WHO ta yi Alla-wadai da hare-haren da ake kai wa ma'akatan lafiya a Kongo
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa ma'aikatan lafiya da ke aikin dakile barkewar cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
Wannan na zuwa ne bayan kashe ma'aikatan lafiya huɗu a hare-hare daban-daban da suka faru cikin makonni biyu da suka gabata a lardunan Tshopo da Arewacin Kivu.
Dakta Tedros ya bayyana hare-haren a matsayin abin takaici matuƙa, yana mai gargadin cewa rashin tsaro ne babban cikas ga ƙoƙarin shawo kan barkewar cutar, wadda yanzu ke ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu yankuna.
Kawo yanzu sama da mutum 11,000 da suka kamu da cutar a larduna takwas na ƙasar, yayin da aƙalla mutane 5,300 aka tabbatar sun mutu sakamakon cutar.
Matsalar sauyin yanayi na ci gaba da tsananta - Guterres
Asalin hoton, Getty Images
Babban sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya mai barin gado, Antonio Guterres, ya shaida wa shugabannin duniya da suka hallara a taron MDD da ake yi a Turkiyya cewa matsalar sauyin yanayi na ci gaba da tsananta fiye da yadda ake iya shawo kanta.
Guterres ya ce shekaru huɗu da suka gabata su ne mafi zafi da aka taɓa samu a tarihin da aka yi rubuce-rubucen illar sauyin yanayi..
Guterres kenan ya ke cewa wadanda suke amfana a fitar da hayakin mai gurbata muhalli, su ya kamata su biya kudaden magance matsalar da suka haddasa.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya shaida wa taron cewa abin takaici ne yadda ake fuskantar matsalar sauyin yanayi a daidai lokacin da duniya ke fama da wasu matsaloli mafi tsanani.
Gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a Sifaniya
Asalin hoton, Getty Images
Ana gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na faɗin Spain, lamarin da ya janyo cikas ga tafiye-tafiye da harkokin sufuri a ƙasar.
Wannan ne yajin aikin gama-gari na farko da aka yi a kasar cikin shekaru 14, inda ƴansanda suka kama masu zanga-zanga da dama a arangamar da suka yi a safiyar yau.
Wakilin BBC ya ce an ga yadda aka katse tafiye-tafiye, mutane da dama sun kauce wa yin balaguro ta jiragen kasa, a cikin gari ma tituna sun yi tsit ba mutane.
Ƙungiyoyin ƙwadago da masu rajin kare haƙƙin jama'a a Sifaniya sun dade suna neman gwamnati ta ɗauki matakan magance matsalar tsadar gidaje, wadda ta haddasa tashin farashin kuɗin haya.
Tinubu ya gaza a wajen ƴan Najeriya - ADC
Asalin hoton, X/ADC
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gaza cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya, inda ya ce rabon tallafin kuɗi, abinci da kyaututtuka a tarukan siyasa ba zai dawo wa gwamnati da amincewar jama’a ba.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga hukumar yaƙi da cin hanci (EFCC) da hukumar zaɓen Najeriya (INEC) da su binciki rahotannin da ke cewa magoya bayan jam’iyyar APC suna raba kuɗi a tarukan yaƙin neman zaɓe.
Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Laraba, jam’iyyar ta zargi APC da ƙoƙarin neman goyon baya siyasa ta hanyar amfani da kuɗi wajen jawo mutane gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kwamitin ya ce rabon kuɗi da wasu kayayyaki ya nuna rashin tausayawa, musamman a daidai lokacin da miliyoyin ’yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa.
Ta ce rahotanni sun nuna cewa an bai wa shugabannin mata na APC motoci masu tsada, sannan an raba kuɗi da abincin da aka dafa ta hannun ƙungiyar City Boy Movement da ɗan shugaban ƙasa ke jagoranta.
Haka kuma, ta ba da misali da wani hoton bidiyo da ke nuna wata shugabar mata ta APC tana raba kuɗi da kayayyaki.
ADC ta kuma nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin nuna bambanci wajen mu’amala da talakawan Najeriya da kuma ’yan siyasa dangane da zargin cin zarafin takardun kuɗin naira.
Jam’iyyar ta buƙaci EFCC da INEC su gudanar da bincike kan waɗannan zarge-zarge, tare da ɗaukar mataki idan aka samu cewa an karya dokokin zaɓe ko na kuɗi.
