Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannans ahfi na kawo muhimman al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 02/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labari da rahotonni da muke kawo muku.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku wasu sabbin labaran.

    Mu kwana lafiya.

  2. Kotun Malta ta wanke wani ɗan kasuwa daga zargin kisan fitacciyar ƴarjaridar ƙasar

    Wata kotu a Malta ta wanke wani fitaccen ɗan kasuwa daga dukkan zarge-zargen cewa shi ne ya shirya kisan fitacciyar ƴar jarida mai binciken ƙwa-ƙwaf ta tsibirin a shekarar 2017.

    Daphne Caru-ana Galizia na gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka shafi harkokin kasuwancin Yorgen Fenech lokacin da wata bam ta fashe a ƙarƙashin motarta.

    An yanke wa wasu abokan hulɗar Mista Fenech hukunci bayan samunsu da laifin aiwatar da harin, amma masu taimaka wa alƙali a babban birnin ƙasar, Valletta, sun wanke Mista Fenech daga zargin haɗa baki domin kashe Caruana Galizia da kuma hannu a kisanta.

    Hukuncin ya sa dangin attajirin farin ciki, yayin da iyalan Caruana Galizia suka fashe da kuka.

  3. Trump ya ce yana farin cikin ficewar Yarima Harry da matarsa daga Amurka

    Yarima Harry da mai ɗakinsa

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana farin ciki yadda Yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan suka yanke shawarar barin Amurka suka koma Birtaniya.

    Mista Trump ya zargi ma'auratan da nuna babban rashin girmamawa ga gidan sarautar Birtaniya.

    An daɗe ana ganin saɓani a bainar jama'a tsakanin Duke da Duchess na Sussex da Mista Trump, inda abokan siyasar shugaban Amurkan ke bayyana komawarsu Birtaniya a matsayin wata nasara ta siyasa ga Fadar White House.

    Tun da farko, wani fitaccen ɗan wasan kwaikwayo kuma daraktan fina-finai, George Clooney, ya yi kakkausar suka ga Mista Trump.

    Clooney ya bayyana gwamnatin Trump a matsayin "gwamnatin da mutanen da ba su cancanta ba suka mamayeta."

  4. 'Ba za mu ce komai ba' kan zargin hannu a boren sojojin Nijar - Faransa

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Faransa Emmanuel Macron

    Faransa ta ƙi yin tsokaci kan zarge-zargen da ke cewa ta shirya tallafa wa wani yunƙurin tawaye da ya auku a wani sansanin soji da ke Yamai, babban birnin Nijar, a ƙarshen makon da ya gabata.

    Ofishin Hulɗa da Kafafen Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Faransa ya shaida wa BBC cewa, "ba zai yi tsokaci kan kalaman Kyaftin Roger Gabriel ba, ko kuma sahihancin majiyoyinsa."

    Kyaftin Gabriel, wanda jami'i ne a rundunar sojin Nijar, ya yi waɗannan zarge-zarge ne a gidan talabijin na gwamnati ranar Litinin yayin da yake bayani kan abubuwan da suka faru a Sansani na 101, inda aka ji ƙarar harbe-harbe masu yawa a lokacin da gwamnati ta ce an yi yunƙurin bore.

    Ya ce ya samu saƙonni da kuma kiraye-kirayen waya da ke nuna cewa wasu sojojin ƙasashen waje na shirin taimaka wa waɗanda suka ƙwace ikon sansanin.

    Har ila yau, ya yi zargin cewa wasu mutane masu alaƙa da hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, sun bayyana cewa ƙawayen ƙasashen waje a shirye suke su tsoma baki, tare da nuni da cewa Faransa da wasu ƙasashen yankin na iya kasancewa cikin lamarin.

    Sai dai babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge.

    Faransa ta shaida wa BBC cewa duk lokacin da take tura sojojinta zuwa wata ƙasa, tana yin hakan ne tare da haɗin gwiwar ƙasashen da abin ya shafa kuma cikin mutunta kon mallakar ƙasashensu.

