An samu mutumin da ake zargin ɗan Hamas ne da laifin daba wa jami'in tsaro wuka a Birtaniya
Wani mutum da ake zargin mamba ne a ƙungiyar Hamas, kuma Jamus ke nema bisa zarginsa da hannu a wani shirin kashe Yahudawa, an same shi da laifin daba wa wani jami'in tsaro wuka a wata kotu a Birtaniya.
An tuhumi Mohammed Al-Fateh, wanda aka fi sani da Mohammed Naeem, mai shekara 40, haifaffen Jamus, da kai wa jami'in hari da manyan wuƙaƙen girki guda biyu a wajen gidansa da ke birnin Birmingham a shekarar da ta gabata.
Alƙalan kotun sun same shi da laifin raunata mutum ba bisa ƙa'ida ba, ɗaukar wuƙaƙe biyu da kuma lalata dukiya.
Sai dai sun wanke shi daga tuhumar da ta fi waɗannan tsanani, ta illata mutane da gangan.
Rahotanni sun ce Al-Fateh ya taɓa kasancewa mai gadin tsohon shugaban Hamas, Ismail Haniyeh. An ba shi mafakar siyasa a Birtaniya a shekarar 2015, sannan ya zama ɗan ƙasar a shekarar 2020.
A yayin shari'ar, an nuna wa alƙalan kotun wani faifan bidiyo da ke nuna Al-Fateh yana yi wa jami'in barazana da manyan wuƙaƙe guda biyu a wajen gidansa da ke yankin Kings Heath na birnin Birmingham.
Sai dai ba a sanar da alƙalan kotun yiwuwar alaƙarsa da Hamas ba, wadda Birtaniya ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci.


























