Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Lahadi 23 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Har yanzu muna shakkar alaka da Isra'ila - Syria

    Ministan Harkokin Wajen Syria ya ce Damascus na sa ran za a sake dawo da tattaunawa da Isra’ila kan yarjejeniyar tsaro nan ba da jimawa ba.

    Kwanaki kaɗan bayan da Isra’ila ta kai harin sama kan wani sansanin sojan Syria, Asad Shaibani ya jaddada a wata hira da Reuters cewa babban abin da Damascus ke son cimmawa a yanzu shi ne dakatar da hare-haren Isra’ila.

    A cewarsa, domin samun ci gaba a wannan fanni, ya zama dole bangarorin biyu su ɗauki matakai na gina amincewa da juna.

    Shaibani ya ce an dakatar da tattaunawar kan yarjejeniyar tsaro tun bayan fara yaƙin Iran, amma yana sa ran za a sake farawa nan ba da jimawa ba. Ya kuma ce an katse hulɗa tsakanin ɓangarorin biyu bayan da Isra’ila ta kai hari kan wani sansanin sojin saman Syria.

    Gwamnatin Syria na fatan cimma yarjejeniyar zai kasance mataki na ƙarshe da zai kai ga janye Isra’ila daga yankunan Syria.

    Shaibani ya yi kira ga Isra’ila da ta yi amfani da wannan “dama ta tarihi”, yana cewa “ƙofofin diflomasiyya” har yanzu a buɗe suke. Sai dai ya kuma nuna damuwa game da rashin amincewa da juna:

    “Mun yi imanin cewa ya kamata a samu hulɗa, musamman da ɓangaren da yake ci gaba da barazana ga tsaron Syria. Amma idan wannan hulɗar ba za ta haifar da wani amfani ba, ba ma buƙatarta. A halin yanzu, ba mu amince da Isra’ila ba.”

    Amurka ta kwashe fiye da shekara guda tana ƙoƙarin sasanta tsakanin Isra’ila da gwamnatin Shugaban Syria Ahmed al-Sharaa, wanda Washington ke ɗauka a matsayin sabon abokinta a Gabas ta Tsakiya, domin cimma yarjejeniyar tsaro. Sai dai har yanzu waɗannan ƙoƙarin ba su yi nasara ba.

    A wannan lokacin, Isra’ila ta tura dakarunta zuwa cikin yankin Syria tare da kai hare-hare kan wuraren gwamnati da kayan aikin soji, tana mai cewa matsalar tsaro ce dalilin hakan.

    Ofishin Firaministan Isra’ila bai mayar da martani ga buƙatar Reuters ta neman bayani kan kalaman ministan na Syria ba.

  2. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ’yan ta’adda sama da 20 a Borno

    Sojojin Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), sun ce sun kashe sama da ’yan Boko Haram 20 a wurare daban-daban da ke ƙananan hukumomin Monguno da Biu na Jihar Borno.

    Hedikwatar ta ce an gudanar da hare-haren ne ta amfani da jiragen sama, bisa sahihan bayanan sirri, tsakanin daren 21 ga Agusta zuwa farkon safiyar 22 ga Agusta, 2026.

    Ta ce hare-haren sun yi nasarar raunana wuraren da aka gano, tare da dakile ƙoƙarin ’yan ta’addan na taruwa, sake haɗuwa da juna da kuma gudanar da ayyukansu cikin ’yanci a yankin, kamar yadda tashar Channels mai zaman kanta ta ruwaito.

    A ɗaya daga cikin ayyukan, wani jirgin sama mai aikin leƙen asiri da kai hari ya gano tare da bin diddigin wasu mayaka da ake zargi da su a yankin Aduwa na ƙaramar hukumar Monguno, kafin daga bisani ya gano wata babbar taro a cikin wani ƙauye.

    Bisa ga sanarwar da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Sojoji, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, bayan bin ƙa’idojin aiki da samun izini, an kai wani hari na musamman kan wurin da aka gano.

    Binciken da aka yi bayan harin ya nuna cewa an samu gagarumin tasiri kan taron ’yan ta’addan, inda kimanin ’yan ta’adda 16 aka kashe a hare-hare biyu na musamman.

    A wani aikin daban da aka gudanar a kusa da Buratai, ƙaramar hukumar Biu, Operation HADIN KAI ta ce wani jirgin saman soji ya gano wasu ’yan ta’adda da ake zargi da su sun taru a wani wuri.