Ta kuma yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ba ta da abin da za ta nuna a cikin shekaru uku da rabi da ta shafe tana mulki, inda ta ce an faɗa matsin tattalin arziki, ƙaruwar matsalar tsaro da kuma bashin da ake bin ƙasar.
'Mun fara bincike don kama waɗanda suka kashe shugaban Miyetti Allah a Taraba'
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansanda a jihar Taraba ta tabbatar da kashe shugaban Miyetti Allah na jihar, reshe karamar hukumar Takum, Alhaji Ibrahim Saidu, bayan buɗe masa wuta da ake zargin wasu ƴanbindiga sun yi masa a kofar gidansa.
Wata sanarwa da kakakin ƴansanda jihar, ASP Victor Mshelizah ya fitar, ta ce tuni ta kaddamar da bincike don gano mutanen da suka aikata ta'asar domin gurfanar da su gana shari'a.
Sanarwar ta ce kwamishinan ƴansandan jihar, CP Edwin Ogbehagha ya ba da umarnin ɗaukar duk matakan da suka dace domin gano abin da ya janyo aka kashe shugaban na Miyetti Allah.
Ƴansandan sun kuma ce suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa da kuma tabbatar da cewa ba a ƙarya doka da oda ba.
Don haka ne rundunar ta buƙaci al'ummar yankin da lamarin ya faru, musamman iyalan mamacin da kuma ƴan uwansa da su kwantar da hankali da kuma guje wa ɗaukar matakin da zai jawo bazuwar rikici ko kuma harin ramuwa.
Daga yanzu mutum uku ne za su riƙa magana da yawun kwamitin yaƙin zaɓen mu - APC
Asalin hoton, Isah Muhammad Salisu/FB
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC ya sanar da yin wasu sauye-sauye a ɓangaren sadarwa da kuma yaɗa labaran kwamitin.
Wata sanarwa da kwamitin ya fitar ranar Laraba, ya amince cewa daga yanzu mutane uku ne kaɗai za su riƙa magana a madadin kwamitin yaƙin neman zaɓen.
A cewar kwamitin, mutanen su ne darakta-janar na yaƙin neman zaɓen, Sanata Abdulaziz Yari, ministan ma’adanai, Dele Alake, a matsayin mai magana da yawun kwamitin da kuma ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris.
Sanarwar ta ƙara da cewa duka mutanen da aka sanar a irin wannan matsayi a baya, za su koma ƙarƙashin karamin kwamitin yaɗa labarai a matsayin mambobi.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen zai riƙa zaɓar mutanen da suka dace domin riƙa magana da yawunsa idan buƙatar hakan ta taso.
Tinubu ya bai wa tawagar Flamingos da suka lashe kofin duniya kyautar miliyan 100 kowacce
Asalin hoton, Presidency NG/X
Shugaba Bola Tinubu ya bai wa kowace daga cikin tawagar mata ta Najeriya yan kasa da shekara 17 da ake wa lakabi da Flamingos da suka lashe gasar kofin duniya, kyautar kuɗi naira miliyan 100.
Uwargidan shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta sanar da bayar da kyaututtukan a wani taro da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
An kuma ware naira miliyan 100 ga babban mai horar da ƙungiyar, yayin da kowane mamba na tawagar masu horarwa da sauran ma’aikatan za su karɓi naira miliyan 50.
Sanata Oluremi ta yaba wa ƙungiyar kan nasarar da ta samu ta hanyar lashe wasanni shida a jere, tare da nuna ladabi da girmamawa bayan kammala wasan ƙarshe.
Ta ce wannan nasara za ta zama abin ƙarfafawa ga matasa mata, tare da nuna musu cewa za su iya cimma burinsu har a matakin duniya.
Har ila yau, ta yaba wa masu horar da ƙungiyar da kuma magoya baya saboda gudunmawar da suka bayar wajen samun wannan nasara.
Ƙungiyar Flamingos ta lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 karo na farko a tarihi bayan ta doke Japan 2-1 a wasan ƙarshe da aka buga ranar 7 ga Nuwamba.
An samu barazanar boma-bomai a makarantun Italiya
Ministan Ilimin Italiya ya ce an kwashe ɗalibai da ma’aikata daga aƙalla makarantu 300 a faɗin ƙasar bayan sun karɓi saƙon barazanar tashin bam iri ɗaya.