    "Lokacin da aka tura rundunar sojin Faransa zuwa ƙasashen waje, ana yin hakan ne cikin haɗin kai da abokan hulɗarmu tare da mutunta cikakken ikon ƙasashen," in ji shi.

    Wannan zargi na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Nijar da Faransa ke cikin wani yanayi na tsami.

    Dangantakar ta muni matuƙa bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023, wanda ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

    Daga baya mahukuntan sojin Nijar suka umarci sojojin Faransa da jakadan ƙasar su fice daga Nijar, lamarin da ya kawo ƙarshen doguwar haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

    Tun daga lokacin Nijar ta ƙara kusantar Rasha tare da maƙwabtanta Mali da Burkina Faso.

    Ƙasashen uku masu mulkin soja sun kafa Ƙawancen Tsaron Ƙasashen Sahel (AES), tare da nesanta kansu daga Faransa da kuma ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS.

    Wannan sauyi ya kuma rage tasirin siyasa da na soji da Faransa ke da shi a yankin Sahel.

  5. Amurka da Venezuela sun cimma yarjejeniyar haƙo man fetur a Venezuela

    Amurka da Venezuela sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta bai wa wani kamfani da Amurka ke jagoranta damar aiki a wasu sarrafa rijiyoyin man fetur na Venezuela da suka kai kusan kashi ɗaya cikin biyar na arzikin man ƙasar.

    Sakataren Makamashi na Amurka, Chris Wright, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata rana ta tarihi wadda za ta kawo sauyi mai girma ga zaman lafiya da wadatar ga al'ummar Venezuela.

    Ya ce yana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wa Venezuela wajen ninka yawan man da take haƙowa cikin shekaru goma masu zuwa.

    Sai dai masu sukar yarjejeniyar sun ce matakin tamkar sayar da arzikin ƙasa ne ga ƙasashen waje a wani salo irin na mulkin mallaka.

  6. Iran ta aike wa Amurka sabon gargaɗi

    Mohsen Rezaei

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta aike wa Amurka sabon gargaɗi game da rikicin baya-bayan nan da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, sakataren majalisar tsaron ƙasar, Mohsen Rezaei ya ce yun ƙurin da Amurkan ke yi ba zai taimaka mata ba.

    "Wannan yunƙurin da kuke yi cikin matsananciyar damuwa ba za su taimaka muku ku kuɓuta daga cikin wutar da kuka hura wa kanku ba. Nan gaba kaɗan za ku ga yadda sabuwar dabarar Iran a fagen yaƙi, diflomasiyya da kuma tinkarar wareta daga duniya za ta rusa tushen ƙarfinku."

    Kalaman na Rezaei sun zo ne bayan mafi munin musayar hare-hare tsakanin ɓangarorin biyu a cikin makonnin baya-bayan nan.

    A hare-haren da aka kai kwanan nan, dakarun Amurka sun kai farmaki kan wurare da ke gaɓar mashigar Hormuz da kuma gabashinsa, baya ga wasu yankuna a yammacin Iran da kudu maso yammaci da kuma kudancin ƙasar.

    Ɗaya daga cikin hare-haren ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu tare da jikkata wasu 68 a wani bikin aure da aka gudanar a birnin Kohstak da ke lardin Hormuz.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana harin a matsayin "laifin yaƙi."

    Iran ta ce ta mayar da martani ne ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a faɗin yankin, ciki har da waɗanda ke Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Kuwait da Bahrain, da kuma Erbil, babban birnin yankin Kurdawa mai cin gashin kansa a Iraƙi.

  7. Me Trump ya cimma watanni shida bayan fara yaƙin Iran?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Watanni shida kenan da fara yaƙin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan Iran, rikicin da shugaban Amurka Donald Trump ya taɓa hasashen zai ɗauki makonni huɗu zuwa biyar kacal.

    Sai dai yanzu yaƙin ya shafe kusan makonni 27 yana gudana, ba tare da wata alamar kawo ƙarshensa ba.

    Duk da hare-haren da aka kai da kuma matsin lambar da aka yi wa Tehran, har yanzu Iran na ci gaba da nuna ƙarfi da jajircewa.

