shirin barin muƙaminsa ya yi barazanar gabatar da ƙudirin tsige Hegseth a mako mai zuwa.
Sakataren Tsaron Amurka ya kuma fitar da wani bidiyo inda ya kare matakansa tare da yin Allah wadai da wannan yunkuri.
"Kun gani, suna sukarmu, suna sukarmu ne saboda muna yin aiki yadda ya kamata. Waɗannan yunƙuri ba za su yi nasara ba. Ba za mu ja da baya ba," in ji shi.
Yasmin Ansari, ƴar jam'iyyar Democrat kuma Ba'amurkiya mai asalin Iran da ke wakiltar jama'a a Majalisar Dokokin Amurka, ita ma tana kira da a tsige Pete Hegseth.
A ɗaya ɓangaren kuma, Marco Rubio ya musanta rahotannin da ke cewa yana tunanin sauka daga muƙaminsa da nufin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2028.
A wata hira da jaridar New York Times, Mista Rubio ya ce ci gaba da aiki tare da gwamnatin Trump har zuwa ƙarshen wa'adin shugabancinsa "shi ne shirin da nake da shi tun farko."
Fadar White House da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka sun musanta rahotannin da ke cewa Rubio na iya sauka daga muƙaminsa bayan shan kayen da aka yi a zaɓukan wannan mako, inda dukkansu suka bayyana rahotannin a matsayin "labaran bogi".
A ranar Alhamis, kamfanin Bloomberg ya ruwaito, yana mai ambaton majiyoyin da ba a bayyana sunayensu ba, cewa Marco Rubio na tuntubar masu ba shi shawara kan makomarsa ta siyasa.
'Iran na gyara cibiyoyin makaman linzaminta da aka lalata'
Asalin hoton, Getty Images
Wani binciken hotunan tauraron ɗan'adam da BBC ta gudanar ya nuna cewa Iran na gudanar da manyan ayyukan gine-gine kusa da muhimman wuraren ajiyar makamai masu linzami guda biyu, inda ta ke ci gaba da gyare-gyare a wasu cibiyoyin da aka lalata a lokacin rikicinta da Amurka.
Masana sun bayyana cewa hotunan na nuni da yiwuwar cewa Iran na ɗaukar matakan ne don kare kanta daga sabbin hare-hare.
Wakiliyar BBC ta ce ana gina sabbin rufi a gine-ginen da aka ruguza a wata cibiya da ke yammacin ƙasar, yayin da a wani sansanin soji da ke gabashin birnin Tehran aka kwashe duk wasu ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe bayan luguden wutan da aka yi a yankin
Binciken sashen tantance bayanai na BBC dai ya nuna cewa gyare-gyaren sun shafi aƙalla cibiyoyi 12.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin kallon kyawawan bidiyoyi da ƙayatattun hotunan, sannan ku yi yi tsokaci a kai.