Yan sanda a Scotland, a Arewacin Ireland, da Jamhuriyar Ireland sun ce an aikewa makarantu a yankunansu irin wannan barazana.
Sai dai hukumomin sun ba da shawarar cewa a ɗauke su a matsayin saƙonnin ƙarya, tare da cewa babu buƙatar kwashe mutane daga makarantu.
Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta bayyana cewa gargaɗin bam ɗin bai haifar da wata barazana ga jama’a ba.
Sakon imel ɗin da aka aika wa makarantun Italiya an sanya masa hannu da sunan bogi na wani dan Rasha Mikha'il Andro-pov.
An kuma ga irin wannan suna a wasu barazanar baya-bayan nan da aka aika wa jiragen sama a sassan Turai, da kafafen yaɗa labarai a Ireland da Bulgaria.
Ana fargabar kisan mutum 11 sakamakon wani hari a Pakistan
Wata ƙungiyar agajin gaggawa a Pakistan ta ce ana fargabar cewa aƙalla jami’an ƴan sanda 11 ne suka mutu a wani hari da aka kai musu a yankin Kohat na lardin Khyber Pakhtunkhwa.
Jami’an tsaro na gudanar da wani samame ne kan wuraren haƙo zinari ba bisa ƙa’ida ba a yankin, lokacin da wasu ƴan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba suka kai musu hari.
An kuma jikkata jami’an tsaro da dama a arangamar.
Har zuwa yanzu, babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, amma ƙungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) da sauran mayakan masu iƙirarin jihadi sun sha kai irin waɗannan hare-hare kan jami’an tsaron Pakistan a baya.
Ba za mu bari a ɗauki ko da ƙwayar zarra na uranium ɗinmu ba - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Mohsen Rezaei, sakataren tsaron ƙasar Iran, ya ce ƙasar ba za ta amince ko da “ƙwaya guda” na sinadarin uranium da ta inganta ya fita daga ƙasar ba.
A wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Al-Mayadeen da ke Lebanon, Rezaei ya ce Iran ta kuma sanar da Rasha cewa za ta ci gaba da ajiye sinadaran uranium ɗinta da aka inganta a cikin ƙasar, kuma za ta yi amfani da su.
Ya bayyana cewa Iran na buƙatar waɗannan sinadarai domin ƙera jiragen ruwa da kuma jiragen ruwa masu nutsewa a ƙarƙashin teku (submarines) waɗanda ke amfani da makamashin nukiliya.
Tun da farko, Rasha ta gabatar da shawarar cewa za a iya kai uranium ɗin Iran da aka tace zuwa ƙasarta a matsayin wani ɓangare na yiwuwar yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da Amurka, amma ta ce Tehran ce za ta yanke hukunci a kan hakan.
Kalaman Mohsen Rezaei sun zo ne a daidai lokacin da shirin nukiliyar Iran ke ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Tehran da Washington, yayin ƙoƙarin da ake yi na kawo ƙarshen yaƙin da ke addabar yankin.
Wakilan Amurka sun ce tattaunawar Rasha da Ukraine ta yi armashi
Wakilin shugaban Amurka na musamman, Jared Kushner, ya ce tattaunawar da aka kammala tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Abu Dhabi ta ƙunshi muhimman batutuwa.
Mista Kushner ya kuma ce a wasu lokutan tattaunawar ta kasance mai tsauri, bayan shafe watanni ana fama da rashin wata hulɗa tsakanin ɓangarorin biyu.
Ya ce an tattauna dukkan batutuwan da suka shafi rikicin, kuma an samu kyakkyawar musayar ra'ayoyi tsakanin bangarorin.
Mista Kushner ya kuma bayyana cewa shi da takwaransa wakilin Amurka, Steve Witkoff, za su tashi zuwa Moscow ranar Alhamis domin ganawa da Shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Ya zuwa yanzu, babban abin da aka bayyana a fili a matsayin nasarar tattaunawar shi ne yarjejeniyar musayar fursunoni mai yawa tsakanin ɓangarorin biyu.
Ana sa ran za a ci gaba da tattaunawa a ranar Alhamis domin fayyace cikakkun bayanai kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar musayar fursunonin.
