Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello
'Batun mashigar Hormuz ya fi na nukiliyar Iran muhimmanci a yanzu'
Asalin hoton, Reuters
Batun nukiliyar Iran ya zama abu na biyu mafi muhimmancin a yanzu a cewar daraktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), Rafael Grossi.
Ya ce har sai an fayyace halin da ake ciki a game da mashigar Hormuz da sauran batutuwan da ke da alaƙa da shi kafin a koma batun nukiliya.
A wata hira da jaridar Argentina ta La Nación, Grossi ya ce an dakatar da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar Iran ne domin batun da ya fi shi muhimmanci.
Ya ce: “Har sai an fayyace babban batu na mashigar Hormuz da sauran batutuwan da suka shafi lamarin, batun nukiliyar ya zama na biyu.”
Grossi ya kuma bayyana cewa halin da fayil ɗin nukiliyar Iran ke ciki a yanzu ya samu tasiri daga sauye-sauyen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yaƙe-yaƙe.
’Yan Najeriya 67 sun koma gida daga Afirka ta Kudu
Asalin hoton, National Commission for Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons (NCFRMI)
Hukumomin Najeriya sun ce ’yan ƙasar 67 sun koma gida daga Afirka ta Kudu a ƙarƙashin wani shirin mayar da ’yan ƙasa da wasu ’yan kasuwar Najeriya ke ɗaukar nauyin sa.
Mutanen sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a yammacin Laraba, a cikin jirgin kamfanin South African Airways, inda ta ce jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da hukumar kula da ’yan gudun hijira, ’yan ci-rani da masu gudun Hijira a cikin gida (NCFRMI) ne suka tarbe su.
A cewar NCFRMI, waɗanda suka dawo sun ƙunshi manyan mutum 30, yara 36 da jariri guda ɗaya.
Mai kula da shiyyar Kudu maso Yamma na hukumar, Alex Oturu, ya shaida wa BBC cewa wasu ’yan kasuwar Najeriya ne suka ɗauki nauyin aikin, ƙarƙashin jagorancin Ikem Ume-Ezeoke.
Ya ce kowa daga cikin waɗanda suka koma ya samu tallafin naira 50,000 ($32; £24), yayin da NEMA ta taimaka musu wajen ci gaba da tafiya zuwa garuruwansu a sassa daban-daban na Najeriya.
Wannan sabon aikin ya zo ne gabanin ranar ƙarshe ta 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin da ke adawa da baƙin haure a Afirka ta Kudu suka sanya, inda suka yi kira ga ’yan ci-ranin da ba su da takardun izinin zama su bar ƙasar.
EFCC za ta ba wanda ya fallasa kuɗin sata da aka ɓoye a ƙasar waje kashi 5
Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Hukumar EFCC ta ce mutanen da suka bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano dukiyar da aka wawure daga Najeriya tare da ɓoyewa a ƙasashen waje, na iya samun lada har zuwa kashi 5 cikin 100 na asalin dukiyar da aka ƙwato.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kira ga mutanen da ke da sahihan bayanai kan inda aka boye kuɗaɗe da kadarorin Najeriya a ƙasashen waje da su fito su bayar da bayanan.
Ya yi wannan kiran ne yayin wani taro kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Ingila, ina ya ce a ƙarƙashin tsarin ladar, mai fallasa bayanai (whistleblower) wanda bayanansa suka kai ga samun nasarar ƙwato dukiya, na iya samun lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka ƙwato.
Da yake magana a taron, Olukoyede ya ce ya kamata a ƙara matakan kariya ga mutanen da ke bayar da bayanan da ke taimakawa wajen tona asirin laifukan kuɗi, inda ya nanata cewa kariyar na da muhimmanci, musamman a ƙasar da wasu masu bayar da bayanai ke fargabar ramuwar gayya bayan fallasa mutanen da ke da alaƙa da siyasa ko kuma masu tasiri a ƙasar.
Najeriya ta ƙaddamar da manufar kare masu fallasa bayanai ta gwamnatin tarayya a shekarar 2016, wadda ta tanadi lada ga mutanen da suka taimaka wajen fallasa almundahana, ɓoye ko karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kadarorinta.
Sai dai, duk da alkawarin bayar da lada, an taɓa nuna damuwa cewa wasu masu fallasa bayanai sun shafe lokaci suna jiran biyan kuɗaɗen da aka yi musu alkawari. Haka kuma, babu wata takamaiman doka da ke ba su cikakkiyar kariya.
Sai dai sabuwar sanarwar EFCC kan ladar ta haifar da tambayoyi kan ko hukumomi za su iya tabbatar da sirri, kariya da kuma biyan ladan kamar yadda aka yi alƙawari.