    Hakan ya sa masu sa ido ke tambayar ko manufofin da Trump ya sanya a gaba sun samu nasara, kasancewar rikicin ya daɗe fiye da yadda aka yi zato tun farko.

    Yayin da yaƙin ke shiga wata na shida, ana ci gaba da fuskantar tambayoyi kan irin nasarorin da Amurka ta samu da kuma farashin siyasa da tattalin arziƙi da rikicin ya haddasa.

    Duk da cewa Trump ya nace kan ci gaba da yaƙin, har yanzu ba a ga ƙarshen rikicin ko wata mafita ta diflomasiyya a sarari ba.

  8. Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da UAE

    jirage

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Iran sun ce sun kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

    Cikin wata sanarwa da sojojin Iran suka fitar, "jirgagen yaƙi marasa matuƙa da dama sun kai hari kan na'urorin rada da wuraren da sojojin Amurka suke a sansanonin Al-Dhafra da Al-Manhad da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa."

    Sanarwar ta kuma ce jiragen marasa matuƙa kirar Arash sun sake kai hare-hare kan tashoshin rada da kuma wuraren da sojojin Amurka suka taru a sansanin Sheikh Issa da ke Bahrain.

    Iran ta ce ta kai waɗannan hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren sama da Amurka ta kai a baya-bayan nan.

    Sa'o'i kaɗan kafin hakan, rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ita ma ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Kuwait da Jordan.

    A nata ɓangare rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta ce ta kammala hare-haren sama kan wuraren da ke ƙarƙashin iko rundunar juyin juya halin ta Iran, ciki har da na'urorin kariyar sararin samaniya da tashoshin rada, kayan aikin ruwa da cibiyoyin sadarwa.

    Amurka ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin martani ga yunƙurin kai hari kan jiragen ruwa na kasuwanci da ke ratsa mashigin ruwa na Hormuz, da kuma kan dakarunta da ke yankin.

    Iran ta ce hare-haren na Amurka sun yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar fararen hula, ciki har da wasu da ke halartar wani bikin aure.

  9. Uber ya dakatar da ayyukansa a Najeriya

    Uber

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin samar da motocin haya ta manhaja, Uber, ya sanar da dakatar da ayyukansa a Najeriya da Uganda daga ranar Laraba 2 ga Satumban 2026, bayan shafe fiye da shekara goma yana aiki a Najeriya.

    Kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne bayan nazarin abubuwan da ya sa a gaba a harkokin kasuwanci da kuma dabarunsa na zuba jari.

    A cikin wata sanarwa da Uber ya aikewa BBC, kamfanin ya ce bayan yin cikakken nazari, ''mun ɗauki wannan mataki mai wahala na kawo ƙarshen ayyukanmu a Najeriya da Uganda, daga ranar 2 ga Satumban 2026. Wannan mataki ya shafi waɗannan ƙasashe biyu kaɗai, kuma ba zai yi tasiri ga ayyukanmu a sauran ƙasashen Afirka ba."

    Ƴan Najeriya da dama musamman ma'aikata da masu ziyara a ƙasar kan yi amfani da manhajar wajen kiran motocin haya domin kai su wuraren da suke so, a kowane lokaci.

    Kamfanin ya ce zai ɗauki matakan tallafa wa direbobin da ke aiki da kamfanin domin rage musu raadin da matakin zai haifar musu a lokacin wannan sauyi.

    A shekarun baya direbobin da ke aiki da kamfanin sun gudanar da zanga-zanga, sakamakon tashin farashin man fetur da ƙarin kuɗaɗen gudanar da aiki, da ƙarancin kuɗin haya da suke samu, da kuma abin da suka bayyana a matsayin rashin kyawun yanayin aiki.

    Uber ya ce matakin dakatar da aikin ya taƙaita ne ga Najeriya da Uganda kawai, kuma ba zai shafi ayyukansa a sauran ƙasashen Afirka ba.

    Sai dai sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu haka Uber na ƙoƙarin inganta harkokinsa a yankin Afirka, Kudu da Hamadar Sahara, inda ya ce yana ci gaba da bunƙasa kasuwancinsa.

    Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin masu amfani da manhajar Uber a Najeriya tuni suka saƙonnin imel da ke sanar da su game da rufe ayyukan kamfanin.