DR Kongo ta amince gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar
Shugaban ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango (DR Congo), Félix Tshisekedi, ya amince da wata sabuwar doka da ta bayar da damar yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin ƙasar.
An tabbatar da matakin ne ta cikin wata sanarwar gwamnati da aka karanta a gidan talabijin na ƙasa ranar Laraba.
Jam'iyyun adawa dai sun shafe watanni suna gudanar da zanga-zanga kan sauye-sauyen da ake son yi wa kundin tsarin mulkin.
Suna zargin cewa sabbin sauye-sauyen na iya bai wa Mista Tshisekedi damar ci gaba da mulki wa'adi na uku idan wa'adinsa na yanzu ya ƙare a shekarar 2028.
An kama matar da ta kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗi a wajen ƙaninta
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan Jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya ta kama wata mata mai shekara 54 bisa zargin kitsa sace kanta domin karɓar kuɗin fansar naira miliyan 15 daga wajen ƙaninta.
Rahotanni sun ce matar ta yi ikirarin cewa wasu mutane sun yi garkuwa da ita tare da kaita cikin daji, inda suka nemi a biya su naira miliyan 15 domin sako ta.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar ne ya bayyana hakan a cikin wani bidiyo da aka nuna matar tana amsa laifin da ake zarginta da aikatawa.
Mai magana da yawun rundunar ya ce an kai rahoton lamarin hedkwatar 'yan sanda ta Ogwashi-Uku ranar 23 ga Oktoban 2026, lamarin da ya sa Kwamishinan ƴansanda ya umarci sashen yaƙi da garkuwa da mutane da ke Obu-Luku a ƙaramar hukumar Aniocha ta Kudu ya gudanar da bincike.
Ya ce jami'an sashen sun gudanar da binciken sirri wanda ya gano yadda aka shirya lamarin, tare da kai ga cafke matar.
A cikin bayanin da ta bayar a bidiyon, matar ta amince ita ce ta shirya sace kanta tare da neman ƙaninta ta tura mata kuɗin fansar.
"Ni na kitsa komai. Na kira ƙanina na sanar da shi cewa an yi garkuwa da ni lokacin da na fita sayen magani, kuma an kai ni cikin daji'', in ji matar.
Ta ce ta faɗa masa cewa suna neman naira miliyan 15, kuma idan bai biya kuɗin ba za su kashe ta.
''Aikin shaidan ne. Ina neman afuwa. Aikin shaidan ne."
Rundunar ƴansandan jihar ta ce za ta gurfanar da matar a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
An naɗa Seyi Tinubu sarautar Ɗan Zakin Gwandu
Asalin hoton, City Boy Movement/X
Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Ilyasu Bashar ya naɗa ɗan gidan shugaban Najeriya, Seyi Tinubu matsayin sarautar Dan Zakin Gwandu.
Asalin hoton, Seyi Tinubu News/FB
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar siyasar Seyi ta City Boy Movement ta wallafa a shafinta na X ta ce an ɗana shi sarautar ne sakamakon gudunmowar da yake bayarwa wajen haɗa kan mutane.
Asalin hoton, Seyi Tinubu News/FB
An gudanar da bikin naɗin ne a fadar sarkin da ke Gwandu a ranar Talata.
Taron naɗin ya samu halartar jama'a ƴansiyasa da ƴan ƙungiyar ta City Boy.
Asalin hoton, Seyi Tinubu
'Wani jirgin ruwa ya kama da wuta a mashigar Hormuz bayan taka nakiya'
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojojin ruwan Iran ta sanar cewa wani jirgin dakon man fetur ya kama da wuta a gabashin mashigar Hormuz da safiyar yau Laraba bayan ya taka wata nakiya da aka dasa a cikin ruwa.
A cikin wata sanarwa da sashen hulɗa da jama'a na rundunar ya fitar, ya bayyana jirgin a matsayin "mai karya doka", tare da cewa ya taka nakiyar ne a wani yanki da aka haramta zirga-zirga kuma maras aminci.
Rundunar ta sake jaddada gargaɗin cewa jiragen ruwa na iya samun tsallakewa cikin aminci ta mashigar Hormuz ne kawai idan sun yi aiki tare da rundunonin sojin Iran tare da bin dokokin zirga-zirgar teku.