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da dala biliyan 1 domin tallafa wa marasa ƙarfi
Asalin hoton, Federal Ministry of Information and National Orientation, Nigeria
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin HOPE-SP na dala biliyan 1 domin agaza wa marasa ƙarfi a ƙasar, inda ta ce shirin zai sauya yanayin tallafin da ake yi zuwa na ɓullo da hanyoyin dogaro da kai.
Shirin mai suna Household Prosperity and Economic Social Protection Project (HOPE-SP), an ƙiyasta zai ci dala biliyan 1, a wani mataki da ke nuna sauyin tsarin tallafin jinƙai daga bayar da tallafi na ɗan lokaci zuwa samar da hanyoyi da gwamnatin ta ce masu ɗorewa da za su taimaka wa jama’a su fita daga talauci.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta ƙaddamar da shirin a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ta yaba wa ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Dr. Bernard Doro, da tawagarsa bisa ƙoƙarin da suke yi.
An tsara sauye-sauyen ne domin inganta yadda ake gano da tantance gidajen da ke cikin buƙata, da kuma tabbatar da cewa tallafi ya isa ga waɗanda suka fi cancanta. Haka kuma, za su ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirye-shiryen jinƙai da na rage talauci, tare da samar da tallafin gaggawa yayin fuskantar matsaloli da kuma ƙara gaskiya da riƙon amana.
Ministan ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan shirin shi ne One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS), wanda zai haɗa shirye-shiryen agaji, zamantakewa da rage talauci cikin tsari guda na ƙasa.
"Tsarin zai yi amfani da rajista guda, hanyoyin isar da tallafi na zamani, ingantaccen tsarin kuɗaɗe da bayanan sirri na zamani domin yanke shawara cikin gaggawa."
Babban Sakatare na Ma’aikatar, Olubunmi Olusanya, ya ce sauye-sauyen za su ƙarfafa haɗin gwiwa da riƙon amana, yana mai jaddada cewa babban ma’aunin nasara shi ne ganin sauyi na zahiri a rayuwar ‘yan Najeriya masu buƙata.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, da abokan hulɗar kamar Tarayyar Turai da Bankin Duniya, sun yaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin ayyukan jin jinƙai a Najeriya.
Aƙalla mutum 177 sun mutu, sama da 800 sun ɓace a ambaliyar Nepal
Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Nepal ta tura jami'ai kusan 2,000 domin taimaka wa aikin nemo mutanen da suka ɓace bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a arewacin ƙasar.
Wakiliyar BBC ta ce har yanzu tituna da hanyoyin sadarwa a toshe suke.
Rahotanni sun ce fiye da mutum 160 sun mutu a sakamakon ambaliyar, yayin da sama da 'yan yawon buɗe ido 600 ke cikin waɗanda har zuwa yanzu ba a san inda suke ba.
Sannan a iyakar da ke yankin Tibet na China kuwa, kafafen yaɗa labaran China sun ce mutum uku sun mutu, yayin da ake neman sama da wasu 500 da suka ɓace.
Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa mai ƙarfi ya rika kwarara cikin yankunan da jama'a ke zaune, yayin da mutane ke gujewa zuwa saman tuddai domin tsira da rayukansu.
Ambaliyar ta lalata ƙauyuka gaba ɗaya, tare da rusa hanyoyi, da gadoji da tashoshin samar da wutar lantarki.
Wanda ake zargi da harin 11 ga Satumba a Amurka, Khalid Sheikh zai bayyana a gaban kotu
Asalin hoton, HO/AFP via Getty Images
Bayanan hoto, Wannan hoto ne da aka ɗauka na Khalid Sheikh Mohammed a shekarar 2003 bayan an kama shi
Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ce wani alƙalin kotun soji ya yanke hukuncin cewa Khalid Sheikh Mohammed, wanda ake zargin shi ne jagoran shirya hare-haren 11 ga Satumba (9/11), zai gurfana a gaban kotu a watan Yunin shekarar 2028, fiye da shekara 25 bayan harin.
An kama Khalid Sheikh Mohammed a shekarar 2003, kuma tun daga shekarar 2006 ake tsare da shi a sansanin sojin ruwan Amurka da ke Guantanamo Bay a Cuba.
Ana zarginsa da tsara harin ta hanyar amfani da jiragen saman fasinja da aka yi garkuwa da su wajen kai hare-hare kan cibiyar kasuwanci ta duniya da kuma hedkwatar tsaron Amurka ta Pentagon a shekarar 2001.
Harin na 11 ga Satumba shi ne mafi muni da aka taɓa kai wa a ƙasar Amurka, inda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 3,000.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.