    Kamfanin ya kuma ce cibiyar taimakonsa ga abokan hulɗa za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 24 ga Satumba, domin amsa tambayoyi da kuma magance batutuwan da suka shafi dakatar da ayyukan.

    Uber ta ce cibiyar hulɗa da kwastomominta za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 24 ga Satumba, domin amsa tambayoyi da kuma magance matsalolin da ka iya tasowa sakamakon dakatar da ayyukanta.

  10. Muna fatan Iran da Amurka za su koma teburin Sulhu - Pakistan

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce har yanzu tana da fatan cewa Iran da Amurka za su koma teburin tattaunawa domin warware matsalolinsu.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana cewa ziyarar da Field Marshal Asim Munir, shugaban rundunar sojin Pakistan, ya kai Tehran, ta haifar da gagarumin ci gaba wajen buɗe ko ciyar da batun mashigin Hormuz gaba.

    Pakistan ce take taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.

    Sai dai duka Iran da Amurka sun bayyana cewa an karya wannan yarjejeniya, kuma ba sa ci gaba da bin tanade-tanadenta.

    Iran ta sanar da cewa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar Islamabad idan har Amurka ta koma aiwatar da nata ɓangaren yarjejeniyar.

  11. Cutar diphtheria ta ɓulla a Filato, Katsina da Kano

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Cutar Mashaƙo na ci gaba da yaɗuwa a wasu sassan jihohin Filato, Katsina da Kano, inda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da janyo rashin lafiya ga wasu dayawa.

    A Jihar Filato kaɗai, aƙalla mutum 23 sun mutu yayin da ake zargin mutane 143 sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi daban-daban, musamman a Jos ta Arewa.

    Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Nicholas Baamlong, ya ce yawancin mace-macen sun faru ne cikin makonni uku da suka gabata, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.

    Ya bayyana cewa wasu marasa lafiya tara na karɓar magani a cibiyoyin killace masu ɗauke da cutar, inda ya ce ƙarancin maganin cutar antitoxin da kuma jinkirin kai marasa lafiya asibiti na daga cikin manyan ƙalubalen yaƙi da cutar.

    Hukumomi sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kai tare da neman tallafi daga Hukumar NCDC domin samar da magunguna da kayan gwajin cutar.

  12. Red Crescent ta Iran ta kai ƙarar harin da Amurka gaban ICC

    Hukumar ba da agajin gaggawa ta Iran (IRCS) ta rubutawa Kotun Hukunta Manyan Laifuks ta Duniya da ke Hague wata wasiƙa inda ta kai ƙarar Amurka kan harin da ta kai wani taron ɗaurin aure a Kudancin Iran.

    A cikin wasiƙar Red Crescent ta ce mutane huɗu sun mutu ciki har da wani yaro guda, kuma sun mutu ne dalilin harin da Amurkan ta kai. An kuma rawaito cewa mutum 67 sun jikkata.

    Hukumar ta ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 21:30 na safe a ranar Talata, lokacin da ake gudanar da bikin auren a garin Kuhestak da ke yankin Sirik.

    "Idan aka la'akari da mummunan halin da wadanda suka jikkata ke ciki, za a iya samun ƙarin waɗanda suka mutu a nan gaba," kamar yadda sanarwar da aka watsa a Telegram ta bayyana. Auren dai na fararen hula ne.

  13. Ya kamata ƴan APC su tausasa harshensu lokacin kamfe - Kawu Sumaila

    ..

    Asalin hoton, BBC/GRAB

    Sakamakon yadda sauye-sauyen da gwamnatin hugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ta jam'iyyar APC ta kawo a kasar wadanda wasu ke gani sun haifar da wahalahalu na tsanani na rayuwa, wani jigo a jam'iyyar kuma dan majalisar dattawa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya shawarci ƴan jam'iyyar su yi amfani da kalamai na sanin ya kamata da mutuntawa da kuma tausasa harshe wajen yakin neman zaɓen 2027.

    Sanatan ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya yi da BBC, yana mai nuni da cewa yadda yan kasar suka fusata da halin tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa to sai an bi su da kalamai na shawo kai.