Tun da farko, Cibiyar Kula da Harkokin Kasuwancin Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce ta samu rahoton wani "abu mai tayar da zargi" da ya shafi wani jirgin dakon mai a mashigar Hormuz, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Har yanzu ba a tabbatar ko rahoton da cibiyar ta Birtaniya ta fitar da kuma sanarwar sojojin Iran na magana ne kan jirgi guda ɗaya ko kuwa wasu al'amura biyu ne daban.
Sanarwar sojojin Iran ɗin ba ta bayyana sunan jirgin ko ƙasar da ta mallake shi ba, haka kuma ba ta yi bayani kan halin da ma'aikatansa ke ciki ko irin girman ɓarnar da lamarin ya haifar ba.
Yadda a baya ban yi APC ba yanzu ma ba zan yi ba - Lamido
Asalin hoton, Mansur Ahmed/FB
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP, Alhaji Sule Lamido ya nesanta kansa da kalaman da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi a kansa.
A lokacin da yake jawabi a taron yaƙin neman zaɓe a Dutse, babban birnin jihar Jigawa a ranar Talata, Kashim Shettima ya Sule Lamido na tare da APC.
''Wai in ana magar Jigawa, su wane ne Jigawa?, ga mu nan muna tare da Saminu Turaki da Ali Sa'adu Birnin Kudu da Muhammad Badaru Abubakar, dukkansu tsoffin gwamnonin jihar, kai har Alhaji Sule Lamido yana tare da mu'', in ji Shettima.
Kalaman sun haifar da cece-ku-ce tsakanin ƴansiyasar ƙasar, inda wasu suka fara zargin cewa Sule Lamidon na yi wa APC aiki ne.
Sai dai jim kaɗan bayan kalaman mataimakin shugaban ƙasar, Sule Lamido ya barranta kansa da kalaman.
Cikin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai da DC Hausa, Lamido ya ce ba abin da zai sa a yanzu ya yi APC.
''Yadda a baya ban yi APC ba, duk da kiraye-kirayen da manyan jam'iyyar suka yi min, ai yanzu ba babu wani dalilin da zai sa na yi APC''.
Lamido ya kuma danganta kalaman na Shettima da wasan barkwancin da ke tsakanin al'umomin Fulani da Kanuri.
Birtaniya ta tsare wani babban sojan Amurka kan zargin laifi
Asalin hoton, Getty Images
Jami’an ƴan sanda a Birtaniya sun tsare wani babban jami’in sojin Amurka a wani ofishin ƴan sanda na London, bayan kama shi bisa zargin yi wa Rasha leƙen asiri.
Mutumin mai shekaru 41, ya shiga hannu ne a wani samame da jami’an yaƙi da ta’addanci suka gudanar tare da haɗin gwiwar rundunar sojin Amurka da kuma Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka (FBI).
Rahotanni sun ce ana kyautata zaton yana aiki ne a wani sansanin soji wanda shi ne hedikwatar rundunar tsaro ta ƙungiyar tsaro ta NATO.
A halin yanzu, ƴan sandan Birtaniya na ci gaba da bincike a wurare biyu da ke kusa da sansanin.
Daraktan hukumar FBI, Kash Patel, ya ce irin waɗannan zarge-zargen leƙen asiri “na daga cikin batutuwan da suka fi tayar da hankali ga Amurka da ƙawayenta.”
Amurka ta gurfanar da wasu mutane kan zargin yi wa Iran aiki
Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta sanar da gurfanar da wasu mutum uku da take zargi da yi wa Iran aiki.
Daga cikin zarge-zargen akwai hannu a wani shiri da ake zargin an kitsa domin kai hari kan sansanin sojojin saman Birtaniya na inda aka ajiye dakarun Amurka, a watan Satumba.
Ana zargin ɗaya daga cikin mutanen, wanda ɗan asalin ƙasar Iran da kuma Iraƙi ne, da tuntuɓar wasu abokan hulɗarsa a Birtaniya daga wani gidan yari a birnin New York.
Sauran mutanen biyun kuma ana zarginsu da gudanar da irin wannan hulɗa daga cikin Iran.
Lamarin shirin kai harin kan sansanin ya fito fili ne bayan da aka ga wasu motoci a kusa da sansanin, lamarin da ya janyo hankalin jami’an tsaro.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin ci gaba da kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.