Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC, ta rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric, sakamakon matsalar kuɗi da kuma gazawar kamfanin wajen cika wasu muhimman sharuɗɗa.
NERC ta ce matakin ya fara aiki daga ranar 10 ga Agustan 2026, bisa tanade-tanaden sashe na 75 zuwa 79 na Dokar Wutar Lantarki ta shekarar 2023.
Hukumar ta ce kamfanin ya tara bashin sama da naira biliyan 118.6 na wutar lantarki a watan Mayun 2026, lamarin da ya sa jimillar bashin da ke kansa ya kai kusan naira biliyan 456.5.
NERC ta kuma ce a shekarar 2025, Kaduna Electric ya biya kashi 41.93 cikin 100 kacal na kuɗaɗen da aka yi masa ƙiyasin biya.
A cewar hukumar, kamfanin ya kuma yi asarar wutar da ake samu da rarrabawa da kuma karɓar kuɗinta, da ta kai kashi 71.88.
Haka kuma, NERC ta ce kamfanin ya kashe naira biliyan 2.48 kacal ne wajen inganta ayyukansa, duk da cewa abin da ake buƙata ya kai naira biliyan 24.51.
Hukumar ta ƙara da cewa ƙasa da kashi 36 cikin 100 na kwastomomin kamfanin ne kawai ke da mitocin lantarki.
Domin tabbatar da cewa ba a samu tangarda wajen samar da wutar lantarki ga al'ummar yankin ba, NERC ta ce ta kafa wani kwamitin wucin gadi na musamman da zai kula da gudanar da kamfanin.
An naɗa Dakta Abdullahi Garba a matsayin shugaban kwamitin, yayin da aka naɗa Dakta Abubakar Umar Hashidu a matsayin mai kula da harkokin kamfanin na tsawon watanni shida.
NERC ta kuma ce Afrexim za ta jagoranci wani shiri na tsawon watanni 12 domin nemo sabbin masu zuba jari da zai maye gurbin babban mai hannun jarin kamfanin.