    Danmajalisar Dattawan ya ce ya mika wa kwamitin yakin neman sake zaben Shugaba Tinubu wasu jerin shawarwari da suka shafi rayuwar 'yan Najeriya, wadanda ya ce ya 'yan kwamitin ya kamata su yi amfani da su a aikinsu na kamfe.

    Ya yi karin bayani da cewa: ''Na yi kira ga shi Abdul'aziz Abubakar Yari da 'yan kwamitinsa da mu da muka shiga zabe cewa mu gaya wa kanmu gaskiya, mu kalli halin da Najeriya take ciki.''

    ''Akwai abubuwa guda uku kwarara wadanda dole maganganunmu sai sun nuna a jikinmu mun san wani abin yana faruwa,'' in ji shi.

    Ya ce, ''Akwai kalubale na tsaro wanda mutane suna rasa rayuwarsu kuma wasu suna cikin wani yanayi na rashin jin dadi na barin garuruwansu, akwai abin tausayawa. Ga zama a cikin tsoro a bangarori da dama a karkashin jagorancinmu.''

    To amma kuma Kawu Sumailan ya kara jaddada irin zargin da ake yi a kan wasu daga cikin 'yan kwamitin yakin neman zaben Shugaba Tinubun na cewa wasunsu da dama suna da kashi a gindinsu, duka da cewa 'yan jam'iyyarsa ne ta APC, inda ya ce:

    ''Gaskiyar magana da yawa daga cikin mambobin wannan kwamitin su ne matsalar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da APC.''

    ''Yan jam'iyyarmu amma kowa zai amsa sunan ubansa. Kowa yana komawa gida a zabo shi ya taho.''

    Ya ce,'' Kuma dukkan irin wadannan abubuwa mun fada a zaman sirri, mun fada a zaman fili, sannan mun fada wajen 'yan jaridu.''

    ''Na duba na ga yawan wadanda suke cikin wannan kwamiti sun taimaka kwarai da gaske wajen tsunduma gwamnatin APC da tsunduma gwamnatin Tinubu cikin matsalar da ake kallonta da shi.''

    Sanatan mai wakilitar mazabar Kano ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya yi karin haske da cewa muhimmin aiki da kuma kasancewar gwamnati na farko shi ne ta tabbatar da tsaron rayuwa da mutunci da dukiyar al'ummarta, daga nan kuma sai samar da abubuwa na more rayuwa su biyo baya.

    Dangane da hakan ya nuna lalle akwai gazawar gwamnati a wannan bangare na sauke nauyin da ke kan gwamnati a kan al'ummarta.

    Ya ce: ''To mutane ba za su gamsu ba matukar ba su ga ko'ina an zauna lafiya ba.Matukar ba su yaba a zahiri sun fito sun ga kokarin da muke yi ba. To duk kokarin da muke yi ya kamata mu tausaya a irin maganganunmu.''

    Kawu ya kwatanta shugabanci da yadda likita yake yi wa maras lafiya magani, da cewa likita yana kokarin yi mawa mutum magani yana tausaya masa amma kuma alokaci guda yana yi masa abin da ke sa mutumin ya ji zafi domin ta hakan ne zai samu lafiya.

    Ganin cewa Sanatan yana daya daga cikin fitattun 'yan jam'iyyar APC daga Kano wanda kuma ya tsaya takarar sake neman kujerar sanatan da yake kai, ya fito yana nuna cewa lalle akwai matsalar a yadda jam'iyyar za ta tunkari al'ummar Najeriya kan su sake zabenta a 2027 sai ya ce:

    ''Babu wani abu ai magana ce ta mu gaya wa kanmu gaskiya kuma duk wanda yake bin maganganu na haka ne dole za ka fade su da dadi ba dadi. In ma an ki maganar da muka fada daga baya za a zo a yarda da ita.''