    Bayan ci gaba da sa ido da kuma samun izinin da ya dace, jirgin ya kai hari na musamman kan wurin, inda aka ce an kashe wasu ’yan ta’adda 10.

    Sanarwar ta ce waɗannan ayyukan sun nuna ƙara ingancin tsarin leƙen asiri da sa-ido na Operation HADIN KAI wajen gano tare da dakile motsin ’yan ta’adda kafin su zama babbar barazana ga sojoji da al’ummomin da ke cikin haɗari.

  3. Wata hadakar malamai a Arewacin Najeriya ta amince Tinubu ya zarce

    Wata hadakar malaman Musulunci daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da amincewa da ya sake tsayawa takara a zaben 2027.

    Hadakar ta bayyana matsayarta ne yayin taronta na Muslim Intellectuals Forum, wanda aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello, Sabuwar Sakatariya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

    Hadimin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Isah Muhammad Yusuf, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

    A cewarsa, taron ya hada malaman Musulunci da masana daga jihohin Arewacin Najeriya 19, inda suka bayyana amincewarsu da jagorancin Shugaba Tinubu da kokarinsa na magance matsalolin da ke addabar yankin, musamman matsalar rashin tsaro.

    Kungiyar ta kuma kada kuri'ar amincewa da Shugaba Tinubu, tare da kira ga 'yan Najeriya, musamman al'ummar Arewa, da su mara wa shugaban baya da jam'iyyar APC a zaben 2027.

    Goyon bayan na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyu da kungiyoyin siyasa ke kara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.

    A nata bangaren, kungiyar ta ce ta yi imanin cewa jagorancin Tinubu da matakan da gwamnatinsa ke dauka za su taimaka wajen magance kalubalen da Arewacin Najeriya ke fuskanta.

  4. Hukumomin tsaron Iran sun gano “na’urorin Starlink 997”

    Farajah, rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta ce a cikin watanni huɗu na farkon wannan shekara, ta gano “na’urorin tauraron dan adam na Starlink 997 da kayan haɗa su.”

    Shugaban sashen tattalin arziki na Farajah ya ce: “Tun bayan yaƙin kwana 12, ’yan sanda sun ƙara mai da hankali wajen ganowa tare da kwace na’urorin tauraron dan adam na Starlink da kayan haɗinsu. Dukkan sassan ’yan sanda, daga iyakokin ƙasar har zuwa cikin birane, sun fara aiki sosai a wannan fanni.”

    Hossein Rahimi ya kuma ce: “Dangane da wannan batu, an kama mutum 163, sannan an kwace motoci 15 da ke ɗauke da kayan aikin Starlink.”

    A cewarsa, mafi yawan waɗannan na’urori sun shigo ƙasar ne ta iyakokin yamma da arewa maso yammacin ƙasar, da kuma daga Azerbaijan da yankin Kurdistan. Haka kuma, wasu sun shigo ta iyakokin ruwa na kudancin ƙasar, ciki har da hanyoyin Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Oman.

    Wannan fasahar tauraron dan adam da ake amfani da ita wajen haɗa mutane da intanet na duniya haramun ce a Iran. Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Iran sun ruwaito lokuta da dama na kama mutane saboda mallakar tashoshin Starlink ko saye da sayar da su.

    Cibiyar sadarwar Starlink wata tarin tauraron dan adam ce da aka ƙera domin samar da intanet mai sauri, mai ƙarancin jinkiri, a duk faɗin duniya.

  5. Ƙasar da ta taimaki Amurka a yaƙin tattalin arziki maƙiyarmu ce - Iran

    Ƙasashen da suka shiga “yaƙin tattalin arziki” na Amurka ana ɗaukar su a matsayin abokan gaba

    Jami’an Iran sun ce duk wata ƙasa da ta shiga abin da suka kira “yaƙin tattalin arziki na Amurka da Iran” za a ɗauke ta a matsayin abokiyar gaba.

    A baya Iran ta kai hari kan wasu ƙasashe a yankin da ke karɓar sansanonin sojojin Amurka, waɗanda daga cikinsu ne aka kaddamar da hare-haren Amurka da dama.

    A halin yanzu, tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta tsaya cik, amma Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana a ranar Juma’a cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen rikicin da ya kwashe watanni shida yana gudana.

  6. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.