    Dangane da yadda 'yan adawa ke ganin APC din ba ta abin da yza ta yi wa 'yan kasar yakin neman zabe da su, sai Kawu Sumaila ya ce:

    ''Daga daya zuwa goma zan iya lissafa maka 'yan'adawa da suka yi wa Najeriya illar da APC ba ta yi mata ba , kuma idan aka fito da ita tashin hankali ne. Su su ma dawo su shiga zabe abin kunya ne don ba irin karyar da ba su yi wa 'yan Najeriya ba.''

    Sanata Kawu ya ce shi dai rokon da zai yi shi ne musamman 'ga Arewacin Najeriya shi ne jama'a su daina duba cewa sai gwamnati ko dan APC ko jami'an tsaro ne za su yi, kowa ya bayar da gudummawarsa a ceto yankin daga halin da yake ciki.

  14. Tankokin mai biyu sun tarwatse bayan taka nakiyoyi a mashigar Hormuz - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce tankokin mai guda biyu sun tarwatse tare da kama da wuta bayan sun taka nakiyoyin ruwa a Mashigar Hormuz.

    A cikin wata sanarwa, IRGC ta zargi sojojin Amurka da karkatar da jiragen zuwa wata hanya da ta bayyana a matsayin haramtacciya, inda ta ce jiragen sun faɗa hannun jami'an Amurka bayan an sauke ma'aikatansu.

    Rundunar ta ce a baya ta yi gargaɗi kan haɗarin amfani da wata mashiga da aka dasa nakiyoyi a cikinta, tare da yin barazanar hukunta kamfanonin jiragen ruwa da ba su bi hanyar da ta amince da ita ba.

    An ce tankokin biyu na ci gaba da ƙonewa bayan aukuwar lamarin.

  15. Hare-haren Iran: Amurka ta buƙaci ƴan ƙasarta a Gabas ta Tsakiya su yi taka-tsantsan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke zaune ko tafiya a ƙasashen Gabas ta Tsakiya su ƙara yin taka-tsantsan saboda fargabar hare-haren Iran da ƙarin tashe-tashen hankula da ka iya biyo bayan rikicin da ke ƙara tsananta a yankin.

    Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abu Dhabi da kuma Ofishin Jakadancin Amurka na Dubai sun yi gargaɗin yiwuwar samun abubuwan da ba a yi tsammani ba, inda suka shawarci Amurkawa su kasance cikin shiri saboda yiwuwar soke jirage, rufe sararin samaniya da kuma wasu matsalolin tafiye-tafiye.

    Sanarwar ta kuma tunatar da cewa cibiyoyin diflomasiyyar Amurka sun taɓa zama abin hari a Gabas ta Tsakiya da wasu sassan duniya a baya.

    Haka kuma ta yi gargaɗin cewa Iran da ƙungiyoyin da ke mara mata baya na iya kai hare-hare kan wasu muradun Amurka a ƙasashen ƙetare, ciki har da kamfanoni da cibiyoyin da ke da alaƙa da Amurka.

  16. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 252 a Najeriya — NCDC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Cibiyar daƙile cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar zazzaɓin Lassa ya kai 252 a bana, yayin da adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya kai 1,035.

    NCDC ta ce an samu sabbin mutum 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar tsakanin 10 zuwa 16 ga watan Agusta a jihohin Ondo, Bauchi, Edo da Benue.

    Hukumar ta ƙara da cewa yawan mace-macen ya sa adadin masu mutuwa daga cutar ya kai kashi 24.4 cikin 100, wanda ya fi na shekarar 2025 da ya tsaya a kashi 18.6 cikin 100.

    A cewar NCDC, jihohi 23 sun riga sun samu aƙalla mutum ɗaya da aka tabbatar ya kamu da cutar a ƙananan hukumomi 117, kuma hukumar na ci gaba da sa ido da ɗaukar matakan daƙile yaɗuwar cutar.

  17. Iran ta gargaɗi ƙasashe kan haɗin gwiwa da Amurka wajen kai mata hari

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedikwatar Khatam al-Anbiya ta Iran ta gargadi ƙasashen yankin da ke haɗin gwiwa da sojojin Amurka wajen kai mata hari tana cewa su sa ran fuskantar mummunan sakamako.

    Gargadin ya zo ne bayan hare-haren da Amurka ta kai wasu yankunan kudancin Iran a daren Talata.

    Iran ta ce dakarunta sun mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin Amurka da ke Jordan, Bahrain da Erbil na Iraqi.

    Hedikwatar ta kuma yi gargaɗi ga ƙasashen da ke karɓar sojojin Amurka, tana cewa duk ƙasar da ta taimaka wa abin da ta kira sojojin Amurka masu kai hari, za su ɗanɗana kuɗarsu.

    A gefe guda, Iran ta ce hare-haren Amurka sun kashe fararen hula aƙalla biyar tare da jikkata sama da 60 a ƙauyen Kohstak da ke Sirik, yayin da ake gudanar da bikin aure.

    Rahotannin kafofin yaɗa labaran Iran sun ce yara na cikin waɗanda suka mutu, yayin da mata da yara ke cikin mafi yawan waɗanda suka jikkata.

  18. Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin Amurka a Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare da jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin sojojin Amurka da ke ƙasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

    A cewar sanarwar rundunar, an kai harin ne a sansanonin Dhafra da Manhad na UAE, tare da kai wasu hare-hare a sansanin Sheikh Isa da ke Bahrain.

    Iran ta ce hare-haren sun zo ne a matsayin martani ga hare-haren jiragen yaƙin Amurka da aka kai a baya.

    Sa'o'i kaɗan kafin haka ma,rundunar juyin juya halin Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Kuwait da Jordan.

  19. Jami’in sojin Nijar ya zargi ƙasashen waje da hannu a boren sojoji a ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami’in sojin Nijar, Roger Gabriel, ya zargi wasu ƙasashen waje hannu a boren da sojoji suka yi a sansanin sojin 101 da ke Yamai a ranar 29 ga Agusta.

    Ya ce ya samu kira da saƙonni daga mutane a Nijar da ƙasashen waje da ke nuna tsoma bakin ƙasashen waje da ke goyon bayan waɗanda suka kai hari a sansanin.

    Jami’in ya yi zargin cewa wasu jami’ai daga Chadi da wasu masu alaƙa da tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, sun ambaci yiwuwar taimakon ƙasashen waje da dakarun musamman.

    Sai dai ba a tabbatar da waɗannan zarge-zarge da wata hujja mai zaman kanta ba.

    Hukumomin Nijar dai sun ce sun shawo kan lamarin bayan harbe-harbe da aka yi a sansanin.

  20. Ba na son ƙulla wata yarjejeniya da Iran - Trump

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta wani rahoto da ABC News ta wallafa a daren Talata, inda ya zargi kafar da ya ƙirƙirar labaran ƙarya da bayar da rahoton cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin tilasta Iran ta shiga tattaunawa.

    Trump ya ce ba shi da sha’awar ƙulla wata yarjejeniya da Tehran.

    "Saɓanin abin da ABC, wadda nake kira Fake News, ta ruwaito, ba na ƙoƙarin dawo da Iran kan teburin tattaunawa. Ba ni da wata sha’awa ga su sa hannu kan wata yarjejeniya da ba ta da wani amfani a gare su," in ji Trump kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

    "Na fi son halin da ake ciki a yanzu, inda muke daf da samun cikakken iko kan mashigin Hormuz, yayin da tattalin arzikin Iran ke ci gaba da durƙushewa gaba ɗaya. Suna kawai ƙoƙarin jinkirta abin da babu makawa zai faru."

    A ƙarshen saƙonsa, shugaban na Amurka ya ce "Yaushe mutanen Iran za su tashi su yi gwagwarmaya?"

    Kalaman Trump sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan da ya bayyana sabbin hare-haren da Amurka ta kai a kusa da mashigin Hormuz a matsayin "waɗanda suka dace", tare da gargadin cewa Washington za ta kaddamar da hare-hare masu ƙarfi fiye da haka idan Iran ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

    Iran ta ce hare-haren sun auka kan fararen hula da ke halartar wani bikin aure a ƙauyen Kohstak Sirik, inda aƙalla mutum biyar suka mutu, ciki har da yaro ɗaya.

    Kafafen yaɗa labarai na Iran sun kuma ruwaito cewa mutane sama da 60 sun jikkata a harin.